Tsokaci

6.5K 766 63
                                    

" Wata irin gaba ce tsakanin talaka da mai kudi. Mai kudi yana yiwa talaka kallon nesa-nesa, irinka irin wahala, Allah nagode maka ba ni ba ne. Yakan kara yi masa kallon na fi ka, da gumina na nema kai ma sakacinka da mutuwar zuciya ya hana ka ka samu...ka da ka roke ni don baka nan lokacin da na nema!
      Talaka na yiwa mai kudi kallon barawo, azzalumi da ya handame dukiyar kasa. Sarkin izza wanda ya ci da rabonmu. Da a ce ni ne ke da kudinka da nayi abinda ka kasa yi, da na taimaki jama'a domin sai nayi yaki da talauci!
Amma abin tambaya anan shi ne mai ya sa ba a kallon mutum a matsayinsa na mutum dan adam sai a matsayin tattalin arzikin da ya mallaka ko ya kasa mallaka???
                                         Zahra Tabiu
                                             Mai Tafiya

Labarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeria mu ga yadda za ta kaya!

Mai tafiya..wani guzuri ka tanada?????

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now