Babi na 20

1.1K 75 9
                                    

BAYAN SHEKARA D’AYA
Zaune yake kan kujerar mulkin sa yana magana da waziri Jabeer ,sarki Haidar ne cikin kaya na alfarma na sarauta sai hira sukeyi wanda har masu gadin ma suna saka baki , ana ta raha, chan waziri yace ” Allah ya baka nasara zan iya yafiya yanzu?” Haidar yayi murmushi yace me zai hana ? Ko so kake kayi tafiyar dare baka ga yamma ta kawo kai ba ? Waziri Jabeer yayi murmushi ya mik’e ya nufi hanyar fita.
Dank’o ne a hannun ta irin na Harbin tsuntsaye ta saita shi a kan kujerar ta sake masa daya a hannun shi ,ko girgiza bai yi ba ya basar ,har tayi sau uku ,sannan ya juya don ganin me aikata masa hakan. Had’a idon da zasuyi kuwa ta zaro manya manyan idanuwanta da suka sha ado da kwalli:oops: sannan ta tattare doguwar rigarta ta ruga a guje ta fice zuwa lambu , murmushi kawai yayi ya mik’e ya kwashi duwatsun da ta jefo mar ya fice ,bai ma san inda ta nufa ba shidai kawai yana ta kallon yadda mutane Kowa ke gudanar da alamuran shi cikin lumana wasu yara kyawawa sun kai biyar suka rugo da gudu suka rungume shi suna dariya ,sai d’aga su sama yake yi yana musu wasa wata tazo wucewa dauke da kwando cike mak’il da kayan marmari ya tsayar da ita ta kawo ma yaran ,sai tace ” Allah shi taimake ka Sarauniya JASEENA ke da buk’atar su ” murmushi yayi yace ” ki basu sai a kai mata wasu , tana ina ne itan?” Matar tace tana cikin lambu ” gami da mik’a masa kwandon ta wuce. Shi kuwa ya durk’usa gaban yaran ya ajiye musu kwandon yace ” bismillah! ” kowannen su ya d’eba shima suna ta Saka mishi a baki sai da yaga sai loda mar suke ya mik’e da sauri yace ” Yauwa maza ku cinye kafin na dawo ya wuce ya barsu suna ta fama ,ba ma mutane ba har dabbobi ma sun san akwai y’anci a Ramali:).
Lek’o ta yayi suna had’a ido ta ruga da gudu ya bi bayan ta sai fama take da doguwar riga hakan yasa ya cimmata ,ya d’aga dutsen data wurga masa kamar zai rama sai yaji daga waje wani mayak’i yace ” Allah ya baka nasara sarkin Kalahari Rizwan ne tafe da Sarauniya Meenah!!!! Jin hakan yasa ya sauk’e hannun shi yace ,a shirya tarbar su ,kuma a sanar da sarkin gida ” mayak’in yace toh ranka shi dad’e! ” sarki Haidar ya maida dubanshi ga Jaseena yace ,kin taki sa’a yau da sai na rama jifan da kika min!!” Ta rungume shi tana ta dariya tace ” kai dai kace kaji tsoro Kar na fille maka kai yanzun nan  ” ya bushe da wata irin dariya yace ” ni din ? Toh ko za’a gwada karfi ne?” Ai ko bamu gwada ba kasan na fika k’arfi ” ya sake bushewa da dariya yace ” karfin cin tuwo ba! Yanzu ma naga an taho da k’aton kwando cike mak’il da kayan marmari Wai naki ne  ” Tuni ta had’e rai tace ” toh ai kasan ba ni kadai bace shi yasa  ” ” Ohhhhh na gane !!! Kar kiyi ma d’ana sharri ,ke kad’ai kike cin kayanki ☺” ta bugi kirjin shi da hannun ta tace ” zan rama ai!!!” Ya kama hannunta suka fita suna tafe yana tsokanan ta………..
Haka dai rayuwar su ta kasance cikin farin ciki da kaunar juna ,ga gaskiya da rikon Amana ,sukan ziyarci junansu daga su har su Rizwan ,Aisha ta auri abokin Rizwan ne majeed aka kuma suka zauna a gidan Benaxir don yanzu kam bata nan dama ba gidan ta bane mallakin su Aisha ne ,majeed kuwa likita ne don babu wani magani da bai san amfanin shi da kuma yadda ake hadawa ba!! Saboda haka wannan babban gida ake kiranshi da gidan majeed likita!
Akwana a tashi yaran Jaseena biyu ,na farkon sunan mahaifin ta ne wato HAMEED na biyun kuma mace ce mai sunan JAUDA yara ne kyawawan gaske son Kowa !
Bangaren Meenah kuwa danta daya mai sunan mahaifin Haidar wato MAHMOUD! Aisha kuwa mace ta Haifa sunan ta Sameerah sunan kanwar majeed da ita ,gaba daya suna cikin farin ciki ,nutsuwa da kwanciyar hankali ,zalunci ya kau!!!!
🙏🏽ALHAMDULILLAH🙏🏽
Godiya ta tabbata ga ubangiji Allah mai Kowa mai komai wanda ya kawo ni har izuwa wannan ranar da na kammala wannan takardan nawa mai suna JASEENA !!
Dama ance in kaki sharar masallaci zakayi ta kasuwa ,kuma abunda kashuka shi zaka girbe , masu iya magana sunce RABON KWAD’O BAYA HAWA SAMA!!!
Duk abunda Allah ya kaddara zaka samu tabbas babu makawa sai ka same shi ,amma in kasa son zuciya toh lallai zai zamto sanadiyyar zubar ruwan idanuwa a gareka  Allah kasa mu dace AMEEN

JASEENA Where stories live. Discover now