8: SABO DA MAZA.....

7K 1K 357
                                    

Sabo da maza jari ne!

Kaduna, Nigeria

Bayan shekara biyar

Alhaji Balala-Cinye-du ya duba tsadadden agogonsa na hannu ya ga karfe 10 cif cif na safe, ya ja dan karamin tsaki ganin cewar ya makara. "Bidding" garesu na motoci kuma karfe goma ne daidai ga shi har goman ta masa a daki. Ya dauki hularsa mai taken minista baka ya dora akan Farar shaddarsa mai babbar riga. kallo daya za ka yi wa shaddar kyaunta ya fallasa tsadarta. Sai ya saka takalma rufaffu sau ciki.

Ya tsaya yana kallon kan sa a gaban mudubin dogon yaro kamar wata 'yar budurwa mai tashen budurci. Baki ne mai matsakaicin tsawo gwani na saka fiskar gizago musamman idan mutum ba dankwali ya daura akansa ba.

Dan kasuwa mai samu fiye da daidai misali amma iyalansa ba su wadatu daga hakan ba. Ya gama shirinsa tsaf ya rufa da fesa turare da yake mutum ne mai son gayu na birgewa. Shekarunsa ba zasu wuce 45 ba amma idan ka gan shi ba za ka ce ya kai 40 ba.

Ya dauki "brief case" da ke dauke da farare bugun Abuja ya rike ta kyam sannan ya kulle kofar sashinsa ya jefa mukulli a aljihu. Ya tako taf taf kamar wani ingarman doki ya shigo sashen iyalinsa cikin takama da izza.

Kallo daya zaka yiwa matar ka zata 'yar aikin gidan ce idan ka karewa yanayinta kallo. Wata kodaddiyar cheras ne a jikinta da ta sha wanki da takalmanta silifas dan madina tana aikace aikace a tsakar gidan. Gida ne yalwatacce ginin zamani sai dai kana zuwa za ka gane babu kulawa.

Duk irin tarin dukiyarsa matarsa Lantana rura gawayi take don tayi girki. Ya karaso gurinta da niyyar ya bata kudin cefanen ranar kawai sai wani almajiri mai zakin murya ya katse shi

Maula ta sidi maula ta balarabe, maula
Muna bara a bamu domin annabi, maula
Kowa ya bamu ya baiwa annabi,
maula

Alhaji Balala ya daka wata mahaukaciyar tsawa ya ce

" wani dan iskan yaro ne anan? Don iyayenka kar ka kara zuwa mun gida tunda bana ubanka ba ne!Shi ma uban naka ai ya san da yunwar ya turo ka almajiranci. Wai tukunna ma Lantana ba na ce a dunga garkame gate din nan ba saboda shigowar sakarkarun yaranan?"

Ya cigaba da sababi Lantana kuma ta cigaba da kujiba kujibar aikinta ba ta ko bi ta kan sa ba. Sai ma tana hura gawayinta ta soma rera wata waka

Wayyo wayyo habiba yardamalmala
Dan Allah zo gareni yardamalmala

Alhaji ya kule. Ya lura da take taken Lantana kwanan nan sai ya ce

"Wai Lantana ba magana nake miki ba kika mayar da ni mahaukaci. Tukunna ma bana hana wake waken nan na wasan hausa ba?"

Cikin halin ko in kula ta ce

" O'o ni ba kayan kallo ba ina zan kalli wasan hausa? A bakin yara na ke ji idan sun je makwabta kallo sun jiyo"

Wani haushi ya turnuke shi ya ce

" Au don lalacewar tarbiyya har yaran nawa kike bari su shiga makota kallon wasan hausa? Kina da hankali kuwa Lantana?"

Ta watso ma sa wani kallo wanda bata taba yi ba har sai da Alhaji ya ji ba dadi. Kan sa ya daure? Wai me ke faruwa ne? Wa ke zuga Lantana? Abinda yake gudu fa yana neman ya faru dalilin kenen da duk aure aurensa bai taba auro 'yar jami'a ba.

Me akai akai 'yar jami'a fitsararrun yaran mata da kan su ya gama wayewa da 'yanci, yaya za ayi su lankwasu? Komai kana yi tana jin daidai take da kai. Ya fi ganewa mai karancin wayewa komai aka gaya ma ta ko bata so ta yi.

Amma mamakin Alhaji bai kai kololuwa ba sai da ta mayar ma sa da

" Yaya za a yi in yi hankali kadangarun barikinka su ma suyi hankali? Ai abun sai yayi mana yawa"

Mai TafiyaWhere stories live. Discover now