13: DAGA ZUCIYA

4.8K 613 163
                                    

Son kasancewarmu tare daga zuciya ne!

Kano, Nigeria

"A'ataqidhu inni waqa'at fil hub!"
( ina tunanin na fada soyayya)

Luba ce ke zuba wannan zance a gaban Hindu , Rukky da 'yar modu. Zaune suke a falon Hajiya Kububuwa ana taya Hindu kwashe kayanta za ta koma sabon gida. To amma aikin na su bai je ko'ina ba saboda abun almarar da Luba ta shigo masu da shi. Bin ta kawai suke da kallo saboda tsananin mamaki. Ta ce

" Sai ina ganin kamar ba ni ba ce. Kun ga Almustapha kuwa Wow..mashallah..mashallah. Ban taba haduwa da mutumin da na ji ina son shi farat daya kamar shi ba! Ai kwana biyun nan da ba ku ganni ba ina gidansa. Kun ga gidan? Aljannar duniya!Dole ne yau na wuce wajen Iyannan na gaya mata yau fa na samu mijin aure! Don bazan juri na ga Almustapha da wata ba! Almustapha...ya rouhi..ya habibii qalbee!"

Rukky ta taso ta zunguri Luba ta ce

" Wai mafarki ki ke ko idonki biyu? Ko dai wani abu kika sha ya gaya miki karya? Na ji har kina batun aure"

Luba ta ce

" Garau nake ras! Ai daga nan wajen Iyannan zan je kawai ta fara shiri"

Rukky buga tsaki tayi ta koma ta zauna ta ce

" A duniyar nan dai luba, a yanzu ban ga son da za a yi masa marmarin aure ba!

Ta koma ta zauna.

Luba ta yi mata kallon sakaka. Sannan ta taso ta zungureta ta ce

" Sukari kin san wanene wannan mutumin kuwa!Uban gidan Idi maina ne fa. Ai irin wannan ba ka dangwali arziki ka bar shi ba! Ka bar shi ka je ina? Ai gwara ka samu gurbi ka dawwama anan daga 'ya'yanka har jikoki sun huta da jaje! Me aka yi da maza in ji karya!Idi Maina ma mene ba a samu a jikinsa ba ballantana ubangidansa."

Rukky ta ja dan karamin tsaki ta ce

" Ai ko wanene tsakanina da shi mu rabu a hanyar da mu ka hadu. Kurunkus!Wai tukunna ma dan gidan wanene?"

Luba ta yi ma ta kallon uku saura kwata ta ce

" ji fa! Ji fa sukari da wata irin tambaya. Yo...idan kin ji ana waye ubanka ai kai ba wani ba ne! Shi fa ogan Idi Maina shi ne shugaba kankat. Shi ke da kamfani shi kuma ke juya kowa da komai. To ina ruwana da ubansa? Tunda ba shi ba ne mai kudin. Watakila ma wani tsohon matsiyaci ne can a kauye, dan ya tura masa a bunda ya sauwaka. Ni ko aurensa nayi ko inda danginsa suke bazan dosa ba!"

Sai a lokacin Hindu ta saka baki ta ce

" This is surprising yau da bakinki Luba kike ambatar aure? Gaskiya zan so in ga wannan mutumin dan na san ya isa! Isar tasa ma ta isa!"

Luba ta miko mata hannu suka kashe.

Sai a lokacin ' yar modu ya tashi yana rawa yana rera wata waka

" Ayyaraye daure jure
Zaman gidan wani tilas ne
Zaman gidan wani sai hakuri
Ai ba da kan ki aka fara ba
Ai da da kan ki aka fara ne
Da kin yi kuka kin koshi

Hindu ce ta taso ta biye masa suke taka rawa. Wai su a dole aure ya zo har ya tabbata.'Yar modu ya karkace baki ya rangwada guda suka tafa da Hindatu ya ce

" Wannan abu yana min siga! Muna jin aure a makwabta yau bana dai tamu za mu kai. Kuma dama ai abun na Allah ne budurwa da jika. Da haka da haka mu ma za a zo kan mu , ba mu fidda rai ba Alquran! Eh ai muna gayawa Azza wa jallah. Kawata lubancy ni zan miki babbar kawa. Billahillazi rabon cingan daga nan har kawayenki na kwatano. Abu namu maganin a kwabe mu! Ahayye Allah na dawo!"

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now