Babi na 5

705 77 0
                                    

Ta kai ak’alla minti talatin tana tafiya wani wajen ma sai ta sunkuya don ta wuce amma bata fasa ba har sai da takai wata Yar k’aramar k’ofa wanda aka toshe bakin da Yar ciyawa tasa hannu ta ture ciyawar dayake rana ta kusa faduwa Hasken wanda yay ja ya dalle mata ido sai kakkarewa take da hannun ta ,cikin dabara ta fito daga ramin dutsen ta tsaya ta jikin dutsen tana bawa idonta abinci domin banda dajin da yake gurin tana hango wani gini mai tsayin gaske ga kyau ,da gani kasan masarauta ce amma gaba yake da dajin shima ta hango shi ne don tana saman dutsen ne ta hango amma akwai wata siriryar hanya da ta bi gurin. Daji ne mai kyau don har yafi na inda suke kyau, da gudu ta juya tana dariya ta koma kogon bata yi wata wata ba sai gida Zainu na ganin ta yai tsalle ya koma kafad’ar ta yay zaman shi ita kuwa ganin yadda tayi datti yasa yasa ta nufi inda take wanka gefen Wannan ruwan tai ta wanke jikin ta tana wasa da ruwa ,k’iran da babanta yay mata ne yasa ta fita da sauri ta nufi inda taji Muryan shi ,fuska a turnuk’e yace “ina kika je?!!!” Nan ta fara kame kame ya juya ya barta gurin bai kuma cewa qala ba….
Cikin sand’a ta nufi d’akin ta, gami da turo k’ofar shi kuwa Hameed sai da ya gama kaifa takobin shi sannan ya wuce d’aki. Cikin dare ya kasa bacci domin jikinshi na bashi akwai abunda zai faru ,duk zuciyar shi sai bugawa take ya rasa dalilin faruwar hakan ,ya d’auki takobin shi ya nufi d’akin Jaseena wanda itama ba baccin take ba ,tana ganin shi ta tashi ta zauna tace ” baba na mai ya sameka? Yaya na ganka cikin daren nan? Murmushi yayi sannan ya kama hannun ta ya d’aura takobin ta daga kai tana dubanshi bai daina murmushi ba har Lokacin yace ” Jaseena !! Ko ma me zai faru yau d’in nan ka……….. Kafin ya k’arasa yaji motsi a waje tuni ya ce Jaseena ta fita ta bayan d’akin amma ta ture Wai itama zata iya fad’a ai kuma bazata tafi ta bar shi ba ,ya gaura mata mari wanda tsabar ta rikice sai da taga wuta ya ce ” nace ki tafi !!! Cikin kuka ta zari jakar ta na fata ta rataya zainu na biye da ita ta fice ta kofar bayan shi kuma ya fita don ya duba me ke wakana. Sauk’ar itace yaji a kansa wanda hakan yasa shi k’ara da zubewa a ‘kasa sumamme , duk abun nan da ya faru a idon Jaseena ne domin la6e wa tayi tana ganin duk abunda ke faruwa duk mutanen ta ga fuskokin su kasancewar Hasken farin wata duk ya mamaye gurin suka jashi suka tafi da shi ,nan ta zube tana wassu zafafan hawaye na takaici, a ranta tace ” toh ya akayi suka gano inda baba ya 6oye? ……,

Kafin kace wani abu har gari ya waye Jaseena na idar da sallah tana goge takobin da Hameed ya bata kawai taji takun mutane ,cikin sauri ta haye wata bishiya cikin duhuwa zainu ma ya bita , a hankali suke magana tana jin su ,”sarki yace a duba ko akwai Dan sa ko kuma d’iya domin da ciki a jikin matar sa ya baro Kalahari !! Jin haka yasa Jaseena ta diro ta yi hanyan Wannan kogon wanda ke bayan ruwa mai zuba ta shige Wannan ramin Wannan karon har da zainu a tare da ita tana dirowa ta d’auki Yar ciyawar ta maida shi gurbin da yake ta fara tafiya tana bin Wannan hanyar da ta gani sai kalle kalle take yi zainu kuwa an samu bishiyoyi ya hau wancan ya kama wancan. Har lokacin bata daina kuka ba ,don tsoro take yi Kar a kashe mahaifin ta.. Gurnani ta jiyo ta gefen hanyar kamar na zaki ai kuwa Kwatsam yayi tsalle ya tare gabanta  ta tsaya chak a gurin ta zubawa sarautar Allah ido , bata ankara ba taga wani kyakkyawan sadauki a gabanta ya tsugunna yana shafa kan zakin ,damtsen shi ma. Kad’ai abin kallo ne shi kanshi kamar zakin yake ga gashi har Ka fad’a wata Yar farmalam ce a jikin shi wanda gabanta a bud’e take ya rataya kwari da baka a bayanshi takalmin ‘kafar shi kuwa na fata ne , ya mik’e yana kallon Jaseena sannan ya k’arasa kusa da ita ,hawayen da ya gani a fuskar ta yasa ta bashi tausayi saidai ba tare da yace komai ba ya ciro k’ullin gurasa a jakar shi ya bata ,kamar yasan tana jin yunwa. Da sauri ta wafce ta nemi guri ta nad’e k’afa ta fara ci ,chan sai ta tuna da mahaifin ta, hawaye na zubo mata sai chusa gurasar take yi tsabar ta zuciya ,har ya shak’e ta ta fara tari kamar dama jira yake , matashin ya ciro wata Yar gora na fata ya mik’a mata ta kar6a sai bayan ta d’an nutsu sannan ta dubeshi tace ” nagode !! murmushi kawai yayi ya yi mata nuni da hannu ma’ana ta tashi su tafi , nan ne ta gane cewa baya magana kuma ba kurma bane yana ji sarai amma baya iya magana ,saidai akwai kyau kamar balarabe , ta tashi ta bi bayanshi suka ci gaba da tafiya har suka k’ure Wannan dajin ,abin da ya bata mamaki shine wani tafkeken kogi ne a gurin saidai daga bakin ruwan ma kafi ganin masarautar ,jirgin ruwa suka shiga mai tuk’in yan ta fama da tuk’in shi kuwa sai wasa da ruwan yake yi…..,…….

JASEENA Where stories live. Discover now