Page 18

2.1K 90 2
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
        _*ZULAYHEART RANO*_💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        1⃣8⃣

Shirye-shiryen biki ya kankama musamman ta bangaren Mummy, shi uban tafiyar ma ko a jikinsa domin ba wani dokin amaryar yake ba, amma Mummy kam uban rawan kan da take abin har mamaki yake ba Alhaji. Biki saura kwana uku su Aunty Ameena suka zo, ta yi mamaki sosai na rashin ganin Zainab, ko da ta tambayi Mummy masifa ta fara dole Aunty Ameena ta ja bakinta ta yi shiru. Fatima kam kullum sai ta yi kukan rashin Zainab, tana tunanin halin da take ciki.
     Ranar juma'a dubban mutane suka shaida auren Abdallah wato (Alhaji) da amaryar sa Feenah, amarya na cike da farin cikin samun Alhaji a matsayin miji, Mummy Kam farin ciki kamar wacce aka yiwa bushara da aljanna, ya yin da ango ko ajikinsa karfe takwas aka kawo amarya fuskarta mursisi ko digon hawaye babu irin wanda amare suke yi, yan kai amarya basu wani jima ba suka tafi aka bar amarya ita ɗaya, har karfe tara bata ga Alhaji ba ranta ya yi masifar ɓaci tsaki sun fi ashirin wanda ta yi a fusace ta nufi bangaren Mummy don ganin me yake yi (kai Allah ya shirya ni kam tunda nake ban taɓa ganin amarya haka ba, sai akan Feenah ko dan irin kunyar nan babu Lallai akwai buk'atar gyara.. Turus ta yi tana kallon sa
     Su kam su Alhaji basu san ma da wata Feenah a tsaye ba hiran su kawai suke sha shi  da yan'uwansa, har Aunty Ameena tana mamakin yadda Alhaji ya saki suna hira cikin kwanciyar hankali, Fatima kan ji take kamar ta gaura masa mari domin wani haushi da yake bata ba kaɗan ba. Mummy ce ta fito daga daki inda take tare da shakikan kawayenta suna ta shewa da tayata murna.
     Ido hudu suka yi da Feenah dake tsaye ta wani hada rai, da sauri ta isa wajenta tana faɗin "a'a Feenah tsayuwar me kike anan kuma?" Sai a time ɗin suka san da wata, da mamaki suka juya suna kallonta don ko a littafin Hausa basu taba ganin irin wannan kayan takaicin ba, wato biyo Alhaji ta yi, hmmmm lallai haka Aunty Ameena ta faɗa a zuciyarta, Alhaji ji ya yi kamar ya mutu don tsabar takaici. Fatima kam wata uwar tsaki ta ja ta nufi ɗakinta,  a ranta tana cewa "wallahi Mummy kin cuci ya Alhaji da kika haɗa shi da wannan banzar." A falo kuwa basu gama mamaki ba sai da suka ji Mummy tana cewa "kai Alhaji tashi ku wuce tunda ga matarka ta biyoka." Amsawa kawai ya wuce ya yin da Feenah ke binsa a baya, tsabar takaici su Aunty Ameena ko tsayawa ba su yi suka yi hayewarsu sama.
   Suna shiga ya yi wucewar sa bedroom ɗinsa, binsa ta yi ya banka mata wata uwar harara ai da sauri ta nufi fita, wanka ya yi ya shafe jikinsa da mayuka masu kamshi sannan ya sanya rigar bacci ya yi kwanciyar shi. Feenah kuwa bayan Alhaji ya zabga mata harara wucewa daki ta yi a ranta ta ce "zan yi maganinka, daret wanka ta shiga bata wani jima ba ta fito, mayukan da Momynta ta ta haɗa mata da shi ta yi amfani, sannan ta sanya wata shegiyar rigar bacci wanda har gara tsirara da ita, babu abin da ta daura kan kayan ta nufi dakin Alhaji, ta ci sa ar  dakin bai rufe da key ba don haka tana turawa ya bude, Alhaji da ya zubawa kofar ido yana shirin ganin mai shigo masa daki kai tsaye, sai ko suka yi ido hudu da Feenah yana shakar kamshin turaren ta sai ya fara fita hayyacinsa ido kawai ya zuba mata, ita kam ganin haka sai ta saki wani mayen murmushi har tana lashe baki domin tasan tarkonta ya kama kurciya.
     Bata tsaya ko ina ba sai kan gado, tana doka wannan murmushi zama ta yi jikinta har yana gogan na Alhaji, ji ya yi kamar ba a wannan duniyar yake ba kafin ya yi wani tunani har ta haɗe bakinsu ta shiga yi masa wani salo, sosai Alhaji ya cika da mamakin Feenah ganin tana jan masa rai sai kawai ya shi bata nashi darasin cikin zafi-zafi, darasin Alhaji ya firgita Feenah don ta yadda Alhaji daban yake ko cikin maza, sun shiga wani yanayi mai wuyar fassara su kadai suka san irin abin da suke ji, sam Alhaji bai yi mamakin rashin samun Feenah a budurwa ba don yasan yadda bata da kunyar  nan tana iya bada budurcinta.

Sam Alhaji bai ji ya gaji da Feenah ba, shi yasa har suka kai asbah suna aikin abu ɗaya, ko da asbah bayan ya yi sallah haka ta kara zuwa masa da jarabarta don shi Alhaji ya gaji, Amma haka ya biye mata. Wani nannauyan bacci ya kwashe shi, ita kuma Feenah wanka ta yi shima ba na tsarki ba domin dai ba iya na tsarki ta yi ba. Babu abin da ta dauka daga cikin falon ta yi ficewarta zuwa bangaren Mummy.
     Zaune ta same su sun gama break suna hira, babu wanda ta gaida sai zama da ta yi tana mika, da kallo suka bita suna takaicin kasancewar ta a family nasu da Zainab ce sun tabbatar babu yadda zata yi masu haka, suna jin haushin rashin ta a gidan yarinya mai hankali da nutsuwa, washe baki Mummy ta yi fuska cike da fara'a take faɗin "A'a Feenah ke ce da safe yanzu nake shirin cewa Fatima ta kawo maku abin break."
   Taɓe baki ta yi ta ce "Lallai Mummy ta ina zan iya jure yunwa har zuwa lokacin da za a kawo mana abinci? Jin cikina nake babu uwar komai sakamakon sussukata da Alhaji ya yi a daren jiya, gaskiya Alhaji baya da tausayi kwana fa ya yi yana aikin abu daya." Ta gama maganar tana gyara zama. Gaba daya kunyar maganarta ta kama su har Fatima, ita kuwa ko ajikinta don bata san wani abu kunya ba. Mummy kam murmushi ta yi irin na takaici kana gani kasan maganar ta ɗan bata ranta sai kawai ta girgiza kai don ta rasa amsar da zata ba.
   Fatima ta mike zata wuce Mummy ta ce "ki haɗa mata break." Turo baki ta yi ta ce "in  haɗa mata break ita aikin me take? Dining din ne bata iya zuwa?" "Ke kinga bafa rashin kunya nasa ki min ba kina ji ko maza ki wuce." Mummy ta dire maganar tana hararan ta. Mtsww ta ja tsaki sannan ta je ta zuzzuba mata komai ta barshi a dining din ta yi wuce warta ɗakinta.
   Tashi Feenah ta yi har tana canza tafiya ita a dole ta kawo budurcinta gidan Aure, abin takaici wai Mummy har da yi mata sannu.

****
Zainab ce ta fito bedroom rike da Fawzan ta haɗa fuska kamar zata zunduma ihu, Umma ta kalleta tare da girgiza kai ta ce "ke kam lafiya?" Hawayen da take ma'kalewa suka zubo ta ce "Umma FAWZAN ne sai da na gama home work ya yaga min buk kuma wallahi da kyar na gama rubutun." Da yake IK ya sa Usman ya samo mata lesson teacher, yana zuwa gida yana koya mata karatu, sosai take jin dadin karatun kuma tana gane duk darasin da yake mata, jiya ne ya bata home work na math gashi da wahala, Fawzan na kusa da ita yana wasa da yake ya fara zama har yana rarrafe ta gama home work din ta manta da book ɗin ta shiga toilet tana fitowa taga har ya rarrafa ya ɗauki book ɗin ya yaga. "Oh! Allah to kuma shi ne abin kuka?" Umma ta faɗa tana kallonta.
   Wani sabon kuka ta fashe da shi, ta ce "Umma don baki san wahalar da na yi wajen rubutun ba shi yasa." "To yi hakuri ki sake wani kin ji. Fawzan dariya yake ta yi don bai san abin da ya aikata ba, takaici ya rufe Zainab da dariyar da Fawzan ke yi, "Umma kin ga fa sai dariya yake min." Da shagwaɓa ta yi maganar. "Kai Fawzan dariya kake yiwa Momman ko ka daina." Umma ta kwaikwayi maganar Zainab tana mik'ewa da Fawzan a hannu "bari mu je mu shakata a waje." Bubbuga kafa Zainab ta fara kamar wata yarinya tana juyowa suka yi ido hudu da shi, wanda sam bata san yana tsaye ba kallon jikinta ta yi sanye take da wata doguwar riga wacce ta yi mugun karbar jikinta kanta babu dan kwali sai kananun kalabar da aka yi mata suka zubo sosai ta yi kyau tana ganin ya kafeta da ido ai da sauri ta koma daki...

      *RANO*✍

BURINA COMPLETEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora