Babi na 16

585 57 0
                                    

Ita mikiya wata tsuntsuwa ce wadda zata iya rayuwa har tsawan shekaru saba’in, amma domin kaiwa wannan Shekarun ,dole sai ta d’auki tsatsauran matakai,domin lokacin da takai shekaru arba’in dogin faracinan ta zasu zama basu da karfin neman ko kuma chafke abunda zasu samu a matsayin abinci,wannan dogon bakin ta mai kaifin zai kwanta (lank’washe ) fukafukan zasu zama tsofaffi, masu kauri kuma ga nauyi , wannan fukafukan masu kauri da nauyi ,zasu zama kamar a k’irjin shi suke hakan zai basu wuya wajen tashi sararin samaniya daga nan ne mikiya zata zama bata da wani zabi wanda ya wuce guda biyu kachal  ko ta MUTU ko kuma ta rayu cikin salo mai wuya na neman SAUYI! Hakan yana bukatar mikiyar ta tashi ne sama ta hau kan tsauni ,ta zauna cikin gidanta (nest) sannan sai Yayita buga wannan tsohon bakin nashi jikin dutse har sai ya fincike shi , sannan wannan mikiyar zata bari har sai sabon ya fito sannan sai ta fincike tsofaffin faracinan ta da shi ,lokacin kuma da wadannan faracinan suka fito ,sai ta fara fiffige tsofaffin fukafukan nata da shi wannan shine chanji da yafi ciwo zafi!! Toh daga nan ne wannan mikiyar take sake daukan sabuwar rayuwa ta sake yin wasu shekaru talatin din a gaba! ME YASA AKE buk’atar CHANJI??? Saboda a rayu kuma ayi zamantakewa!! Muma dole mu bi hanyar SAUYI!!! Amma ba kamar mikiya ba ,Muma dole mu sauya munanan d’abiun mu zuwa kyawawa da kuma abubuwan da muka aikata marasa kyau zuwa masu kyau ,mu zama masu koyi da abunda addini ya zo mana da shi!!
Saboda haka domin daukar hanya zuwa wannan SAUYI sai ku watsar da wadancan d’abiun domin samun sababbi ,duniyar da fadi take amma mu bita a Sannu! Ku bude ajiyayyan k’wak’walwar ku don ku Adana wannan ko zaku tashi da sabuwar rayuwa irin ta mikiya!!!……..
Kowa yayi shiru jiki a sanyaye ,fadar tayi dub kamar babu wata halitta a cikinta , wasu na hawaye amma hawaye ne na farin ciki cewa yau gaskiya ta dawo masarautar Ramali! Wani dattijo ya mik’e yace ” wannan haka yake yarima Haidar! Muna tare da kai ! Dattijawan gari suka na’da Haidar a matsayin sarkin Ramali , ganin yadda komai yazowa Haidar cikin sauk’i yasa Rizwan ya mak’ale mishi yace shi zai raka shi masarautar Kalahari don ya nemi gafarar mutane wata’kila in yasa baki za’a yafe masa shashanci da yayi ta aikata musu ba dare ba rana,nan suka sake sabon shiri dukan su tare da wasu mayak’a guda ashirin suka d’au hanyar Kalahari……

JASEENA Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz