page 10

2.1K 130 2
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

                        1⃣0⃣
Bai yi wata wata ba ya kwarara mata ruwan nan mai shegen sanyi, take ta saki wata ajiyar zuciya tare da tashi ta zauna. Mtsww! Alhaji ya ja tsaki ya ce

"Tashi ki bar min daki tun ban watsa maki mari ba." Ya dire maganar yana fadawa kan gadonsa cike da nishaɗi.

Mik'ewa ta yi tsaye tare da kwashe kayanta idonta na ci gaba da zubar hawaye da kyar take iya taka kafarta, ko da ta shiga bedroom toilet ta wuce ta haɗa ruwa masu zafi sosai ta shiga, kuka take tana karawa ta canza ruwa ya kai sau uku kafin ta ji dama dama har zuwa lokacin bata daina kuka ba, wankan tsarki ta yi sannan ta fita bata iya yin komai ba ta faɗa kan gado.

Tunanin irin rayuwar da zata yi da Alhaji take, don yau kam ta tabbatar da cewa Alhaji cikakken mugune, da wannan tunanin bacci ya kwashe ta, Alhaji kam daddaɗar bacci ya yi a wannan rana don ya fitar da abin da ya hana shi sukuni kiran sallar asuba ne ya farkar da shi, cike da nishaɗi ya shiga toilet ya yi wanka ya dauro alwala bayan ya idar ya koma baccinsa.

Zainab kuwa da kyar cikin dabara ta iya tashi tsaye, domin wani irin zazzaɓi ne ya kama ta jikinta ko ina ciwo yake mata sam bata jin dadin sa, ruwan zafi ta kuma haɗawa ta shiga sannan ta dauro alwala ta yi sallah akan sallaya bacci ya kwashe ta. Ita dai maganar Fatima ce ta tashe ta daga nannauyan baccin ta, buɗe idonta wanda suka mata nauyi ta yi tana kallon Fatimar.

"Lafiya kuwa sister?" Fatima ta tambaya tana kallon Zainab.

"Wallahi kin ga bana jin dadi sam da zazzaɓi na kwana."

"Ayya sannu tashi ki yi break sai ki sha magani."

Tashi Zainab ta yi ta nufi toilet, da kallo Fatima ta bita ganin tana dingisa kafa, Zainab na fitowa Fatima ta yi saurin fara tambayarta.

"Sis me ya same ki haka kike dingishi?"

"Ki bari kawai sister jiya bayan barin ki sasan nan na shiga toilet don yin wanka shi ne na faɗi, kinga wallahi sosai na bugu kafar ciwo take."

"Sannu ki rika gasata da ruwan zafi zata yi sauki." Fatima ta yi maganar cikin tausayawa.

"Ina gasata tun jiya na fara shi yasa ma na iya takawa."

Break ta soma yi suna hira da Zainab abin su gwanin sha'awa. Gefe daya kuma tana fargaban haɗuwa da Alhaji anjima.

Alhaji a office wuni ya yi yana tunanin Zainab, da yanayin da ya shiga a jiya sakamakon kasancewar su tare, lallai ya yadda sai da mata ake samun nutsuwa, sai Alla-Alla yake lokacin tashi daga office din ya yi ya koma gida don ya kara shan zumarta.

Ai kam yana komawa gida ya samu har ta rufe kofa, murmushi kawai ya yi don yasan bonono ta yi wai rufe daki da ɓarawo, sai da ya yi duk wani abu da ya zame masa al'ada sannan ya shiga ɗakinta, duk da kuwa ta sanyawa kofarta ki amma da yake yana da nasa sai ya yi amfani da shi, Zainab na kwance sai jin mutum ta yi a jikinta, ko kafin ta yi wani yunkuri har ya soma aiwatar da abin da ya kawo shi.

Yana jin tana kuka amma ko ya sarata mata sai da ya ga dama don kasan kafin ya barta, tun daga ranar Alhaji ya sanyata gaba da buk'atar sa sam bata da hutu da rana aikin Mummy da dare Alhaji ya hanata bacci. Zainab dai tana ganin rayuwa kullum tunaninta shi ne yau she ne burinta zai cika ta yi kuka ta yi addu'a amma kullum jiya i yau.

****
A bangaren IK kuwa Alhamdulillah domin ya samu nasarar kasance cikin daya daga cikin manyan club na yan ball ɗin duniya, tashin farko miliyan biyar suka saye shi take maigidan sa ya sayar da shi, shi kam IK duk sati biyu miliyan uku ake ba shi, nan da nan ya zama wani biliyan Naira sunansa babu inda bai zaga ba, ranar farko da ya ga alart na makudan kudaden da suka shiga account ɗinsa har kuka sai da ya yi, don bai taba tsammanin zai samu kuɗi kamar haka ba.

Yau kimanin watansa takwas kenan a Ingila, IK ya tara mahaukatan kuɗi wanda shi kan sa bai san yawan su ba a bin farin ciki kullum sai IK ya yi waya da iyayensa, addu'a fatan nasara suke masa a ko da yaushe, yanzu burinsa ya koma gida kawai ya auri Zainab tunda abin nema ya samu.

Kamar kullum yauma Alhaji ne ya bukaci Zainab ta je dakinsa, domin a matse yake tana shiga ya kai mata wani irin kyawawan runguma, har yana sakin ajiyar zuciya dan zame jikinta ya yi daga nashi, jin yadda jikinta ya yi wani irin zafi.

"Ke lafiyar ki kuwa?" Ya yi tambayar yana tsare ta da ido.

"A'a zazzaɓi ne yake damuna." Ta bashi amsa.

"Sannu sai ki sha magani don jikinki ya yi zafi sosai." Yana maganar ne yana ci gaba da abin da ya ke.

"To! Zainab ta amsa domin dai har ta saba da wannan zazzabin wanda kusan sati Uku kenan tana fama da shi."

Saurin toshe hancinta ta yi, don kwata kwata bata son kamshin turaren da yake amfani da shi.

Harara ya jefa mata ya ce

"Uban me kike wani toshe hanci?"

Kai ta girgiza tana toshe bakinta, domin ji ta yi kamar zata yi amai yan hanjinta sai yamutsawa suke yi.

Mtsww ya ja tsaki yana ci gaba da abin da ya ke, sam bai sarara mata ba sai da ya samu nutsuwa, tana ganin bacci ya kwashe shi ta gudu ɗakinta domin sam bata k'aunar kamshin turaren Alhaji da kyar ta iya jurewa wannan tarayyar ta su.

Tana sauka daga gadon ta soma kwarara amai kamar zata amayar da hanjinta, a rude Alhaji ya farka har bai san lokacin da ya soma mata sannu ba, ita dai sai aikin maida numfashi take har ta koma normal.

Manej ds page wallahi da kyar na yi typing ɗin, don bana jin daɗi, ina yinku fan's

Matsalar ba ku yin comments😏

     *RANO*✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now