Babi na 13

592 80 0
                                    

Jaseena ta juyo idanuwan ta duk sun yi ja ,tace “Na baka !! Na baka ya Haidar!! Ka kula da ita domin taka ta riga ta iso inda zata tsaya da farautar kuma bani da tabbacin zata koma gareka !!” Haidar ya mik’e yace ” nagode kyakkyawa !! Jaseena tayi murmushi tace ” akwai maganar da nake son sanar da kai ne ” Haidar yace” ki fad’a mana ko ma menene. Ta kwashe duk abubuwan da ya faru a daren jiya ta sanar da shi har abunda yasa ta shiga d’akin Rizwan. Haidar ya sake bata hakuri ,sannan ta gyara zama ta ce ” baka k’arasa min labarin ka ba” ya d’an yi murmushi sannan ya ci gaba……..

A lokacin ina da shekaru goma sha shida ne ,k’ anin babana wato Hasheem ya bi rud’in uwarsa na cewa Kar ya kuskura ya bar babana da rai don in har ya tsufa a kan karagar mulki nine zan gaje shi na zama sarki , don shi a cewar shi ni ba komai bane in ya kawar da mahaifina, da duk wani mai ji dani, kasantuwar kullum da safe muna fita daji ni da kakana yana nuna min nau’in ganyayyaki da amfanin su ,hakan yasa ya shirya mana gadar zare.
Mun yi Nisan kiwo nida kaka har bayan la’asar sannan muka iso gida ,muna shiga wasu mutane a kan dawakai su kuma suna fita ,ga gari duk ya turnuk’e da hayak’i ko da muka k’arasa cikin fada nan muka tarar da gawawwakin iyayena da kuma na k’annen k’ anin Hasheem Hayatud-deen , Hasheem ya kwanta a kansu sai kukan munafurci yake yi kamar da gaske ,a nan ne zuciyar kakana ya buga take rai yayi halinsa , bayan kwana uku da faruwar hakan ,kawu Hasheem ya na’da kanshi a matsayin sarkin Ramali ,duk dattijawan da basuyi Na’am da hukuncin da ya yanke ba sai ya sa aka kwashe su aka kai su masarautar Kalahari aka rufe ana basu horo mai tsanani ,daga cikin wadannan dattijawan sun had’a da mahaifan Aisha da kuma Jauda ,kamar yadda na fad’a miki Meenah itace d’iyar kawu Hasheem amma tun tana y’ar shekaru tara ne abun ya faru don duk sa’anni suke da Aisha da Jauda kinga kuma k’awaye ne hakan yasa ta baro fada ta zab’i zaman bauta a gidan Benaxir har ta girma ta kawo lokacin nan da kike gani….
Ni kuwa tun lokacin da abun ya faru na daina magana da Kowa da na gano hakan kawu Hasheem ya ke so sai na nuna mishi ma kwata kwata bana magana na daina yi ko da da wasa ,a haka shi da mabiya bayansa suka zata na riga na zama miskini. Kin ji yadda rayuwa ta ta kasance kullum cikin k’ask’anci amma ko a jikina domin na san dole ne wata rana sai gaskiya tayi halinta!!” Amma tunda haka abun yake toh mu zamu fara wargaza mishi rayuwar sa” Jaseena ta goge d’an hawayen fuskar ta sannan tace ” lallai ka shiga k’uncin rayuwa Haidar !! A nan ne Jaseena ta kwashe labarin ta ta bashi ta kuma sanar da shi ko wanene sarki Jalalud-deen. Sun dad’e suna shan hirar su ,kafin nan suka nufi gidan Benaxir don yin magana da su Jauda………

JASEENA Where stories live. Discover now