page five

2.6K 129 0
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

Wannan page Sadaukarwa ne ga duk wani mai bin wannan labarin, ina jin dadin yadda kuke bina sannu a hankali ba zan gaji da yi maku addu'a ba Allah ya barmu tare da ku😍😍😍

                        0⃣5⃣

"Ina sam haka ba mai yiwuwa bane gaskiya."

"Oh! Kenan bani da ikon zartar da hukunci akan Alhaji? Karfa ki manta Asma'u dake da duk wani wanda ke gidan nan, karkashin ikona kuke, abin da na zartar dole a bishi domin haka auren Alhaji yau saura kwana shida. Yana gama faɗin haka ya bar mata falon gaba daya.

Shiru Mummy ta yi tana tunanin maganar Daddy, bata da yadda zata yi tunda ya furta tofa tabbas sai an yi shi domin tafi kowa sanin halin mijinta, kafi daya ne duk abin da yasa a gaba sai ya cika burinsa, take ta ji ko da wacce yarinya za'a hada Alhaji ta tsaneta bata sonta sam, lallai ko wacce yarinya ce sai ta dandana kuɗarta, domin rabon da su sami matsala da Alhaji har ya yi fushi da ita har ta manta, amma yau dalilin wata har tsawa Alhaji ya daka mata kwafa ta yi tare da barin falon.

Karfe bakwai na safiya Alhaji karami AK in ji abokansa, ya shiga cikin falon cikin shirinsa na tafiya office, mummy da Daddy ne sai Fatima da Ammar a dining din. Gaida iyayensa ya yi tare da zama, sannan su Fatima suka gaida shi.

Cikin kulawa Mummy ta kalleshi

"Baban Mummy an yau ka fito da wuri fa."

"Eh! Wallahi Mummy Ina da wani aiki ne, kuma zamu yi baki shi yasa zan fita da wuri."

"Allah ya taimaka." Ta yi maganar tana aje masa duk abin da yake buk'ata a gabansa.

"Thank you My Mummy."

"You're welcome my sweet boy."

"Kai Alhaji anjima idan ka dawo ina son ganinka." Maganar Daddy ce ta katse masu hiran.

"In sha Allah." Alhaji ya yi maganar cikin ladabi.

Daddy bai kuma magana ba ya bar dining Yana fadin

"Sai na dawo."

"A dawo lafiya." Mummy ta faɗa jiki a sanyaye.

Shima Alhaji yana gama break ya wuce office, bai samu kansa ba sai shida na yamma, a gajiye ya shiga gidan babu abin da yake buk'ata irin ya yi wanka ya huta, a gaggauce ya yi wankan ya sanya kayan shan iska, bai je falo ba, sai kwanciyar da ya yi akan kujera kiran sallah yasa shi mik'ewa ba don ya so ba.

Bayan ya dawo sallah ne ya isa falo don ya yi dinner, yana kammalawa ya shiga bedroom din Daddy domin bai manta ba, gaida Daddy ya yi ya zauna kansa a kasa haka kawai ya tsinci kansa da faduwar gaba, Inna lillahi yake maimaitawa a cikin zuciyarsa muryar Daddy ya ji kamar daga sama

"Alhaji wanene ni a wajenka?"

"Mahaifina." Ya bashi amsar cikin sauri.

"Ina da iko da kai ko bani da? Daddy ya kuma jefa masa tambaya.

"Kana da shi Daddy."

"Gud." Daddy ya faɗa sannan ya ci gaba "kamar yadda ka ce ina da iko da kai, to na zartar da wani hukunci a matsayina na mahaifinka na zaba maka matar aure nan da kwana biyar biki."

Wani ɗagowa Alhaji ya yi jikinsa har yana rawa, ya ce

"Dad-daddy matar aure?"

"Eh! Biki nan da kwana biyar don haka ka soma shiri."

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now