Page 23

1.9K 89 0
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
        *ZULAYHEART   RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        2⃣3⃣

Ko cikin motar tarin yake mai tsanani, da yar ya samu ya ɗan lafa amma kallo ɗaya zaka masa kagane yana cikin tashin hankali domin yadda ya koma a cikin lokaci ƙalilan, motar ya ja da taimakon sunan Allah ya kai kansa gida, a cikin gidan ma da ya yi fakin kasa fita ya yi domin yadda zuciyarsa ke yi masa tukukin zagi da raɗaɗi, hannu kawai ya sanya ya dafe saitin zuciyar numfashin sa na sama sama gaf yake da daukewa, mai gadi da ya ga har a yi kusan minti biyar bai fito ba ya k'arasa jikin motar don duba ko lafiya.

A firgice ya nufi falon gidan jiki na rawa ya yi sallama, Mummy dake zaune ta amsa tana tambayarsa " lafiya" "Babu lafiya Hajiya ga Alhaji can ya shigo amma ba a cikin hayyacinsa ba." Da sauri Mummy ta tashi har tana yin tun tube domin maganar ta razanata, a yanayin da ta ga Alhaji bata iya tsayawa wani abu ba ta sanya mai gadin ya taimaka suka maida shi daya bangaren ita kuma ta shiga mazaunin direba da wani irin gudu ta fita, wani asbiti ta shiga da shi mai suna *(A'A SPECAL HOSPITAL)* Nurse din asbitin suka dauko abin gungura mara lafiya suka shiga da shi ciki Allah ya taimaka babban likitan yana cikin asbiti taimakon gaggawa ya soma ba shi cikin kwarewa da gwaninta, kallo ɗaya zaka yi wa likitan ka tabbatar kwararre ne a fannin duba marasa lafiya Dr Asmad Abubakar kenan, miji Ameesha na cikin littafin SANGARTA.

Mummy sai kai komo take domin hankalinta ya masifar tashi, bata kaunar ta rasa Alhaji a daidai wannan lokacin, addu'a take Allah ya tashi kafadar sa a ƙalla an yi kusa minti arba'in kafin Dr Asmad ya fito daga dakin da aka kwantar da Alhaji, kai tsaye bai kalli Mummy ba sai ma tafiya ya yi da niyyar shiga office ɗinsa, da sauri Mummy ta tare shi tana faɗin "Dr ya jikin Alhaji?" "Da sauki Hajiya sai dai ina son ganinki a office yanzu." Yana gama maganar ya ci gaba da tafiya.

Binsa a baya Mummy ta yi har cikin office din, kujera ya nuna mata ta zauna shi kuma ya ci gaba da yan rubuce-rubucen sa kamar minti uku ya ɗago da kai tare da ake biro ya gyara gilashi idonsa "Wato Hajiya ki yi hakuri da abinda zan faɗa maki." Jikin Mummy ya k'ara sanyi domin bata san me zai faɗa mata ba, a sanyaye ta ce "ina sauraronka Dr." "Alal hakika yaronki na cikin wani yanayi domin kuwa yanzu haka da kyar muka samu numfashin sa ya daidaita, saboda zuciyarsa ta fara kamuwa da ciwo kuma tana niyyar yi masa illa." "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un ciwon zuciya Dr?" "Eh ciwon zuciya Hajiya amma wannan kada ya dame ki in sha Allah zai warke amma sai an yi kokarin sama masa abin da yake so, sannan zamu daura shi akan magani idan an kula to komai zai saukaka."

"To likita za a kula in sha Allah zan iya ganinsa?" "Eh! Duk da yana bacci kar ki bari wani abu ya farkar da shi sai idan shi da kansa ya farka ga takaddan maganin da za a saya Allah ya ba shi lafiya." "In sha Allah zan kula na gode Dr." Daga haka Mummy ta fita daga office din zuciyarta Cike da alhini.

Lokacin da ta shiga dakin yana ta baccinsa sai dai kallo ɗaya zaka masa kasan yana jin jiki, zama Mummy ta yi kusa da shi ta zabga uban tagumi idonta akan sa, bai farka ba sai da ya yi awa biyar cur da sunan Zainab ya farka, kallonsa Mummy ta yi cike da takaici yadda yake ambaton sunan Zainab ɗin wato kenan saboda ita ya shiga wannan halin? Lallai sai ta mike tsaye don ba zata yadda yarinya ya sabauce ba akan wata matsiyaciya ba, kwafa kawai ta yi sannan ta fita kiran likitan bayan ta yi masa sannu, dudduba sa ya yi sannan ya umurci Mummy ta ba shi abinci da magani domin bugun zuciyar ta sa ta daidaita, da kyar ta samu ya ci ya sha maganin sannan ya koma bacci.

****

Yau bikin saura kwana biyu biki duk wasu shirye-shirye an kammala sai jiran ranar daurin aure kawai, Zainab na zaune da Abbanta suna hira wayarta ta fara fitar da daddaɗar sauti hakan ya tabbatar mata da wanda ke kiran, cikin nutsuwa ta dauki wayar tare da karawa a kunne wanda yin haka ya yi daidai da faduwar da gabanta ya yi, a sanyaye ta ce "Assalamu Alaikum barka da warhaka." Daga daya bangaren ya amsa cikin shauki da zallar soyayyar ta "Wa'alaikumus salam My Zee gani a rano." "A rano?" Ta yi tambayar cikin mamaki.

"Eh, kewarku na yi ke da yarona Fawzan Please ki fito ina jiran ki kofar gida." "To." Ta amsa cikin wani irin yanayi da ta rasa tantance na menene. Kallon Abbanta ta yi tare da fadin "Abba wai ya Khalil yana jirana a kofar gida." Fawzan dake jikin Abban ya yi saurin dira ya yi waje cikin sauri, murmushi kawai Abba ya yi ya ce "Sai kin dawo Allah ya tsare." "Amin" ta amsa tana nufa hanyar kofar gidan gefe ta tsaya ganinsa tare da mutane, cikin sauri ya sallamesu. Tunda yaga ta fito ya kafeta da idanuwansa da suke saukar mata da kasala, take kuwa ta tsinci kanta cikin yanayi mai wuyar fassara langaɓar da kai ta yi gefe cikin marairaicewa ta ce

"Haba BURINA wannan kallon fa?" Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke wanda har ya bai wa Zainab mamaki, ware ido ta yi ta ce "Har da ajiyar zuciya?" Gira ya daga mata domin ya kasa bata amsa da kyar ya ce shigo mota mu je Please." "Ina za mu je?" "Ke dai shigo gidanmu." Bata kuma magana ba sai shiga ta yi shi kuma ya tada motar sannan suka dau hanya. A kofar gidan ya yi horn Mai gadi ya buɗe da sauri shi kuma ya cusa hancin motar cikin gidan a farfajiyar inda aka tanada don aje motoci ya yi parking duk suka firfito, boot IK ya bude ya dauko wata bakar jaka irin ta zuwa office hannunsa rike da na Fawzan.

Direct kofar falon suka nufa shi mika mata key ya yi ta buɗe sannan suka shiga ciki, a je jakar ya yi tare da zaunar da Fawzan dake zuba masa surutu akan kujera, ita dai Zainab ta zubawa sarautar Allah ido gaba daya tsoron IK ya baibaye zuciyarta, musamman da ta ga ya yi tagumi hannu bibbiyu. Sanyaya murya ta yi ta ce "lafiya kuwa Ya IK ni fa wallahi ban gane wannan zuwan naka ba kuma ga shi ka kuma sanya Ni a duhu me ke faruwa?" "Nima ban sani ba Zainab wallahi tun shekaran jiya nake jina bani da lafiya ga yawan faduwar gaba shi ne na yake shawarar zuwa na ganku." "Subhanallah! Ta furta cikin sauri da mamaki domin ita kanta shi take fama da shi ta rasa dalili.

"Kar ki damu babu abin da zai faru sai Alhairi kuma ban faɗa maki don ki tashi hankalinki ba, ki nutsu ina son mu yi magana dake kinji ko?" "To." Ta amsa cikin rashin kuzari. Takaddu taga yana fitowa da su cikin jakar da ya shigo da su, ATM card da wasu takaddu ya fara mika mata, a sanyaye ta amsa tare da cewa "na menene wannan?" "Saboda idan kina da buk'atar kudi za ki iya cire wa, da sunan Fawzan na bude, wannan kuma." Ya nuna mata wani ATM din ya ce "saboda su Umma na buɗe ina son zuwa nan da kwana huɗu ki ba su, ga takaddan wannan gidan da muke ciki domin ki na gina shi don haka na mallaka maki, wannan kuma na can gidan da Umma ke ciki ne ki bata ki ce na mallaka mata shi, wannan kuma don Allah ki bada masallaci nake so a gina min da makarantar islamiyya dayan ATM card din cikin hudun na ginin masallacin ne, ga na motar da na saya maki na so ranar aurenmu ne zan danka maki ita sai dai hakan ba mai yiwuwa ba ne." Jikin Zainab ya dauki kyarma da maganar IK ba ta san lokacin da ta ce "Ya IK hakan ba mai yiwuwa ba ne me kake nufi da wannan kalmar...?

To wallahi nima Yar Mutan Rano na kasa fahimtar maganar IK domin ta masifar girgiza ni, to wai me IK ke nufi da wadannan maganganun mai kama da wasiyya? Sai kun biyo alkalamin yar mutan Rano sannu a hankali har ya warware mana.

*RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now