14

37 3 0
                                    

*ALHAKI...*

Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 14.

Da safe.

Wajen takwas da rabi Safeena ta shirya cikin wasu kaya farare riga da wando ready made ta ɗaura brown ɗin gyale a kanta, ta ɗauki jaka da takalmi mai kalar baƙi da brown ta shirya tsaf, fuskarta ba wani makeup amma tayi kyau ta ɗauki duk abinda take buƙata ciki har da system ɗinta ta fito ta zuba a mota ta shiga, dama tuni mai gadi ya buɗe mata gate daya ga fitowarta sai ta fice abinta. A lokacin Namir ya tashi daga barci saboda ƙugin motarta da ya ji kamar a mafarki, ya sauko daga gado yana miƙa ya saka jallabiyarsa ya fito farfajiyar gidan ya ga ba motarta hakan ya tabbatar masa da fita tayi, kuma ya san yau sunday ranar hutunsu ne basa fita sai in fitar ya zama dole, yasan duk tana yin haka ne da gayya saboda abinda ya faru, ya koma ciki yayi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya ya ɗauki wayarsa ya saka agogonsa a hannu kana ya ɗauki key ya fito dan zuwa asibiti, yana ƙoƙarin shiga mota yaji ana buga hon a ƙofar gate, mai gadi ya wangale gata motar ta shigo, Namir tsayawa yayi yana jiran ƙarasowarsu dan ya gane motar Dadyn Safeena ce, da suka yi parking suka fito Namir ya matsa kusa da motar ya risinar da kai suka gaisa kana suka yi masa jajen abinda ya faru tare da bashi haƙuri, Namir yace ba komai an samu rashin fahimta ne amma komai zai wuce, suka tambayi Safeena yace bata daɗe da fita ba, Dady yace.

Dama gidanku zamu je da ita ta basu haƙurin abinda ta aikata, dan na kira Abbanka yace an sallamesu tun ɗazu.

Dady ai Safeena har yanzu bata sauko ba In Sha Allah ni da kaina zan kaita ta bada haƙuri.

To shikenan bari mu ƙarasa gidanku.

Yace to kana suka shiga mota suka wuce shima ya shiga motarsa ya wuce yabi bayansu dan shima gidan zai je. Ko da suka isa sun samu duk suna babban falon Amira tana zaune a carpet har an yi mata ɗaurin, hawayen wahala kawai teke fitarwa tana tsinewa Safeena a zuciyarta, bata jin zata iya yafe mata, Sannan ma ba zata taɓa yarda da auri Namir ba, tuni ma ta nima son da take masa ta rasa wanda hakan ya faru ne saboda tsoro da tashin hankalin data gani jiya, sai taji yanzu sam ba zata iya rayuwa da shi ba,l. Bayan su Dady sun gaisa da juna ne da yiwa su Abba jajen abinda Safeena tayi suka daura da masu haƙuri, Abba yace.

Komai ya wuce amma gaskiya yana da kyau ku tsawatar mata dan wannan abinda da tayiwa Amira, da ba dangi bane wasu ne can Allah kaɗai yasan fitinar da ta kwanto.

In Sha Allah zan ja mata kunne sosai ba zata sake wannan rashin hankalin ba kuma zata zo har nan ta baku haƙuri.

Cewar Dadyn Safeena, Hajiya ta ja gunyun tsaki tana cewa.

Aure ne dai ba fashi In Sha Allah sai anyi shi idan zata kwantar da hankalinta su zauna lafiya to, in kuma taƙi kanta zata yiwa dan ba zamu zuba mata ido tana wannan abin ba, in mun yafe wannan to wlh ba zamu yafe duk wani rashin hankali ba nan gaba.

Hajiya ayi haƙuri a yafe mata in sha Allahu ma ba zata ƙara haka ba, zamu tsawatar mata. Aure kuma Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu, Amira kiyi haƙuri kinji In Sha Allah haka ba zata sake faruwa ba.

Cewar momy, Amira dai banda hawaye ba abinda take yi, jinsu kawai take wai sai anyi auren, ita kam tuni ta haƙura dan wannan baƙar izayar da ta sha ba karen hauka ne ya cijeta ba da zata yarda a ɗaura auren, Namir ko da autan maza ne ta haƙura da shi har abada. Namir bayan sun gaisa ne Hajiya ta tambaye shi akan ya kwaso kayansu Amira, yace ya manta sai tace ya miƙe ya wuce ya kwaso musu kayan, yace to kana yaja Anas suka tafi tare ya taya shi kwasowa. Sai wajen sha ɗaya iyayen Safeena suka bar gidan bayan sun jide musu kayan siyayya da yawa na dubiya da suka kawowa Amira.

*****

Safeena.

Gidan Kubura ta wuce ta samu mijinta yana nan dan haka ta maƙale a ɗakin yara har sai da Kubura ta sallami Ibrahim ya fita kafin suka koma bedroom ɗinta suka zauna, Kubura ta kalleta da kyau tana cewa.

ALHAKI...Where stories live. Discover now