Page 16

2.3K 104 0
                                    

 
💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        1⃣6⃣

Tun da Alhaji ya fita daga gidan bai dawo ba sai bayan la'asar, daret bangaren Zainab ya nufa don ganin a wani hali take haka kawai ya tsinci kansa da son ganin Zainab, musamman yadda zuciyarsa ke BBC azalzalarsa akan Zainab ɗin ya rasa yadda aka yi har ta shiga zuciyarsa, ko da ya bata a falo sai ya nufi bedroom ɗinta can din ma wayam, kan sa ya daure da rashin ganin ta a bangaren duk iya dubawa babu ita a tunaninsa kila tana falon Mummy shi yasa ya shige wanka, bai wani daɗe ba ya fito jallabiya ya sanya tare da nufa bangaren Mummy. Da sallama ya shiga Mummy dake zaune a falon ta amsa tana fadada fara'ar fuskarta.
   Waje ya samu ya zauna yana fadin "Sannu da hutawa Mummy." "Yawwa Babban mutum ya aikin?" "Alhamdulillah amma aiki babu dadi musamman yanzu da babu Daddy duk sai abin ya yi min yawa." "Ayya sannu Allah ya maka albarka ya kara budi." Amin ya amsa cikin farin ciki. "Bari a hado maka abinci don karshen ta babu komai a cikin ka." Mummy ta yi maganar tana kiran Fatima dake kicin.
      "Mummy bana jin yunwa fa da abar shi kawai." "A'a Abdallah ka ci abinci zama da yunwa babu dadi." Daidai nan Fatima ta iso dauke da tiren da ta shirya masa abincin. Kallonta ya yi yaga yadda idanuwanta suka kumbura sun yi ja kamar mai ciwon ido. Fara zuba masa a plet ta yi jiki a sanyaye ta mika masa, amsa ya yi yana faɗin "ke lafiya kuwa kin ga yadda fuskarki ta yi?" Hawayen da take ma'kalewa ne suka samu nasara zubowa, hankalin Alhaji ya tashi sam baya k'aunar ganin hawayen yan'wansa, don haka da sauri yake tambayarta  "Fatima me ke faruwa?" Da kyar ta ce "Yaya Mummy ta kori sis cikin halin ciwo." "Wacece sister kuma?" "Sister Zainab." Ta bashi amsa.
   Wani irin mik'ewa tsaye ya yi har yana zubar da abincin bai ma sani ba, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un shi yake maimaitawa ya yin da ya kafe Mummy da ido. Mtsww ya ji Mummy ta ja ta dogon tsaki ta ce "Wannan tashin da ka yi na menene? A kwanakin nan sam na rasa gane halinka mene damunka? Don na koreta shi ne kawani zabura haka, to tun wuri gara ka samu nutsuwa tun ban saɓa maka ba." Kallo ɗaya zaka wa Alhaji ka tabbatar da zallar tashin hankalin da yake ciki, ransa ya masifar ɓaci bai taɓa mai da wa Mummy magana ba amma yau har bai san lokacin da ya fara magana cikin ɓacin rai da takaici "Amma Mummy baki ganin abin da kika yi sam bai kyautu ba, yarinya tana fama da ciwo kika koreta? Wallahi bana jin Allah zai barmu haka ba tare da ya saka ma yar mutane ba, Mummy wannan halin baya da kyau." Harara ta watsa masa ta ce "Bani da labarin ka zama Malami ai, sannu da k'ok'arin wa'azi kai ka haifeni ko ni na haifeka?" Cikin fada take maganar.
      Da taimakon sunan Allah ya samu dan nutsuwa har ya tuna maganar da ya faɗawa mahaifiyarsa sam bai kamata ba, duk da dai gaskiya ya faɗa, akan gwiwoyinsa ya durkusawa yana rokon Mummy gafara "don Allah Mummy ki yi hakuri bazan sake ɓata maki raina, fushinki a gareni tamkar rasa jin dadi ne a gareni." Ganin yadda Alhaji ya yi sai ya ba Mummy tausayi, hannu tasa ta ɗago shi ta ce "Allah ya maka albarka ina alfaharin samun ka matsayin ɗa." Murmushin jin dadi ya yi kawai bai iya furta komai ba.
     "Ina son anjima ka shirya don zuwa gidan Hajiya Turai ku tattauna da Feenah mun gama maganar aurenku da ita." Ya Salam. Alhaji ya furta a zuciyarsa, shi kenan ni kuma ba za a barni in samo matar aure ba sai aita haɗani da wasu yanzu ita Mummy ta rasa dawa zata hadani sai wannan mara kunyar yarinyar? Kai nikam ina ganin rayuwa wannan wacce irin masifa ce shi kenan *BURINA* ba zai cika ba?" Da kyar ya tattaro nutsuwarsa baya k'aunar ya bata ran mahaifiyarsa don haka sai ya ce "In sha Allah Mummy zan je." Yana gama faɗin haka ya fita daga falon gaba daya.

Da yamma haka Alhaji ya je gidan domin cika umurnin mahaifiyarsa. Lallai ya kuma tabbatar da rashin kunyar Feenah zalla domin yadda ta rika yi masa abin ya mugun bata ransa, haka da ya daure ba tare da ya nuna komai ba sannan ya taka mata burki akan wasu abubuwan.

*****
A asbiti kuwa yau kwana su Zainab biyu, domin Dr ya ce sai ta yi kwanaki bakwai ko biyar kafin ya bata sallama, jin bayanin Dr sai IK ya nufi kano da kan sa ya dauko mahaifiyarsa inda ta ci gaba da kula da Zainab da kuma jaririnta, sosai Umma ta tausayawa halin da taga Zainab a ciki, gayi ko sun tambayeta mijinta sai dai ta fara masu kuka, daga karshe Umma ta hana a tambayeta komai har sai lokacin da ta so don kanta ta sanar masu, haka kuwa aka yi.
    Misalin karfe tara na safiya IK ne zaune a kan farar kujerar da ke dakin da aka kwantar da Zainab, rungume yake da jaririn a hannunsa kallon sa ya kai ga Zainab ya ce "Zee kin ga har yau suna ga shi yaron ko huduba ba a yi masa ba kuma ke kin ki fadan unguwar su mijinki balle a nemo shi, zuwa yanzu ya kamata a ce an sanya masa suna."
   Kanta akasa ta hawaye da rawar murya ta ce "don Allah ya IK kabar yi min maganar Alhaji, yaro kuma na baka dama duk sunan da ya yi maka ka sanya masa don koda Alhaji na nan bana jin zai iya ba yaron nan suna." Da mamaki suke kallonta, har IK ya bude baki zai yi magana Umma ta yi saurin kallonsa don haka sai ya yi shiru.
     "Kai Khalil bashi sunan kakansa wanda ya haifi ubansa." "To ai Umma ban san sunan ba." "Faɗa masa sunan ke Zainab." Umma ta bata umurni fuska babu alamar wasa. A hankali sai ka saurara da kyau zaka ji mai ta ce ta furta" *AHMAD*" murmushi kawai IK ya yi ya yiwa yaron huduba take ya ce "Allah ya raya mana Ahmad bisa tafarkin gaskiya Ubangiji ya albarkaci rayuwarsa." A tare suka amsa da Amin. IK kam hoto ya fara ɗaukan Yaron da wayarsa. Muryar Umma suka ji tana faɗin "Sai ki samo sunan da za'a ke kiransa don ba a kira shi kai tsaye da sunan sa ba." To ta amsa tare da tunanin wani suna zata sanya masa, murmushi ta yi da ta tuna wani hira da suka taɓa yi da Fatima tun kafin tasan zata ɗauki ciki, farin ta gyara zama ta ce  "Sis idan har kika samu ciki kika  haihu indai namiji ne sunansa FAWZAN." Dan murmushi ta yi mai haɗe da kwalla ta ce a fili "Allah sarki Sis ga shi yau na samu Yaro namiji kuma zan cika maki burinki ga FAWZAN Nan ya samu." A tare Umma da IK suka dubi Zainab. Umma dai bata yi magana ba sai IK ya ce "Suna mai dadi FAWZAN kuma sunan ya dace da shi Allah ya raya.
    "Wai Khalil ba yau zaka tafi bane?" Umma ta yi tambayar tana kallonsu. "Yau zan tafi mana sai karfe sha daya jirgin zai tashi, amma Umma mai kika gani da kika ce na fasa tafiya?" "ban ga kana alamar tashi bane." "Allah umma bana son rabuwa da FAWZAN ne, kila kafin in Kuma zuwa ya soma zama." Murmushi ta yi ta ce "to ai akwai waya sai ku rika gaisawa." "Umma kin manta gidan su zasu koma?" Da muryar tausayi ya yi maganar. Sai a lokacin Umma ta tuna sai dai bata yi magana ba. Zainab kam mamaki take ta yi wai IK zai koma Ingila shi kenan ta rabu da Burinta, wasu siraran hawaye suka zubo mata, ta yi saurin share su. Mik'awa Umma FAWZAN ya yi yana faɗin "Umma Usman nan duk abin da kuke bukata zai yi maku, Please Zee ki kula da FAWZAN kar ki rika barin yana kuka, idan zaku tafi gidan Abbansa a sanar min." "Allah ya yi maka albarka Ubangiji ya baka abin da kake nema Allah ya baka zuri'a dayyaba." Umma ta yi ta masa addu'a. Tana gama giya FAWZAN ta fita daga dakin. Shi kuma ya tsaya kallon Zainab wanda kanta ke duke "ZEE BURINA zan tafi." "Allah ya kiyaye hanya yaya Nagode sosai Ubangiji ya bar zumunci, Allah ya saka maka da mafificin Alhairi na gode."
     "Amin Zee na ji dadin addu'ar ki, in sha Allah bazan wuce wata uku ko hudu ba zan zo, zan yi kokarin neman gidan ki ko dan FAWZAN." Yana gama faɗin haka ya nufi fita, Zee Kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi.

*Masha Allah Ubangijin Allah ya raya Ahmad Abdallah Rano (FAWZAN) rayuwa mai albarka, muna ta ya Zee murna har ma da Alhaji da Mummynsa wanda basu san da shi ba*😜

      *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now