6: MUTUWA MAI TONON ASIRI

8.8K 875 390
                                    

Mutuwa mai yankan kauna, bakin takobi mai raba soyayya!

Niamey, Niger Republic

A shekara 18 babu wani namiji da zai daga ido ya kalli Rokaiyatou ba tare da bukata daya ta mamaye ran sa ba, na ya mallaketa har abada. Amma a zuciyarta mutum guda ne kacal! Frère Momodou. Idan da shi a duniya to ba ta ki sauran maza duk a hada ayi jana'izarsu ba wannan ba matsalarta ba ce!

Sau da dama takan yi tunani a duniya akwai irin Frère kuwa? Dan adam guda daya tal da zai iya maye gurbin dangi guda ya zama kamar uba? A so da kauna, tausayi da jin kai babu ya Frère duk duniya a hasashen Rukaiyatou. Shin wai da babu shi wata irin rayuwa za ta yi ita da Momma. Shi ya tsaya tsayin daka cin su, shan su, karatunta tun daga Ècole Elementaire har Ècole Secondaire.

A halin da ake ciki yanzu Momodou yana kasar Faransa a wani gari mai suna Montpellier. Ya gama digirinsa na biyu da dadewa amma fafur mahaifinsa ya ki ya dawo gabadaya. Ya dora shi akan al'amuransa na kasuwanci ba shi Faransa, ba shi Nigeria ba shi Niger.

Da gaske mahaifinsa yake bai son ya dawo, tsakaninsa da Niamey sai dai idan ya zo ziyara. Ya gama gane cewa duk kan maganar Rokaiyatou ke ya sa yake ma sa walagigi da rayuwa na kusan shekara biyar. Ko son yayi maganar aure ba ya yi ga shi shekarun sa sun ja. Da wannan aniyar ya dawo gida wannan shekara. Rokaiyatou ta gama Ècole Secondaire aurenta a yanzu ba gudu babu ja da baya!

Da wata safiya ne Rukaiyatou na tsakar gida tana tankaden garin tuwo yayin da Momma ke dinkin hula akan tabarma. Ta dube ta cikin farin ciki ta ce

"Momma sakamakon gwajinmu ya hito kuma na kokarta na san Frere zai nema mun Universete ko amren namu za a yi?"

Momma ta buga tsaki ta nuna ta da dan yatsa ta ce

" ke ki fita idona, ni ki ke yiwa maganar aure?"

Rukaiyatou ta kwashe da dariya ta ce

" To gwada mini wa nake da shi baya ga ke?"

Momma tayi dariya suka cigaba da hirarrakinsu a ran Rokaiyatou fal tunanin Momodou

A lissafinsa satin da wuce ya kamata ya zo, to amma har yanzu shiru. Sai ta yini sukuku ko me ya rike shi ga Faransa? Ta kwaso kwanukansu ta kawo bakin rijiya don ta wanke, ta hado da wata tsohuwar rikodar momma ta kamo gidan radio. Ta fara wanke wanke ta ji sun sako wakar Sogha Niger, wayyo dadi zai kasheta don tana son wakar dankwali. Ta fara bin wasu baitikan tana aikinta kamar da ita aka rera

A can da dauri,
An ka je yin wasa
'Yanmata su sanyo kwalli,
Sauran sai su sa janbaki,
Sai a taru hilin wasa
Samari sai suna wilgawa,
Ka ga wacce ranka yake so
Hitilla ce ka ke matsawa
Rawa da waka rannan sai sahe....

Duk sallamar da ake yi ba ta ji ba, sai kamar daga sama ta ji an ce

"Bonjour!"
( ina kwana/ ina yini)

Ta dago da sauri tana mai kashe rikodar jin muryar Momodou. Kawai sai ta sa dariya cikin wata murya ta ce

"Frère!"
(Danuwa)

Shi ma ya sa dariya. Ta dago ta kare ma sa kallo ya sa riga mai dogon hannu fara tas da bakin wando. Takalminsa ma baki ne sau ciki daga ganinsa fes fes. Jikinsa ya nuna alamar hutu, da wata karamar jaka a hannunsa daga alamu ko gidansu bai shiga ba dirowarsa kenen. Da ta kare ma sa kallo sai ta ji gabanta ya fadi sai take ganin kamar ya fi karfinta.

Murmushi ya sakar ma ta ganin kamar ta fada tunani ya ce

"Comment allez-vous"
( ya ki ke)

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now