Page 11

2K 99 2
                                    

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
                        *Z&R*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

*Ma su yi min addu'a Nagode kuma na samu sauki, ina godiya da kulawar ku a gareni, Allah ya barmu tare da juna*😍😍

*Comments yana karanci fa🤨 kuma kun dai san comment ɗin nan shi ke karawa  writers kwarin gwiwa, to a rika daurewa ana yi😍😍*

''' This page for you AMRAH AUWAL MASHI (princess Amrah)'''❤💚💜

                        1⃣1⃣

"Tashi ki gyara min bedroom tun muna shaidar juna." Maganar Alhaji kenan cikin daure fuska.

"Yanzu zan gyara ka yi hakuri." A sanyaye ta gama yi maganar. Haka jikinta babu kwari ta gyara wajen tas kamar babu abin da aka yi a wajen, har turare ta fesa a wajen.

Ta mik'e da niyyar komawa ɗakinta Alhaji ya hana, dole bata da yadda zata yi ta koma ta kwanta, rungumeta Alhaji ya yi aiko take wani aman ya tasowa Zainab duk yadda taso kar ta yi masa a jiki abin ya ci tura, don sai da ta wanke shi tas da amai ran Alhaji ya yi masifar tashi ko tausayin halin da take ciki bayyi ba ya wanketa da wawan mari.

Sosai marin ya shigi Zainab, a zabure ta sauka a gadon tana hawaye sai kakarin amai take, babu imani ya ce sai ta gyara masa gado ta wanke beedshit ɗin da ta bata, wayyo Zainab baiwar Allah haka ta wanke beedshit ɗin ta canza wani tana yi tana fitar da numfashi da kyar don ta galabaita, mugu Alhaji yana kallonta har ta gama.

Daki Zainab ta koma a wahalce ta kwana, daga dare zuwa safe sosai ta canza kamanni ta faɗa ta yi fayau da ita ga mugun zazzaɓi ga amai, babu mai tausayinta sai Allah, Fatima dake tausaya mata sun tafi Rano hutu, haka duk da yadda take ji bai sa Mummy tausayin Zainab ba sai da ta gama mata aiki sannan ta je ta kwanta.

*****

Dawowarsa kenan daga fili, yau sun buga wasa mai zafi sosai Allah ya basu nasara sune suka ci wasan, Allah ya sa IK ne ya ci masu, Jessy ɗinsa ya cire yana cikin kwance igiyar takalmin sa wayarsa ta fara kara haka kawai ya ji faduwar gaba, musamman da yaga Number Umar ne.

Dauka ya yi tare da sallama,

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Umar me ya same shi?"

Shiru ya tsara kafin IK ya ci gaba da magana "Zan shigo ko da zuwa gobe ne, don bamu da wasa cikin satin nan da satin sama please ka yi duk abin da yakamata kafin nazo, idan ma kano ya dace akai shi don Allah ku je samun lafiyarsa ya fi min komai."

Umar ya tabbatar masa zayyi duk yadda ya bukata, daga haka suka yi sallama, sam hankalin IK bai kwanta ba da ciwon mahaifinsa, in da ya godewa Allah basu da wasa a kwana kusa har ya je ya dawo tukun.

Aiko washe gari tun misalin sha daya jirgin su ya sauka Abuja, daga Abuja jirgi ya hau zuwa Kano, Umar ne da wasu daga cikin abokansa suka taro shi, kai tsaye cikin asibitin da aka kwatar da Malam Sa'idu sukawa tsinke, mutane sai kallon IK suke ciki mutunci yake gaisawa da jama'a har ya isa dakin da Malam Sa'idu ke ciki don daki na musamman aka aje shi, sosai IK ya firgita da yanayin da Babansa ke ciki, kankame hannunsa ya yi yana faɗin

"Baba kaine ka koma haka? Tun yaushe baka da lafiya amma baku sanar min ba?"

Malam Sa'idu ma kara rike hannun IK ya yi ya ce cikin wahalalliyar murya

"Ibrahim Khalil kai ne? Na gode maka Allah da ba ka kasheni ba sai da yazo, Allah ya yi maka albarka Ubangiji ya albarkaci rayuwarka, ko yanzu na mutu *BURINA* ya cika domin nasan zaka rike mahaifiyar ka da kannanka."

"In sha Allah ba zaka mutu ba Baba." Cikin kuka Khalil yake maganar

Baban ya bude baki zayyi magana amma ya kasa, yana rungume jikin IK Allah ya amshi ransa, kuka sosai IK ya yi daukar gawan Malam Sa'idu suka yi, suka tafi Rano inda za'a masa suttura.

Suna isa babu jimawa aka yi jana'izar sa a ka kai shi makoncinsa, sai mu ce Allah ya jikansa da gafara. Sai zuwa yi ma IK da mahaifiyarsa gaisuwa ake har aka yi kwana uku bai ga Zainab tazo masa gaisuwa ba.

Sosai ya cika da mamaki yau dai ya gaza hakuri suna zaune da Umar ya dubi Umar ɗin ya ce

"Wai kam Umar tun da aka yi rasuwar nan banga Zainab ba ko gaisuwa bata zo ba an ya tana lafiya kuwa, Kuma da Babanta aka yi zaman makoki, bai faɗa min komai ba sai dai ya ce min na yi masa hakuri ya yi min laifi, amma ban kawo komai a raina ba, don nasan ba wani mugun abu ya yi min ba, tashi mu je don na dubo lafiyarta."

Tun da ya fara tambayar hankalin Umar ya tashi, shiru ya yi ya rasa wani karyar zai zabga masa

"Ya ka yi shiru? Ko dai bata da lafiya ne? Hankalina yaki kwanciya tun ina can idan na ce ka kai mata waya sai ka fara yi min hanya hanya, don Allah Umar ka faɗa min gaskiya idan ba haka ba zan shiga wani hali."

"Ka yi hakuri IK wallahi tun ranar Baba ya ce a sanar maka, amma ina tsoron a samu wata matsalar ne shi yasa, amma ka yafe min."

"Zainab ta mutu ko? Hmmm! Shi yasa kullum nake mafarki da ita, ashe Allah ya amshi ranta." IK ya gama maganar hawaye suna zubowa daga idonsa.

"A'a bata mutu ba sai dai an auras da ita ga ɗaya daga cikin *MODIBBO FAMILY* zuri'ar su Alhaji kenan..."

Wani irin mik'ewa IK ya yi cikin tashin hankali wanda bai shiryawa zuwansa ba, tashin hankalin da IK ya shiga bai kai ta lokacin da babansa ya rasu ba, wasu hawaye masu zafi yake fitarwa, bakinsa har yana rawa ya ce

"Zee ta yi aure! Amma Zee ta ci amana ta har zata iya auran wani ba niba?"

"Kar kaga laifin Zee domin umarnin mahaifinta ta bi, ka yi mata uzuri domin karin kowa sanin abin da Zee zata aikata."

"Zee ce *BURINA* Umar, bani da Burin da ya wuce in aureta ba zan iya zama a garin nan ba yau zamu bar garin nan."

"Za ku bar gari zuwa ina ban gane maganar ka ba?"

"Babu amfanin zama na a Rano in har ba Zainab, yau zan dauke Umma da su Abubakar ba zan zauna anan ba na rasa Zainab *BURINA* na rasa Babana, ba zan iya jurewa."

Duk yadda Umar ya so fahimtar da IK amma sam yaki sauraronsa, haka ya shiga cikin gidan kamar mahaukaci, da kyar ummansa da taimakon Malam Ali mahaifin zee suka  lallashe shi har ya kwantar da hankali, sai dai ya cewa Umma zasu koma Kano a kwanan nan.

Ta yadda ta kuma sa albarka, don ita ɗin ma zaman Rano ya fita a kanta tunda mijinta ya rasu, dama kusan yan'uwanta a cikin Kano suke. Sosai hankali Malam Ali ba karamin tashi ya yi da jin batun komawarsu Kano, amma ya ya iya banda hakuri. Kwana IK goma ya koma cikin bakin cikin rashin Zee dinsa burinsa.

****

Zuwa yanzu Zainab ta tabbatar wa kanta da ciki gareta, domin rabon da taga al'adar ta tana wata na hudu kenan, duk wanda ya kalleta zai ba zai taba fahimtar yaro cikin dake jikinta ba, domin kullum cikin hijab take, shi kan sa uban tafiyar bai fahimta ba duk da kullum cikin addabar ta yake, ita kuma tana toshe duk wani hanya da tasan zai sanya su gane, don tana son cikinta bata son wani abu ya same shi, kuma tabbas idan har Mummy ta sa ni akwai matsala babba.

A fili ta furta "Babban BURINA na haifi abin da ke cikina lafiya."

Ko Fatima bata san da shi ba duk da irin shakuwar da suka yi da ita, Mummy tana zaune Zainab nata kai komo tsakanin falo da bedroom hankali kwance take aikinta, tsira mata Mummy ta yi kamar mai son gano wani abu, take gabanta ya fadi tana addu'ar Allah yasa ba abin da take tunani ba.

HaZainab  ta gota ta Mummy ta kwala mata kira cikin daga murya. Jiki a sanyaye Zainab ta k'arasa kusa da Mummy kanta a kasa

"Yau she rabon ki da ganin al'adar...?"



    *RANO*✍✍

BURINA COMPLETEWhere stories live. Discover now