Page 31

2.3K 101 4
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S P.M.L*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
  *ZULAYHEART RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        3⃣1⃣

Da kyar sakamakon sunan Allah da ta ambata yasa ta dawo cikin nutsuwarta cikin karfin hali k'arasa gaban gadon da yake kwance, take wani irin tsoron Allah ya shige ta ganin yadda Allah ya maida Alhaji lokaci ɗaya, wasu zafafan hawaye suka fara zarya a kuncinta har bata san time ɗin da Dr ke faɗa mata ta zauna ba, sai da ya kuma maimaita mata "Madam ga wajen zama in sha Allah nan da mintina kadan zai farka." Da kai ta iya amsawa sannan ta zauna tana mai yi masa addu'a Allah ya sassauta masa.

Tana zaune tana dai ci gaba da addu'a kanta a kasa bata son ta daga ido balle har ya sauka kan Alhaji, don gani take kamar ya mutu zaman kusan minti goma ta yi a gaban sa da kyar ta iya ɗago kai ta kalleshi kara ware ido ta yi don sai ta ga kamar yana motsi, tashi ta yi ta matsa wajen bakinsa take kallo wanda yake furta *ZAINAB*  a hankali "Ya Alhaji gani nan please ka buɗe ido ni ce Zainab gani gaban ka." Buɗe ido ya soma yi a hankali har ya bude su duka fes ya sauke idonsa kan Zainab, a wahale ya ce "Zee! Ke ce? Don Allah karki kuma guduna ke ce farin cikinsu kuma BURINA." "Ba zan kuma gudunka ba Ya Alhaji Allah ya baka lafiya." "Yawwa Zainab ki yafe min duk abin da na yi maki wallahi na yi nadama." "Haba ka yi shiru kai da ba lafiya gareka ba, bari na kira Dr." Ta dire maganar da niyyar fita, da sauri Alhaji ya riko hannunta tare da girgiza kai "Dr zan kira maka kuma su Mummy da Daddy suna waje."

"Please karki daɗe Zee bana son ki yi nisa dani." "Yanzu zan dawo." Ta bashi amsa cikin tabbatar masa da haka. A waje hankalin Mummy ya tashi ganin har an yi minti ashirin da biyar da shigan Zainab dakin amma har a time ɗin bata fito ba ya sa ta fara sintiri, gani take kamar zata rasa Alhaji, shi kam Daddy kacokan ya mai da hankalinsa kan Fawzan sau hira suke su uku da Umma da Fatima Fawzan sai gwaranci yake masu. Mummy tana ganin an bude dakin ta yi saurin matsawa tana ganin Zainab ce ta yi saurin cewa "Zainab ya jikin Alhajin ya farfaɗo kuwa?" Dan murmushi ta yi ta ce "eh! Ya farfaɗo idonsa biyu Dr zan kira." Tana gama bata amsa ta nufi office din Dr, Faɗa masa ta yi Alhaji ya farfaɗo sannan ta koma dakin a lokacin su Daddy har sun shiga cikin suna masa sannu.

Dudduba shi Dr ya yi, inda ya tabbatar da babu wata matsala sannan ya dubi Alhaji fuska ɗauke da murmushi ya ce "Madallah! Abokina lafiya ta samu ko?" "Alhamdulillah! Na samu sauki sai rashin karfin jiki." "Kar ka damu da wannan tun da masoyiyarka tana kusa." Harara Zainab ta aikawa Dr da shi ta gefen ido, Dr ya lura don haka sai ya ja bakinsa kawai ya dubi Daddy "Alhaji Alhamdulillah lafiya ta samu sai dai ba zamu ba shi sallama ba sai ya kara kwana biyu don ya samu karfin jiki." "Muna godiya Dr ai dama fatar mu kenan kuma tun da lafiya ta samu Alhamdulillah." Daga haka Dr ya yi masu sallama ya fita.  Alhaji da tun ɗazun idonsu ke kan Fawzan dake rungume jikin Fatima ya ce "Fatima wannan yaron fa?" Murmushi ta yi ta ce "yaro na ne Ya Alhaji." "To masu ɗa ina kika samo shi?" "Yaron da Sis ta haifa mana ne fa." Da murmushi ta karasa maganar. Tsirawa Zainab ido ya yi yana son gasgata abin da Fatima ta faɗa sai dai Zainab ɗin ta yi kasa da kanta balle ya tabbatar ɗin.

Amsan  yaron ya yi daga wajen Fatima ya rungumo shi jikinsa son Yaron da kaunarsa suna ratsa shi, yana rungume da yaro bacci ya dauke shi, ganin haka sai Zee ta matsa wajen Daddy tana fadin "Daddy tun da jikin da sauki zamu isa gida mu dan huta zuwa anjima sai mu dawo." "Allah ya yi maki albarka Zainab karki damu zuwa anjiman sai ku dawo." "To Daddy." Ta amsa tana riko hannun Fawzan. Wajen Umma ta nufa tana faɗin Umma tashi mu isa gida anjima sai mu dawo."   "Haba Zainab tun yanzu?" "Eh Umma ina son in huta ga baccin da nake ji." "Da dai kin kuma zama ni sai na tafi tun da ya farfaɗo kuma jiki ya yi sauki." "Oh! Umma mun yi magana da Daddy kuma ya ce na tafi don haka tashi kawai mu je."

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now