Babi na 1

2.4K 120 1
                                    

       Gudu yake kan wani farin doki mai kyaun gaske da ka ganshi kasan a rude yake ,wata mata ce a bayanshi ta ‘kank’ame shi sai zare ido take yi yayinda shi kuma sai ‘kara gudu yake ,da an hau tudu ko tsauni sai matar ta sa ‘kara ta rike ciki da hannu daya, da ‘kyar ya samu wani kogon dutse ya shige ga dukkan alamu Matar na’kuda take yi domin dauke take da juna , ‘karar dawakai da yaji sun tukaro inda kogon yake yasa ya toshe wa Matar baki da hannun shi ganin tana kuka duk jikinta yana b’ari ,mutanen suka gama dube -duben da zasuyi sai wani daga ciki yace “sun yi nisa sosai!! Mu koma kawai ,a lab’en da suke babu wanda ya motsa har mutanen suka tafi sannan ya cire hannun shi daga bakin Matar da tuni na’kuda ya zo mata gadan-gadan, Allah cikin ikonsa ya jiyo ‘karan ruwa daga d’ayan ‘bangaren kogon ya ja mayafin ta ya nufi hanyar da gudu ,kafin ya dawo ma har ta haifu Yar cikin Jini Kwance a ‘kasa itama uwar haka ,ruwan da ke jikin tsumman ya d’an matsa a fuskar ta ta dan farfado ,shi da kanshi ya gyara yarinyar ya mik’a mata. Murmushi take yi tana hamdala amma hawaye ne zafafa ke bin kuncin ta ,ta sumbaci yarinyar sannan ta rufe idonta hannunta ta sa ta damk’e hannun mutumin wanda da ka ganshi kaga sadauki, tana salati rai yai halinsa.
         wani ‘kara mutumin ya saka wanda duk kogon sai da ya d’auka, ya kifa kai a cikin matar yana ta rusa kuka mai ban tausayi ,idanuwan shi suka rine kamar garwashi ya mik’e tsaye ya d’aga jinjirar sama cikin murya mai firgitarwa yace” masarautar KALAHARI !!! Sai na mayar muku jin dad’i da walwala !! Na lashi takobi!! da ikon Allah sai  JASEENA ta zamo ciwon ido ga azzalumi JALALUD-DEEN!!!!
          

Asalin labarin
         Masarautar Kalahari babbar masarauta ce wanda ake sakota a matsayi na farko cikin jerin masarautu, mai kuma cike da tarihi, mayak’a da kuma kayan ma’adanai na ‘kasa kamar su lu’ulu’u , gwala-gwalai da sauransu. Sarki Hameed shine ke mulkin Wannan masarauta, mutum ne jarumi ,mai tausayin talakawa gashi da kwarjini. Hameed shine d’a na  biyu kuma na k’arshe gun mahaifin su ,ma’ana yana da wa mai suna JALALUD-DEEN ,wanda ya kasance baya son talakawa kuma shi duk abunda zai yi in dai don ya musguna ma talaka ne toh ya fi burgeshi, son zuciya gareshi , hakan ne yasa da aka tashi bada sarautar sai dattijawan gari suka zabi a bawa Yerima Hameed kasantuwar d’abiun sun daban ne kwata kwata JALALUD-DEEN bai chanchanta ya mulki Kalahari ba, a fuska JALALUD-DEEN ya nuna babu wani abu amma dai na ciki na ciki !!domin zuciyar sa tafarfasa takeyi kuma a nan ne ya k’udiri niyyar ganin bayan Hameed !!!

JASEENA Where stories live. Discover now