seven

2.3K 101 0
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*
                 
Happy sallah to all Muslim umma💗💓💖😍😍

                   0⃣7⃣

Tana zaune ita ɗaya a falon babu wanda ya shigo mata, abinci ma sai wanda su Inna karima suka rage take ci, idan lokacin sallah ya yi take mik'ewa ta yi, har magriba ta kawo jiki tana niyyar mik'ewa domin shiga bedroom ta ji sallama, da sauri ta amsa tana juyowa.

Yarinyar da ta nuna masu yadda ake amfani da famfo ne ɗazun, don haka sai ta saki murmushi ta faɗin

"Sannu da zuwa."

"Yawwa Aunty kina ta zaune ke kaɗai, ina son shigowa ina tsoron Yaya Alhaji."

"Ayya ai gaki yanzu kin shigo, na gode sosai wanene Alhaji kuma?"

"Lah! Baki san Yaya Alhaji ba?" Cikin mamaki Fatima ta yi tambayar."

"Ummh." Shi ne kawai Zainab ta iya faɗa.

Kafin Fatimah ta yi wata magana sai jin kiran Sallah suka yi, da sauri Zainab ta mik'e tana faɗin
"Lokacin sallah ya yi bari na yi sallah."

"To." Zainab ta amsa tana gyara zama, don ita bata sallah. Da watanni Zainab zata girmi Fatima, don ko tsawo kusan daya suke sai dai Fatima ta nuna mata kyan jiki don cima ba daya ba, Fatima tana da yawan surutu ita kuma Zainab bata da yawan magana.

Bayan ta idar da sallar falo ta dawo, sanye da hijab

"Lah! Ashe baki tafi ba?"

"Eh! Ina nan jira nake ki fito."

"Ai kam kin kyauta." Zainab ta yi maganar tana zama. Hira suka shiga yi duk a maganar daga "eh" sai "a'a" shi ne amsar Zainab.

Bangaren Mummy kuwa Alhaji ne zaune a falo yana ta famar latsa waya hankalinsa kwance, Mummy ce ta sauko daga sama cikin kwalliya, sanye take da wani rantsattsen lacce wanda ya karbi jikinta, kunnenta ma'kale da wani dankune kirar Saudiyya haka wuyanta, kusa da kujerar da Alhaji ke kai ta zauna, ɗago kai kawai Alhaji ya yi ya sakar mata murmushi, ita ma maida masa murmushi ta yi tana faɗin

"Babban mutum kana zaune kai ɗaya?"

"Eh! Mummy Yanzun nake son tashi."

"Lallai kam gara dai aje asamu hutu."

"To Mummy." Ya amsa yana nufa sama.

"A'a kuma ina zaka je?"

"Bacci zan yi Mummy."

"Bacci kuma? Ka manta yanzu Iyali gare ka?"

"Oh! Wallahi Mummy na manta gaskiya Daddy ya ɗaura min aiki."

"Zo ka wuce tun bai fito ya sauke mana yayyafi ba, domin yanzu kaɗan yake jira."

"To ya zan yi ai dole na wuce, amma wallahi yarinya zata dandana kuɗarta a wajena."

"Kar ka saurara mata nima nan ba zan saurara mata ba, domin komawa zata yi kamar mai aiki, abu daya nake so ka yi min shi ne karka kuskura ka kusanci inda take, bana so in haɗa zuri'a da talakawa kaskantattu."

"Haba Mummy me zan yi da wannan yarinyar, ko hannunta bana jin zan iya rikewa balle na haɗa jiki da ita."

"Yawwa ɗan albarka haka nake so, jeka sai da safe."

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now