9

48 3 0
                                    

*ALHAKI...*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 9.

Washe gari da safe aka yi addu'ar uku tare da sadakar abinci. Sai wajen sha biyun rana ne kafin mutane suka ragu, dama baba yace a ranar za a daina zaman makoki kowa yaje ya cigaba da hidimar gabansa. Muna zauna a ɗaki Habib ya aiko ƙanina akan na zo yana kirana, da sauri na miƙe na gyara mazaunin hijab ɗina kafin na fita zuwa can ƙofar gida, can gefe na hango shi inda ba mutane yana zaune kan mashin ɗinsa, na isa na tsaya tare da jingina bayana da bangon gidanmu, sai na gaishe shi ya amsa fuska sake tare da yi mini gaisuwa na amsa kana ya tambaye ni jikina nace da sauki, sai muka ɗanyi shuru na mintuna daga bisani na sauke ajiyar zuciya nace.

Ya maganar 'yan sanda kuwa an samu gano wanda ya shiga gidanmu ɗin?

Batul ba a samu ba jiya sai da naje har ofishinsu Bashir muka yi maganar, yace wlh ba wani labari suna ta dai bincikensu ne.

To Allah ya tona asirin ko waye yasa a gano shi, dan gaskiya hukunta wanda ya kashe Hibba shine zai sa zuciyata ta samu rangwame daga ƙuncin da nake ciki.

Ameen ya rabbi, In Sha Allah za a kama shi mu dai cigaba da tsananta addu'a. Ya batun komawarki gida? naga baba yace yau an daina zaman makoki sai dai a cigaba da amsar gaisuwa a cikin gida.

Wlh dama ina son ganinka akan batun komawata, gabaɗaya na kasa mance yadda naga Hibba cikin jini, hakan shike ƙara tada mini hankali, shiyasa nace zan yi kamar sati biyu a nan gida mu gani, in ma na kai kwanaki arba'in ƙila na samu natsuwar komawa.

Eh hakan ma yayi ai ina ganin ki zauna har sai lokacin da kika samu natsuwa sai ki faɗa mini na zo da kaina na ɗauke ki. Dan gaskiya nima a gidan Umma nake kwana tun ranar rasuwar na kasa kwana ni kaɗai saboda jimamin abin da ya faru. Allah ya isar mana ga duk wanda ya samu cikin wannan tashin hankalin.

Amin nace ina jin daɗin yadda Habib ya bani goyon baya da cigaba da zama a gidanmu, muka ɗan taɓa hira kaɗan kafin muka yi sallama yace bayan kwana biyu zai zo kan addu'ar bakwai, nace ya gaida su Umma kana ya wuce. Da ɗan farin ciki na shiga gida saboda hirarmu ya ɗan ɗebe mini kewar damuwar da nake ciki kaɗan, ban sanar da Mama yadda muka yi da Habib ba dan nasan zata hana ni zama a gidan shiyasa na bar maganar har sai sun tafi dan nasan baba bai da damuwa ba zai takura ni ba.

*****

Ranar addu'ar bakwai, bayan anyi addu'a da sadaka ne su Mama suka shirya suka wuce ƙauyensu, kafin su wuce sai da ta yi mini maganar zuwa yamma na koma gidana nace mata to kawai dan bana son tasan nan zan zauna. Har zuwa yamma kowa ya watse hatta yayyuna mata duk yau suka wuce sai ni ce na rage a ɗakin da da yake matsayin namu, dama na sanar da Yadikko ta sani kuma ta mara mini baya, ta shigo ɗakin muna ɗan hira sai ga kaka Iya ta leƙo, da ta ganni kwance a katifa ta soma sakin salati.

Ke me kike jira baki tafi ba kowa ya kama gabansa, ko mijinki ne zai zo ya ɗauke ki?

Kaka ina nan sai nan da kwana biyu zan tafi saboda bana jin daɗi kuma can gidan ni kaɗai ce nan kuma akwai mutane zan fi sakewa, kuma na yiwa Habib bayani yace ya amince.

To meyasa baki bi uwarki ba zaki zo ki ɗaura mana wahalar ciyar dake, to wlh tun wuri ki haɗa kayanki ki tafi gidanki, munafuka dama kin damu da 'yar uwarki ce da kika tafi kika bari aka kasheta, ai wlh alhakinmu sai ya kama ki ke da mijinki, muna zaman mu lafiya kika nace sai an baki ita, ɗan talla da take yi mana muna samun na kashewa kika daƙile mana, Allah ya saka mana kawai.

Mama ki daina faɗin haka, haka Allah ya rubuta zai faru, kuma ke da Batul ba a jinku fa saboda ta wajenki ne karki kware mata muyi muku dariya.

Cewar yadikko cikin zolaya, murmushi nayi na kasa magana dan nasan kaka ba zata sakar mini mara nayi fitsari ba amma duk da haka yafi na zauna dasu dan zasu ɗebe mini kewa. Ƙofa tayi tana cewa in baba ya shigo zata faɗa masa ya koreni na tafi gidana, tunda ita bana jin maganarta to dole ne naji na baba, guntun murmushi nayi ina jinjina rikicin kaka da kullun yake ƙaruwa kamar wata ƙaramar yarinya. 

ALHAKI...Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα