Babi na 17

557 58 0
                                    

Kasantuwar ba hanyar da su Jalalud-deen suke bi don shiga k’asar Ramali zasu bi ba ko dawakai basu d’auka ba cikin sauki suka bi ta inda Jaseena ta fito suka shiga wannan ramin ruwan har ta kaisu ga asalin cikin kogon ,bayan sun gama dirko wa daga wannan dutsen ne suka tsaya karkade jiki su Jauda se kalle kalle ake yi basu ankara ba suka ga sojojin yak’i sun zagaye su kowanne hannu rik’e da mashi ,gashi kuma abun da ya basu mamaki duk babu saurayi cikin su don duk sun manyanta da gani kasan sun yi zamani, Jauda ce ta fara jefar da jakar da ta rik’e tana motsar k’walla ” baba!!! Abunda ta iya furta wa kenan ta nufi gurin d’aya daga cikin wad’anda suka zagaye su ta rungume tana kuka Aisha ma ta nufi gurin wani da ke tsaye yana kallonta sai hawaye ,Jaseena da ke kallon su tuni itama ta fara k’wallar saboda ta tuna nata mahaifin da bata ma san wanne hali yake ciki ba , Muryar sarki Haidar ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, tana juyawa taga gurin babu Kowa daga shi sai ita ta fara juye juye fuskar ta cike da alamar tambaya?? Kafin ta furta komai Haidar yace ” ya ke ma’abociyar kyau da farin hali, kada ki damu Mun basu dama ne su gana da iyayen su domin kuwa sun yi kewar juna ” Murmushi Jaseena tayi sannan ta fara share hawayen da ke gangaro wa daga idanuwan ta ,Haidar ya matso kusa da ita yace ” ya isa haka Kar ki sake yi min asarar hawaye ! Kuma baba yana cikin k’oshin lafiya” Jaseena ta d’ago manyan idanuwan ta tace ” don Allah muje in ga baba na ,don hankali na bazai kwanta ba in ban sa shi a ido ba tana fad’in hakan hannunta guda kuma ta chafke wuyar rigar shi ,inda ta shak’e ya kalla sannan yayi Yar murmushi cikin murya irin na zolaya yace ” irin wannan chafka haka ,duk kin yamutsa min riga! Lallai kina so na sa a kulle min ke a kurkuku yanzungaske. ” Hakan yayi matuk’ar bata dariya yadda ya ta6e fuska kamar da gaske. Ya ce Haba!! Ko ke fa ? Amma matar sarki guda gashi kuma jarumar mata amma tana hawaye kamar raguwa?” Dariya ta bushe da shi tace ” Aa ba wani nan ! Cewa zakayi jarumar mata da maza  ai mazan ma saidai in basu nemi in sambad’e su ba ”. Dariya sosai ta bawa Sarki Haidar har ya shagala ya nemi gurin zama yana kallonta, ita ko sai fama take da y’ay’an innibi,yana kallon yadda karamin bakinta ke motsawa cikin nutsuwa ta lumshe idanuwa sai faman tauna take, yayi murmushi ya mik’e ya d’auki wani dan karamin dutse ya wulla mata ya samu damtsen ta ,tuni hankalin ta ya dawo daga duniyar da ta lula tace ” ya dai?* ya had’e rai yace ” kin barni babu hira sai faman tauna kike yi !! Ni na fa gaji ma kuzo mu tafi inda zamu je kafin dare yayi mana” chan sai suka lura ko ina yayi shiru cikin kogon
Cikin sand’a yake tafiya tana biye da shi ,haka suka gama dube duben su basuga Kowa ba a cikin kogon ,Jaseena tace ” toh ina suka tafi ne?” Haidar ya yi shiru na yan mintina sai yace” duk yadda akayi sun nufi Kalahari ne zo mu tafi!! ” ko da suka fito bakin kogon suka tsaya suna tunanin yadda za’a yi su tafi Kalahari babu doki kuma gashi da nisa suna so su tadda su Jauda. Har ta hak’ura ta jingina da jikin kogon kawai suka jiyo sautin doki ,tana juyowa ta hango zainu shi kad’ai ya dumfaro su ta juya ta dubi Haidar tace baba ne ya turo shi , na tabbata sun isa Kalahari!!

JASEENA Where stories live. Discover now