Page 30

1.8K 87 0
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S P.M.L*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
  *ZULAYHEART RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                       
*Afuwan da rashin ganin post kullum hakan nada nasaba da rashin samun isasshen lokaci, ina godiya sosai masu text da kira lafiya lau nake har abada ba zan manta da kulawarku ba.*

*Godiya gareki MAMAN AHMAD*

_*hhhhhhhhh! An ya kuwa Besty kin yi wa sangarta adalci da kika ce BURINA ya fi shi daɗi? Nasan dake a da can ke ce ta farko mai nunawa sangarta soyayya, amma yanzu kin koma son BURINA, to ni Yar Mutan Rano da sauran sangarta fan's bamu da kamarsa.*_

                 *30*

"Na rokeki da Allah Zainab ki ji tausayina ki tausayawa Alhaji yana cikin wani yanayi mai wuyar fassara." "Mummy ni ce fa Zainab Wacce kike ce ba zaki taɓa sona ba, Mummy kin mance ikirarin ki na cewa kin tsani talaka baki kaunar abin da zai hadaki da talaka Mum..." Kasa k'arasa maganar ta yi dalilin wani kuka da ya taso mata da gudu ta ruga tare da rufe kofa, tana ci gaba da kukanta domin sosai ta ji ta kara tsanar Mummy da Alhaji saboda sun kasance masu tsananin son kansu. A falo kuwa ita ma Mummy kuka take yi cin karfinta musamman da ta lura sam Zainab ba sauraronta zata yi ba, wajen Umma ta wai ga cikin dashewar murya ta ce

"Don Allah ki taimaka ki sanya baki, wallahi duk mai imani idan ya kalli Alhaji yasan yana cikin wani hali, sannan kuma Dr ya ce nan da awa ashirin zai farka don Allah Hajiya kunsa baki?" "Karki damu Hajiya in sha Allah zata sauko amma sai a bari zuciyarta ta yi sanyi." Cikin karfafa mata zuciya Umma ta yi maganar. Gyada kai Mummy ta yi jiki a sanyaye "ki zauna Hajiya karki damu fa." "To." Ta amsa tana zama kamar yadda Umma ta bukata, sai a lokacin idonta ya sauka akan Fawzan zuba masa jajayen idonta ta yi tana kallon sa, sak Alhaji yana yaro bata taɓa ganin mai irin wannan kamar ba hatta yatsun kafarsu iri daya ne, sansanyar ajiyar zuciya ta sauke tana godewa Allah da bai sa Zainab ta zubar da cikinta ba.

A bangaren Zainab kuwa kuka take kamar ranta zai fita, idanuwanta sun kumbura suntum fuskar ta yi jawur har a wannan lokacin bata bar yin kuka ba a haka Umma ta shigo dakin ta sameta "Ya subhanallah! Zainab kina da lafiya kuwa? Wannan wacce irin zuciya kike da ke abu baya wucewa a wajen ki?" "Umma bani iya manta Mummy da Alhaji abin da suka min ya fi gaban na manta su." Murya bata fita ta yi maganar." "Zainab yana da kyau ki manta da duk wani abu da Mummy da Alhaji suka maki domin ya wuce, ko yanzu sun tabbatar ba faduwa kika yi ba sai dimbin riba da kika samu, ki manta baya ki fuskanci gaba idan kika yi haka shi zai nuna kin fi su Mummy har a wajen mahalicci."  "Umma kina nufin in manta abin da Mummy ta yi mi? No! Ba zan iya ba Umma."

"Zaki iya Zainab ki kudurta ahaka a zuciyarki, Allah zai taimaka maki kuma ya zama dole ki manta ko dan Fawzan da ya shiga tsakani." "Umma su sun manta zan haifi Fawzan ɗin ne suka wulakanta ni? Please ki bar yin wannan maganar don Allah." Yana gama faɗin haka ta shige toilet kanta na mugun sarawa. Duk yadda Umma ta so shawo kan Zainab abin ya gagara dole sai zuba mata ido ta yi ita ma Mummy dole ta koma gida cikin karayar zuciya don ta san Zainab ba zata amince ba.

Washegari tun safe Mummy ta iso gidan amma kemadagas Zainab ta ki bari ko muryarta Mummy ta ji, tana dai zaune tana addu'a Allah ya sanyaya zuciyar Zainab, tun dare da Usman ya koma Rano ya sanarwa da Abbanta duk halin da ake ciki, sosai ran Abba ya ɓaci shi yasa ya ce Usman ya zo gobe ya shiga da shi cikin Kano karfe goma da kwata suka isa gidan, umma kanta ta yi mamakin ganin Abba a gidan. A falo ya samu waje ya zauna ya dubi Umma ya ce "Habibah kira min Zainab ki ce mata ni Alhaji Sa'idu ne ke kiranta."

Tana zaune ta hada kai da gwiwa gaba daya ta rasa tunanin da zata yi sai jin motsin buɗe kofa ta yi a ɗan razane ta ɗago kai "Malam na kiranki a falo." Shi kenan abin da umma ta iya faɗa ta wuce toilet, jiki na rawa ta dauki mayafi tare da nufa hanyar falon tana hada ido da Abban wasu hawaye suka fara zarya a kuncinta "sannu gwana isasshiya." Shi ne abin da Abba ya fara faɗa mata. Wajen sa ta karasa tare da tsugunawa tana faɗin Barka da zuwa Abba ina kwana?" "Lafiya lau, ashe Kema haka kike Zainab? Wato kin zubar da duk wani tarbiyya da na yi maki? Yanzu ashe ke baki cikin mutane masu yafiya ga abin da aka musguna masu? Ashe ke baki iya rama Alhairi da sharri? Ki bani mamaki Zainab har kullum cikin alfahari nake da ke akan kina cika duk wani BURINA, ashe akwai ranar da zaki bata min akan abu kalilan?" A matuk'ar zafafe Abba ya gama maganar.

"Ka yi hakuri Abba har kullum BURINA shi ne na faranta maka, wallahi Abba zan iya yi maka komai in har ranka zai yi fari ka yi hakuri Abba ka yafe min Umma don Allah ki yafe min, ki roki Abba ya yafe min." Cikin kuka sosai take maganar. "Daina kuka yar albarka na yafe maki dama baki min komai ba ke ma ki yafe abin da aka maki." "To Abba." A ladafce ta amsa. A jiyar zuciya Mummy ya yi tana hamdala ga Allah, Abba bai wani jima ba ya tafi duk yadda yaso su tafi tare da Zainab sam taki yadda a cewar ta zata zo ita ɗaya, haka Mummy ta so su tafi tare amma ko kallon arziki Zainab ta ki yi mata dole ta kakkaɓe jiki ta tafi ita ɗaya zuciyata fal murna domin Alhaji zai farka yaga *CIKAR MURADIN ZUCIYAR SA* sai dai tana fatar Allah yasa kafin ya farfaɗo ta isa asbitin don saura awa biyu kacal.

Tana zaune a daki sai faman buga Game take a wayarta sam babu abin da ya dameta, Fawzan na gefe yana kallo suna yi suna dariya, umma ce ta shigo turus ta yi tana kallon Zainab "ke kam kina da lafiya?" "Umma mai kika gani?" Ta yi tambayar fuska cike da walwala. "Iyye! ZAINAB kin manta da inda zaki je ne? Ko ko dai kina nufin Malam bai isa dake ba?" "Lah! Sorry Umma wallahi sam na manta bari na tashi ai yanzu zamu wuce." Ta ida maganar tana mik'ewa tsaye, har ga Allah ta manta da zata je wani Rano Fawzan ta soma yi wa wanka sannan ita, a karamin lokaci har sun gama shiryawa basu dauki wani kaya ba don suna da kaya a gidan can, cikin kwarewa take jan motar har Allah ya kaisu garin Rano har zata wuce Umma ta ce su fara shiga asbiti dole suka fara shiga ɗin, fakin ta yi wajen faka motoci sannan suka fito tana rike da hannun Fawzan kai tsaye bangaren da suke tunanin nan Alhaji yake suka fara nufa, da Daddy suka fara karo murmushi ya kubce mata don tana son Daddy shi ne mutum na uku da suka nuna mata kauna a duniya, a gabansa ta zube tana kwasar gaisuwa.

"A'a wani ke gani kamar Zainab?" Daddy ya yi tambayar bayan ya amsa gaisuwar. "Ni ce Daddy." A kunyace ta ba shi amsa. "To sannunku da zuwa ku k'arasa ciki mana." "Yawwa Daddy." Zainab ta amsa tana mik'ewa. "Wannan wanene mai kama da Alhaji?" Da mamaki yake kallon Yaron. "Takwaran ka ne Alhaji sunanku ɗaya dan wajen Zainab ne." Umma ce ta ba shi amsa domin Zainab ta yi gaba ta bar masu Fawzan a wajen. Murmushin yake ya yi ya ce "Madallah Allah ya raya." Cikin zuciyarsa karin haushin Mummy ya kama shi wato ashe har da ɗa ta kori Zainab shi ne bata sanar masa ba, gaskiya ta gama cutarsa." Fawzan ɗin ya dauka suka shiga ciki inda Mummy da Fatima har da Aunty Ameena suke, rungume juna suka yi da Fatima suna murnar ganin juna, Fatima tana ganin Fawzan a hannun Daddy ta yi saurin zuwa ta amsheshi tana faɗin.

"Sis wannan ne Yaron mu?" "Eh! Shi ne yaronku Sis." "Wow so fine boy mai kama da Ya Alhaji sak ya sunansa?" "Sunan da kike so shi aka sanya masa Fawzan." "Kai Masha Allah na yi farin ciki da haka ina godiya da kauna yar'uwa." Fawzan fa ya zama ɗan gata kowa sonsa yake babu kamar Mummy Wacce ke ji kamar ta maida shi ciki, suna haka Dr ya k'araso ya bukaci Zainab ta bishi dakin da Alhaji ke ciki haka nan ta ji gabanta ya fadi cikin dauriya ta bishi yana tura kofar gabanta ya tsananta faduwa a haka suka ida shiga ciki idonta ne ya sauka kan Alhaji dake kwance kamar gawa wani irin yanayi ta shiga take ta ji kanta na mugun sarawa da kyar ta iya kai hannu ta dafe...

             *RANO*✍

BURINA COMPLETENơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ