15

62 3 1
                                    

*ALHAKI...*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 15.

Last free season 1.

Safeena gida ta koma ta kasa zaune tsaye, hankalinta in yayi dubu to ya tashi tunanin hanyar da zata bi don magance matsalarta take yi, so taka ta ƙarfi da yaji a fasa wannan auren, haka ta ɓata lokaci mai tsawo tana saka da warwara, daga bisani ta yanke hukuncin da zata yiwa Namir, ta sauke gauron numshi tare da duba agogo dake manne a bango, taga ƙarfe ɗaya saura, sai a lokacin ta ji ana sallar azahar a masallaci, ta miƙe ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallah kana ta ƙara shiryawa ta fita a mota ta shiga cikin gari, da ta gama siyayyar da za ta yi sai ta biya restaurant ɗin da ta saba oder ta siya abinci a nan taci, da ta tashi tafiya ta siya shinkafa da miya da cosilo sai ta siya kunun Aya, tace zuwa yamma a kawo mata sai ta basu kulolin da za saka mata, kunun ayar ne ta tafi da shi gida. 

Namir a gidansu ya yini yana ta ƙoƙarin nuna kulawarsa akan Amira dan ya samu hajiya ta sauko daga fushin da take dashi akan laifin da ba shi ya aikata ba, duk da yace zai auri Amira ba zai janye ba amma taƙi sake masa fuska, Amira kam kallonsu kawai take yi, burinta ta isa katsina gidansu ta sanar da iyayenta ba zata auri Namir ba dan ta san sune kaɗai zasu fahimci abinda take nufi. Da aka kira sallar magrib ne Namir yayi sallama da iyayensa ya fito ya nufi gidansa amma sai da ya tsaya a hanya yayi sallarsa kafin ya ƙarasa gida. Ya samu falonsu sai ƙamshin turaten wuta yake an gashi an gyara ko'ina komai yana a mazauninsa, hango kan dinning da yayi cike da kayan abinci ya saka shi sakin murmushi hakan ya tabbatar masa da Safeena ta gama saukowa tunda yau gashi har tayi girki, ya samu waje ya zauna yana jiran ta sauko dan ya san taji shigowar motarsa kuma duk inda take hankalinta yana gunsa, zamansa ba daɗewa Safeena ta fito cikin shigar wata rigar kanti wanda ta tsaya mata a iya cinya, ta kamata sosai a masa daga cikinta kuma ta buɗe sosai, gashinta kuma ta ɗaure da ribom ta saka ɗan kunne fashion mai tsayo tare da zobensa da kuma abin hujin hanci, fuskarta powder kawai ta shafa da man baki ta saka takalmi filat, sosai tayi kyau ta ƙaraso gabansa tayi wani juyi rigarta ta buɗe tana fidda wani kamshi mai matuƙar daɗi, Namir sai da ya lumshe ido kamar ya suma dan daɗi, sosai ta burgeshi ya kuma yaba da kwalliyar ya haɗa babbar yatsa da manuniya ya kanne ido ɗaya yana cewa.

Komai yaji kyakkyawar matata.

Safeena tayi farr da ido tana cije leɓenta na ƙasa tare da shafa sumar kanta tana cewa.

Zumu ci abinci yanzu ko sai anjima.?

Da wunya na shigo gidan kuma kin san bana so nayi miki laifi na ci abinci a waje, dole ne na dawo muci a tare.

ka yiwa kanka farar dabara. Muje muci kan a kira sallar isha'i.

Ta faɗa tare da yin gaba shima ya mike ya bi bayansa suka isa dinning suka zauna yana cewa.

Da kanki kika yi girki.? Yau wace rana.

Bani nayi ba oder ne, kawai dai na tsara wajen yayi kyau yadda zai kayatar da kai.

Kin yi ƙoƙari kuwa.

Yace yana murmushi itama murmushin ta mayar masa ta zuba masa nashi sannan ta zuba nata, suka fara ciki suna hira jefi jefi, Namir ya zuba kunun aya a ƙofi ya sha, yadda yaji ɗanɗanonsa ya saka shi kallonta.

Yau mutanen nan sun sauya ɗanɗanon kunun nan ko baki na ne? Naji yayi zaƙi sosai kuma yana ɗan ɗaci ɗaci kaɗan.

Uhum Safeena tace tana taunar abinci, Namir ya kuma dubanta yace.

Beb ya kamata ki je gidanmu ki duba jikin Amira daga nan ki bawa su Hajiya haƙuri dan Allah, bana so rashin jituwa ya shiga tsakaninki da su.

Haƙuri kace na basu akan laifin me? Wlh ba zan je ba idan har sai na duba Amira zata ji sauki to ta mutu, ko dan kaga nayi shuru da maganar shiyasa kake da gwanjin tunkarata da wannan zancen.

ALHAKI...Where stories live. Discover now