04

52 4 1
                                    

*ALHAKI...*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 4.

Batul…

A ganina ihun kukan da nake yi shine kaɗai zai sama mini sassaucin zafin da nake ji daga zuciyata, Su maman Zeena suka dinga rarrashina tare da bani baki, wanda daga bisani sai kukan da ihun ya ɗauke ɗif tamkar an ɗauke mini wuta, jikina yayi mugun sanyi ƙalau tamkar wacce aka zarewa lakka duk a dalilin ambaton Allah da su maman Zeena suka tunasar dani nake yinsa a zuciya, cikin dakiya na ɗago idona da yayi jajir nace.

Ina gawar Hibba.?

An kaita gidanku yanzu haka ma sun isa.

Cewar Uwale, sai na mike da kyar ina cewa.

Dan Allah ku kaini nayi bankwana da 'yar uwata ba zan iya zama a nan ba.

Maman zeena ta soma koro mini bayanin Habib yace zai zo da kansa mu tafi, nan na kafe nace lallai su barni na tafi, shine fa Uwale da maman zeena suka ce zasu rakani, nan sauran matan suka ƙara yi mini gaisuwa suka wuce, mu muka muka fito daga gidan muka samu napep muka wuce zuwa gidan mahaifina.

Tun daga kan layinmu na ƙara tabbatar dagaske Hibbatu ta rasu domin mutane ne sun taru sosai a ƙofar gidanmu da muke hange sai alwala suke yi, muna ƙarasowa Uwale ta biya mai napep sai muka wuce cikin gida inda mutane sai kallonmu suke wanda nasan ni ake kallo dan kowa yasan Hibba a gidana take kuma a can aka kasheta, hakan yasa hankali ya ƙara tashi bugun zuciyata ya ƙaru har muka shiga cikin farfajiyar gidanmu da yake da ɗan girma, mata a cike yan uwanmu ne da maƙota, ana gani na aka soma ga Batul tazo, kakarmu Iya itace ta nufo ni da sauri tana karasowa ta fincikoni tare da sakar mini kyakkyawar mari wanda yasa ni ganin taurari, hakan yasa na saki gigitaccen kuka kaka Iya ta soma magana.

Ina kika tafi ki bar Hibba a gida aka kasheta, Allah ya isa bamu yafe miki ba ashe b azaki iya riƙe amanarta ba kika dage ke da mijinki a baku ita, to wlh sai Allah ya saka mana wannan tashin hankalin da kuka sanya mu a ciki. 

Haba Iya wannan lokacin bana mayar da magana bane, Batul ta fiki shiga tashin hankali dan haka duk muyi haƙuri Allah ya nufa can ajalinta yake.

Cewar matar Yayan Babanmu, ni kuwa tsugunawa nayi a gurin ina rizgar kuka kamar raina zai fita, nasan dama za a yi haka dan gidan namu ba ilimin addini ne ya ratsamu ba balle mu san yadda ake haƙuri da ƙaddara, ko kaka bata yi mini haka ba nasan wasu daga dangi sai sun sakar mini magana, na tabbatar wannan shine zai ƙara wutar kiyayya a zukatan wasu daga cikinsu musamman masu baƙin ciki da mijin dana samu mai wadata fiye dana sauran 'ya'ya. Yin kuka nake ina shassheka tare da fizgo numfashina da yayi mini nauyin fita, hakan yasa Iya ta koma mazauninta itama tana kuka, yayarmu Halima itace ta zo ta kamani tana rarrashina sai ta kaini kan tabarma na zaunar dani, su Maman zeena kuwa su suka bawa kansu wajen zama, muna cikin wannan mawuyacin halin sai ga yayan babanmu Sale ya shigo yana cewa su yayanmu Alhasan su shiga ɗakinmu su ɗauko gawar Hibba zuwa ƙofar gida za a sallaceta, kamar an tsikare ni na tashi zubbur na rigasu faɗawa ɗakin bai hana sunbi ni a baya ba, ni kuma tsayawa nayi ina kallon gawar Hibba wacce take cikin makara, suka ɗauketa suka fito tsakar gida, da sauri na biyo bayansu na kama makaran ina tsala ihun magana.

Ku barni naga fuskar Hibba banyi bankwana da ita ba, wayyo Allah Hibba dana san mutuwa za kiyi da banyi tafiyar nan ba, illalillahi wa inna ilaihir raji'un sun kashe ta sun raba ni da gudan farin cikina, ke nake kallo kike ɗebe mini kewar Umma da bata kusa damu, ina zan saka rayuwata Allah ka saka mana ka wulaƙanta wanda ya kashe mana ke. Allah ya jikanki Hibba yasaka miki da makoma mai kyau insha Allah ke 'yar aljanna ce.

Ba wanda kukana bai ƙara masa tashin hankali ba, da kyar 'yan uwana suka rabani da makaran na zube akasa in aburgima da ƙafafuna, a dai dai lokacin Ummanmu ta shigo tare da 'yan uwanta da suka zo daga soba, ganin halin da nake ciki yasa suka ƙaraso da sauri, umma kuwa wucewa tayi wajen su kaka ta samawa kanta matsuguni tana share hawaye, 'yan uwan umma sune suka kamani ƙanwar inna Hadiza ta soma cewa.

ALHAKI...Where stories live. Discover now