11

38 4 0
                                    

*ALHAKI...*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 11.

Safeena sai da ta jima a wannan wajen ta kasa jan motar saboda nauyin da ƙirjinta yayi mata, tayi kuka har sai da ta gaji dan kanta ta yi shuru, wayarta kuwa a silent ta saka saboda kiran da ake ta yi mata, sai wajen karfe biyu da rabi ta iya saita kanta ta ɗaura ɗan kwali kana ta duba madubi ta gyara fuskarta har da kwalli ta saka amma duk da haka ya nuna alamar tayi kuka sosai dan idanunta sun kumbura fuskarta kuma tayi ja, ta tada motar ta wuce wani restaurant dake nan kusa dasu ta shiga, bayan ta yi parking ta wuce ciki ta shiga vip ita kaɗai ta zauna, ba jimawa wata budurwa ta zo sai ta faɗa mata abinda take so sai ta wuce. Jalof din taliya wanda yaji kayan lambu da soyayyen naman kaza aka kawo mata sai maltina mai sanyi da ruwan gora, badan ranta na so ba ta ci abincin sai dan ta kawar da yunwar da take ji, bayan ta kammala ta biya su kuɗinsu kana ta fito ta shiga mota ta hau hanya, tunanin inda zata je take yi wanda zata kasance ita kaɗai saboda bata so kowa yasan da wannan labarin har sai ta zartar da hukuncin data niyya, dan haka ta wuce can nasfat GRA ne da ba mutane ta samu gefen wani fili ta yi parking ta kwantar da seat ta kwanta tana duba wayarta, kira fiye da ashirin ta gani, na Kubura da na Momy Sai na Namir da ƙaninta Ahmad, har da text Namir yayi mata na tambayar inda taje dan momy ta kira shi akan ta kirata ba ta ɗauka ba, dalilin daya sa ya san bata gidansu. Taɓe baki tayi ta mayar da wayar tana lumshe ido saboda sanyin AC motar yana ratsata, mamakin rainin hankalin da Namir ya yi mata take yi, yanzu da ace bata sani ba haka zasu cigaba da ninketa suna hidimarsu karshe sai an ɗaura taji labari kamar tarar aradu, tunda aure baya ɓoyuwa wata ƙila daga bakin ƙawayenta zata samu labari, hakan kuwa ba ƙaramin raini da ƙasƙanci zai kawo mata ba a cikin kawayenta, dan dole zasu yi mata dariya su ƙauketa makaryaci akan cika bakin da take na yabon mijinta ba zai mata kishiya ba.

Ina wlh ba zau yuwu ba dole sai nayi abinda za a fasa auren nan, dan ba zasu saka naji kunya ba. Allah na gode maka daka tona mini asirinsu kan a ɗaura, yadda suka nima tozar tani wlh nima sai na ɗanɗana musu gumar baƙin ciki.

Tace a fili tana fuzzar da iskar bakinta mai ɗumi, kanta ya ɗau chaji har ciwo yake mata saboda damuwar data ɗaurawa kanta, ta kuma lumshe ido saboda raɗaɗin da take ji a zuciyar da tunanin hukuncin da take son zattar musu, haka ta ɗauki lokaci tana saƙe saƙe har sai wajen karfe biyar da rabi kafin ta saita kanta ta tada motar ta nufi gidanta cike da ƙarfin zuciya da ƙissima abinda data aikata.

Ƙarfe shida da minti takwas ake kiran sallar magrib dan haka shida tana yi Anas da Aliyu suka yi alwala suka tafi masallaci, Haneefa itama tayi nata alwalar tana zaune a falo kan a kira sallah, dama Namir bai dawo ba tun fitar da yayi ɗazun, Amira kuma tana kitchen dan ƙarasa musu girki, A lokacin Safeena ta ƙaraso mai gadi ya buɗe mata gate ta shiga ta ajiye motar inda da saba ajiyeta, sai ta fito ta wuce ta shiga falo, Haneeta tana ganinta tace.

Sannu da zuwa Anty.

Safeena ta amsa fuska sake kamar ba wani abu, tace.

Ina 'yan uwanki?

Yaya Anas da Aliyu sun je masallaci, Adda Amira kuma tana kitchen.

Ok ta ce sai ta wuce kitchen ɗon ta tsaya a bakin ƙofa tana ƙarewa Amira kallo ta bayanta, tsanarta na ƙara ruruwa a zuciyarta da kissima rainin hankalin da suke yi mata har da sakin jiki a gidanta kuma zata aure mata miji, tayi guntun murmushi wanda yafi kuka ciwo hakan yasa Amira ta juyo da sauri dan Murmshin nata ya ɗanyi sauti, cikin fara'a Amira tace.

Laaa Anty kin dawo, ashe ba kwana za kiyi ba.

Amira fasawa nayi saboda wami dalili, me kike girkawa?

Tuwon shinkafa miyar yauƙi yaya yace nayi, na gama miyar nake jira ta silala na sauke.

ALHAKI...Where stories live. Discover now