Babi na 10

615 78 0
                                    

Haidar ne a kan doki suna Jere shi da wasu ,yayan sarakuna ,Jaseena da ke zaune a bene na farko kuma na k’asa ita da su Jauda kawai ta mik’e ba shiri ,su Aisha ma suka mike suna tambayar ta ko meyasa ta zabura haka? Fuskar ta babu almuru tace ” tabbas na san wancan !! Shine Rizwan d’an sarki Jalalud-deen !!! Me kuma yake yi anan ? Duk yadda akayi sarki Jalalud-deen ma yana nan !!” Aisha tace ” kice ba mu muka je neman su ba su da kansu sun kawo ‘kafar su inda ya dace!!” Duk suka bushe da dariya ,chan kuma sai Jaseena tace ” toh amma ai in an gama gasar yau gobe zasu tafi ko ?” A tsare Meenah tace ” sati biyu ake yi ana wasannin lallai muna da dama ” duk suka jinjina kai ,yayin da Jaseena tayi murmushi cikin ranta tace ” lallai Wannan Meenah d’in y’ar ganin dama ne !!.
Tun da aka fara tseren dawakai Haidar ne ke Jan ragamar Kwatsam sai dokin shi tayi wani irin ‘kara ta tik’a shi da k’asa ta yi gaba ,yarima Rizwan wa wuce shi yana masa wata muguwar dariya gami da cewa “Wannan karon kam baka isa ba!!! ” dokin Haidar da ya fita a guje ya zagayo ta inda su Jaseena ke zaune kawai se ta mik’e tayi tsalle ta fad’a kan dokin ” Hyaaaa!!! ” ta sa gudu ,ganin yadda ta kusa cimma Rizwan yasa sarki Jalalud-deen ya mik’e tsaye yana zare idanuwa.
Gudu suke daf da daf da ita yayinda Rizwan ya kasa mai da hankalin shi kan tseren ,abunka da mayen mata ,ya tsura mata ido ita kuwa ta sakar masa da wata hadaddiyar murmushi wanda ya sa sai da ya kusa tsaya wa. Sai da ta tabbatar ya gama rud’ewa kawai taja linzamin dokin ta kara gudu har ta tsallake Jan layin da aka zana ,ta zo na d’aya ,bak’in ciki ya sa Rizwan ya gagara k’arasawa yayin da idon Jalalud-deen suka rine tsabar haushi ace duk shirin da suka yi na ganin sun ci amma hakan bai yiwu ba?
Mutanen gari aka hau ihu ana Jaseena! Jaseena !! Jaseena!!! ,Wannan sunan da aka kira yasa sarki Jalalud-deen d’agowa cikin sauri yana kallon Jaseena !tabbas babu maraba tsakanin ta da mahaifiyar ta ,saidai a tunanin shi wata’kila idon shi ne ke mishi gizo sai yayi tsaki ya juya ya bar wajen ,yayinda Rizwan da sarkin yak’i Amjad suke taka mishi baya.

JASEENA حيث تعيش القصص. اكتشف الآن