21: LOKACI

5.9K 695 339
                                    

Lokaci wani irin bahagon alamari...idan ba ka yi a sannu ba sai ya wuce ya barka! Ya kan tafi da abubuwa dayawa cikinsu har da raggon imani. Idan da rai da rabo, idan da yarda da aminci!

Cape Town, South Africa

Sauka yayi daga tasi ya shiga wasu runfuna na farmers market da ake siyarda kayan marmari.

Yawa yawan mazauna garin kan ji harshen turanci wasun su kuma yaren Afrikaans ko xhosa. Ya dubi dan tsamurmurin tsohon mai siyarda su inibi tufa da sauransu. Sai wani  sikeli babba da karami na awo da ke gabansa. Ya ce da shi a yaren Afrikaans

Hallo! Hoe gaan dit? (Barka, ya ka ke)

Dan tsohon ya washe hakora, na alamun farin cikin ciniki ya zo ya ce

"Baie goed, dankie" (kalau nake, nagode)

Mutumin ya ce da shi

"Praat jy Engels?" ( kana jin harshen turanci)

"n Bietjie "( kadan kadan) ya ba shi amsa yana murmushi, sa'anan yana nuna kadan din da 'yanyatsun sa.

Murmushi mutumin ya ma sa. Ya nuna masa abubuwan da yake so da dan yaren afrikaans din da yake ji kadan kadan da kuma alamu irin na kurame.

Ya gama saya, ya biya shi a kudinsu da suke ce ma rand  sannan ya ce da shi

"Dankie" (nagode)

Ya wuce.

Ya fara tunani, tasi ya kamata ya shiga ta kai shi summit clinic da ke Rondebosch medical center da ke nan capetown. Wani asibiti da ya kware wajen kula da duk wani abu da ya shafi kwakwalwa. Matar shi na can.

Ya tsayar da tasi ya shiga. Ya cigaba da kallon ledar hannunsa yana tunanin ko zata so ci? Sun shafe watanni amma ya ga abincin bai dame ta ba.

Ko ya zai gan ta yau? Lokacin ziyara yayi so yake ya leka ya gan ta ko da ba za ta ce komai ba.

Ya nisa ya nutsa cikin tunani na yadda lokaci ke tafiya babu kakkautawa. Shekaru goman da suka zo sun zo ma sa da wasu al'amura da baya ko son tunawa.

Wai ashe dama haka duniya take? Haka lokaci yake idan duniya na yi da kai? Sai ta daukake ta daga ka sama ka ke jin kan ka a gizagizai? Lokacin da ta ga dama sai ta sake ka fado! Irin faduwar da ba lallai ka sake doruwa ba.

Shi Almustapha Iliyasou Tillaberi yana da labarun bayarwa game da rayuwa. Mamaki yake yi yanda a yau zai shiga Najeriya a garin kano amma ba lallai a samu mahaluki daya da zai daga ido ya kalle shi ya ma sa kallon sani ba. Rayuwa ta canja!

An wayi gari babu I and A group of companies. Wani alamari da yake tunanin ba zai taba faruwa ba a duniya.

Tun bayan bata ma sa suna da aka yi investors dayawa suka janye hannun jarinsu, masomi kenen. Sai ya zamana cewa babu wasu manyan kamfanunnuka ko qungiyoyi da za suyi trusting din sa su saka dukiyarsu.

Sannu a hankali abubuwa suka fara ja baya. Ba a shekara 2 kwarara ba sai da kamfani ya rushe. Kamfanin da ya sha gwagwarmaya kafin ya tsaya da kafafunsa. To amma a lokacin ya san a halin da ake ciki ko da akwai investors ma kamfanin ba zai je koina ba.

Domin shi ma ai ba a hayyacinsa yake ba. Idan ya tuno mafi yawan dukiyar I and A haram ce sai ya ji babu mamaki da ya ruguje.

Dukiyar a cakude take da kudin caca! Sa'anan rabin dukiyar an ciwo ta ne ta haramun domin kuwa kashe Ahmadou Tillaberi aka yi aka handame.

Bai kara tsorata da duniya ba sai da mutuwar mahaifinsa, mutuwar da aka rasa wanda zai yi ma sa wankan gawa!

Wai kamar mahaifinsa wanda ya girma ya daukaka a duniya aka rasa wanda zai sa hannu a wanki gawarsa saboda tsananin wari.

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now