19: TSAKANINA DA KE

7.2K 911 476
                                    

Ashe tsakanina da ke wani alamari ne mai ban mamaki? Ashe tsakanina da ke 'yanuwantaka ce? Ashe tsakanina da ke soyayya ce? Me ya sa abubuwa ba sa zuwa a daidai lokacin da ya kamata su zo? Me ya sa su kan zo a kurarren lokaci? Me ya sa????
                   Almustapha Iliyaso Tillaberi

( you may need a tissue paper, this is going to be a tough ride. Going on a break i have exams to write. Do not conclude until you have read the last chapter, the last sentence, the last word. Few chapters to go inshallah)

Hajiya Hadiza ke tafiya akan titin zoo road da ke kano. Tana hanyar zuwa wani biki diyar kawarta na nunawa sa'a. Nakasasshen mijinta ta bar shi a gida ko bi ta kan sa ba ta yi ba. Warin da ya isheta ne ma ya sa ta sa aka maida shi baskwata don ba zata iya ba.

Kiri kiri abokiyar zamanta Khulsumou da ke Niamey ta ki zuwa sai faman aiken malamai ta ke. To ita ina za ta iya? Ta godewa Allah Almustapha dan ta shi ke kan komai da ina za ta sa kanta?

Ta san in dai ta khulsumou ne da ta wawure komai ta gudu ta bar ta da salallami.

A zuciyarta ta kagu maigidan na ta ya cika ko ta rabu da alakakai. Dama ai kowa ya debo da zafi bakinsa ya ke kaiwa. Ita ta aike shi ya zalunci jama'a ga shi nan abu ya dawo kan sa zai shafe su. Inaa...ba da ita ba.

Wannan gidan bikin da zata je ta za ta hadu da matar mataimakin shugaban kasa dalilin ma da ya sa ta ci burin bikin kenen. Sun yi ajandar cewa za su hadu su tattauna kan batun 'ya'yansu. Akwai diyarta Ramlat da take yiwa Almustapha hange. Ta san sun dace yanayin arzikin gidajensu ya dace da juna.

Idan ta biyewa Almustapha ta san ba zai tsaya yayi zabe yadda ya dace ba. Gwara ta zaba ma sa wacce ta dace da shi yadda sunansa zai kara daguwa a idon duniya.

Wani abun ma shi ne ba ta ma san inda dan na ta yake ba ko wani hali ma yake ciki. Kwana 2 ma ba suyi waya ba. Dama haka halinta yake in dai ba wai tana bukatar kudi ba ko wani abu da wuya ta neme shi don a ganinta kar ta katse ma muhimman aiyuka.

Za ta neme shi da zaran ta gama da gidan bikin nan, dole ne ma ta neme shi. Tunaninta kenen.

Dama zaune take a bayan mota gefen mai zaman banza direba na jan ta. Da yake ma'abociyar karatun jaridu ce sai ta ce bari ta sayi jaridu akan juction. Ta siya aka ba su hannu suka wuce. Wani abu daya tak ne ya sa ma ta luguden zuciyarta. Labarin farko da ta gani a shafin jaridar daily news da kuma Nigerian ne ya girgiza ta. Ga abunda ta gani

 Ga abunda ta gani

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Mai TafiyaWhere stories live. Discover now