Babi na 11

625 73 0
                                    

Haidar kuwa murmushi kawai yayi ya nufo inda take ,kanshi a k’asa yace ” nagode jarumar mata!!! ” Wannan sanyin Muryar tashi ta sa Jaseena lumshe idanuwa tana murmushi ba tare da ta tanka masa ba,shi ma yadda yayi maganar ba wanda zai gane magana yake yi ..
.  Gurin duk an watse Kowa ya koma gida, daga Aisha ,Jauda, Jaseena sai Meenah da Haidar, suna ta hirar su cikin nishad’i Meenah ce kad’ai kamar bata gurin. Jauda tace “Jaseena mu zamu tafi dare na yi sosai Kar Benaxir ta rufe k’ofa Kinsan ba mutunci gareta ba! Nan suka yi sallama suka bar ta da Haidar. Ganin sun share mintina babu wanda ya tanka wa wani yasa Jaseena ta mik’e tana kad’e rigar ta tace ” sai da safe yarima ,idon shi cikin nata yayi mata wani murmushi ba tare da ya tanka ba ,ganin shiru yasa ta juya zata tafi…….
Mahaifina sarki Mahmoud shine mai mulkin Wannan masarautar mutum ne wanda bai yadda ya ci ya sha ba tare da ya tabbatar jama’ar k’asar nan sun wadatu ba kullum burin shi yaga na gefen shi cikin walwala koda shi zai rasa ,hakan ne yasa ya fita daban da sauran yan uwan shi wanda kuma sun kasance ba uwa d’aya suke ba domin shi d’aya mahaifiyar shi ta Haifa kuma halin shi ma babu mai irin sa kasantuwar ,kakan mu mata biyu gareshi…..
Da sauri Jaseena ta juyo ta dawo inda yake ta nemi guri ta zauna don ta jiye wa kunnen ta ……. Yerima Haidar yaci gaba da cewa ” duk mahaifina ne babba a ciki domin mahaifiyar sa itace ta fari daga baya ne zaliha (ta biyun ) ta haifi maza biyu Hasheem ,Hayatud-deen ,da kuma mace d’aya Saleemah. Duk cikin su ukun Saleemah kad’ai ke son baba na don sun shaqu sosai hakan ne yasa tun tana y’ar shekara goma ,mahaifiyar ta Zaliha ta bada ita aure a wani masarauta Wai shi Kalahari aka daura mata aure da d’an sarkin garin yarima Jalalud-deen , wanda hakan yasa bata ‘kara zuwa ko da ziyara nan masarautar ba,Domin shine hud’ubar da mahaifiyar tata tayi mata.
Jin haka yasa Jaseena ta mik’e a razane ta ce ” Kalahari?? Jalalud-deen?!! ” shima Haidar ya mik’e yace “eh! Kin san su ne? Nan ta kwashe labarin rayuwar ta ta fada masa yayinda ya cika da mamaki ” haka Allah yake abin shi!! Shine abunda Haidar ya iya cewa kenan ,ya dubi Jaseena yace “Kin ga yanzu dare yayi ,ki je ki kwanta ki huta gobe in shaa Allah zan sanar da ke dukkan labari na. A nan suka rabu da alkawarin zai sanar da Jaseena komai game da shi washegari……………..

JASEENA Where stories live. Discover now