11: TARKO

5.4K 873 395
                                    

Tarkon so....tarkon kauna.

Kano, Nigeria

Ayye mama ayye mama, mama ye iye
Ayye mama labo labo, mama ye iye
Da aure ya kan raba aure, mama ye iye
Da na biki mun tafi tare, mama ye iye

Kandala ta cigaba da rera wakarta tana jefa danwake. Dirkekiyar mace ce da ta doshi shekara 50 a duniya. Fuskarta na dauke da fashin goshi, yanayin fatar jikinta tayi haske irin na bilicin da kuma dabbare dabbare na tabubbukan da bilicin din ya bar ma ta. Lebanta sun yi baki sidik saboda shan taba.

Jikinta sanye da wata atamfa code vore da aka yiwa dinkin zurmemiyar riga mai aljifai na saka kudi. Fuskarta ba yabo ba fallasa tana jefa danwakenta na siyarwa da yayi suna. Daga wajaje daban daban ake zuwa saya a wani kango data kama. Tana da kananan ma'aikata masu zubawa mutane da mika musu.

Kandala wata tsohuwar karuwa ce da duniya ta yi mata atishawar tsaki daga karshe ta qarke da sana'ar danwake. Ba wai ta daina kananan iskance iskance ba ne, kawai dai yanzu duniya bata ta tata.

Daga gefenta kadan Rukky ce kwance akan wata tabarma tana ta bushe bushenta na iska. Sanye take da wani wando tiri kwata da ya kame ta tsam, ta sa wata riga marar hannu. Duk wanda ya shigo kangon nan yakan zuba mata ido cike da mamakin rashin kunyarta amma ko a jikinta.

'Yan iska kuma zauna gari banza su ke jifanta da fito ko yabo amma babu wanda ta kula.

Sai ma ta kara mikewa ta dago kafarta tana karkadata a hankali. Duk na mujiyar mutanen nan ma su siyan danwake su fice bai dada ta da kasa ba.

Wajen danwaken kandala wani waje ne da Rukky ta mayar wajen nishadi. Anan ta kan zauna idan bata son magana da mutane tana so ta kadaice tayi tunane tunanenta na duniya. Haduwar jininsu da Kandala ya sa ta mayar da gurin wajen zuwanta ko banza ta mata hirar duniya.

Tana wannan kwanciyar ta lissafa yawan wakokin da kandala ta rera a zamanta na kasa da awa biyu. Ta rera sama da 20..tana kan ta ashirin da daya. Shin wannan matar na da matsala kuwa? Ta dauke tunaninta daga kan wakokin kandala ta koma tunanin abunda ya shafe ta.

Burinta a duniya bai wuce ta kai wa makiyanta farmaki ba..to amma ta yaya. Ta zata i yanzu ta gawurta ta kai matsayin da za tayi fito na fito da su to amma abun ya gagara. Ga shi ba ma ta da wani takamaiman labari a kan su. Idonta idon Iliyasou Tillaberi ko wani da ya dangance shi, to kashinsu ya bushe.

Muryar Kandala tana aiken wani yaro shi ya tsayar ma ta da tunaninta.Ta ji ta ce

" kai ajiye kwanonka a nan in aike ka"

Ta zira hannu a daya daga cikin aljifan rigarta ta zaro N20 ta baiwa yaron ta kara cewa

" maza maza je ka shagon Namadi ka siyo min taba rotmans..idan ka siyomin benson sai na ci uwarka..."

Ta karasa tana nuna masa danyatsanta sabbaba alamar gargadi. Sai daga baya ma ta karewa yaron kallo ta washe hakora ta ce

" Au...au..ashe ma isuhulle ne na wajen tabawa....ai ga idon nan irin na uwarka..maza je ka kafin ka dawo an zuba maka"

Yaron ya fyalla a guje. A wannan lokaci ta gama jefa danwaken ta dauraye hannunta ta goge a jikin atamfarta. Masu saya sun fara raguwa dan isuhulle ya kawo mata tabar ya dauki kwanon danwakensa ya tafi.

Mutane suka watse saboda danwake ya kare sai masu taimaka mata da ke wanke wanke. Zaune take aka kujera 'yar tsugunno ta kunna wannan tabar ta fara zuka a hankali. Sai ta karkato da jikinta gaba daya tana kallon Rukky ta ce da ita

" Yarinya ki bar zuke zuken nan..kar ki je ki haukata kan ki a banza a wofi!"

A hankali Rukky ta taso daga kwanciyar da take ta kurawa mata ido da lumsassun idanunta. Kallo ne take mata na 'ke me kike yi'. Kandala tayi murmushi ta ce

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now