17: SHARRI KARE NE...

5.8K 611 287
                                    

Ai sharri kare ne, mai shi yakan bi!

( i think i'm about to take a break)

Kano, Nigeria

Shekaru kadan da suka wuce

Harabar La mirage cike take da manyan motoci na masu fada a ji, wadanda shedan ya buga musu ganga suke taka rawa. Ranar ta kama asabar yawan yawan ma'aikata da suke Abuja da kaduna sun shigo hutun karshen sati. Mafi yawansu kan rashe a wannan waje domin nishadi, suna taba dan shaye shaye da caca.

Wannan karin wani mawakin Hausa suka dauka mai suna "dan mudubi". Sukan yi hakan idan sun so nishadi ko su dauko masu garaya suna wake su kan su na fasuwa.

A ranar dai waken dan mudubi bai wuce kan Almustapha ba. Almustapha bai fasa yi masa ruwan nera ba kamar bai san ciwonta ba!. Ran dan mudubi fes! Har yakan ce

Ka ga Mustapha gwani na gwanaye!

Yaro da kudi abokin tafiyar manya

Mai takalmin karfe kowa ka taka ya taku
M
usty nera ka je las vegas sun buga sun kyale!

Wanan abu kan fasa kan Almustapha, sai ya dunga jin kamar shi kadai ne ya gawurta duniyar! Aka dunga cika masa kofi da gulder yana sha yana barin nera!

Akwai wani da ake kira Hafeez kamala. Wani matashin yaro ne mai irin zubin Almustapha. Shi ma gwanin caca ne ba karya kuma wannan kirari na dan mudubi yana sosa masa rai. Yaushe Almustaphan ya shigo bariki har da zai nuna musu ya isa? Karamin yaro dan haure asalinsa ma ba dan najeriya ba! Ya za a zo garinsu a fi su da rawa sa'annan a bi su tsinannen duka?! Ina ba za ta yiwu ba!

Almustapha ya cigaba da cika tambulansa da giya yana durka ma cikinsa, yau nishadi yake ji! Wani abu da bai cika yi ba, buguwa da giya. Na kusa kusa da shi mazigansa da suke kiran kansu masoyansa sa suna kara ingiza shi nuna masa duniya fa ba komai ba ce.

Ana cikin wannan shagalin ne da Hafeez kamala fa ya lura Almustapha ya yi tatul sai yayi challeging din sa da caca. Ba ai wata wata ba aka share fili ana shirin ganin wannan wasa tsakanin gwanaye biyu. Kowa yana da magoya bayansa 'yan shaida. Ba a komai sai iface iface da kumburawa mutum kai.

Sai a lokacin Hafeez kamala yace

" idan ka cika kai gwani ne na gwanaye. Yaro ne kai abokin tafiyar manya. Ga dan mukullin mota ta. Sabuwa ce dal! Zuwan shekaran jiya. Benz ce da za ta kai kimanin naira miliyan ashirin. A yau na sata a tsakiyar fili idan a yau kai ka ci cacar nan na ba ka ita!"

Ya dauko mukulli ya aje bisa tebur

Waje ya dau ihu da sowa Almustapha yana murmushin takaici. Kamar shi har za ayi challenging irin haka? A la mirage babu gwani kamarsa! Zai nunawa Hafeez Kamala ya ci ubansa ya dama a caca!"

Ya ce

" Na ka wasa ne. Me aka yi aka yi motar miliyan 20? A gurinka take kudi. Sabon kamfaninmu da zamu bude da zai doke kowani kamfani na sayarda kayan masarufi a Arewacin Najeriya gabadaya shi zan aza bisa tebur! In ka isa kai gawurtacce ne sai ka nuna a daren yau!Idan ka ci ni ka dauka na baka halak!"

Yawa yawan mutanen gurin sun ga wautar Almustapha to amma su fa 'yan abi yarima a sha kida ne. Sun san giyar kudi ke rudarsa, Idan ba don haka ba wa zai yi wannan gangancin?

Hafeez kamala ya ce a fusace

" karya kake ba zaka iya ba! Idan za ka iya dauko takardun a aje bisa tebur idan ka haihu cikin uwarka"

To wannan abu ya fusata shi har ya bazama dauko takardun da ke compartment na motarsa. A ranar ya karbo su daga inda ya bada a ajiya a banki, mahaifinsa zai saka hannu à wani waje. Sai akai rashin sa'a wannan muhawara ta ritsa da su.

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now