💞komai daren dadewa💞

113 14 0
                                    

Shi dai khalifa zai kai kimanin shekara 11_12su kuma humaira da Abdulgaffar zasu kai shekara 7_8 dayake sa'annine sai Khadija da 5_6 years sai kuma safiya da bazata wuce 13_14 yrs  ba. Anty na ganinsu su Anty baby da safiya kamar wacce aka tsungula ta tashi ta karaso da su har zuwa inda  suke zaune a dinning table d'in ta zaunar da su tana fad'in a'a maraba da yarana 'yan albarka itadai safiya ba abunda zuciyarta keyi sai bugawa da kuma mamakin hali irin na Anty . Ganin mahaifinsu a wurin yasasu zubewa 'kasa gabad'aya suka Shiga kwasar gaisuwar Abba da Anty. Abba ya amsa musu cikin sanyin murya kamar haka "lafiya kalau yan albarka".Abba ne yashiga tambayar safiya yanacewa " ke  sufin Abba (da yake haka yake cemata) INA kika je  ban gankiba tun  da safe safiya tace Abba school fa naje  ko kamanta yau friday .eh ai duk dahaka ai yau sha biyu kuke tashi tun dakuka dawo ban ganki a falo ba sai yan uwanki da keta aikin kallo. Tace Abba kaina ne ke d'an ciwo ta karashe maganar cikeda shagwaba. Abba yace subahanllahi INA fatar kin sha magani ko? Tace eh nasha yace to Allah ya kara sauki duka suka amsa da ameen banda Anty wadda ba abunda zuciyarta keyi sai kuna jitakeyi kamar ta kashe yarannan ta huta domin yanda ya damu da su ko yayanta bai damu dasu hakaba. Abba yace toh kukira sauran yan uwanku kuzo muci abinciko. Duk suka amsa da toh. Anty baby CE taje ta kira sauran yam uwanta dake falo suna kallo. Itakuma safiya ta tafi ta kira Maryam (wacce take bimawa) tanashiga dakin ta tararda Maryam a kan gadota na sharar bacci. Da sallama tashiga dakin ahankali ta shiga  tashinta tana cewa anty maryam ki tashi Abba na kiranki wai kizo muci abinci jin an ambaci  Abba yasata mikewa da sauri ta fada toilet ta wanko bakinta tana fitowa ta nufi hanyar dinning. Tana zuwa itama ta kwashi gaisuwa ta ja kujera ta zauna. Shuru ana cin abinci sai abdulsalam yacewa safiya cikin hausarnan tasada bata gama nunaba yace "Anty safiya naga idanunki sun kumbura tayi kwafa tace me kagani nifa kai nane  ke ciwo
Abba ya d'an yi gyaran murya yace abdulsalam ba na hanaka magana idan ana cin abinci ba ko kana san Allah yayi fushi dakai. Dajin haka yayi Sauri yace a'a Abba na dena wlhy. Abba ya d'an yi murmushin nan nasu na many a yace toh shikenan naji
Duk wannan abun da akeyi Anty na jin su saidai bata iya cewa komai ba sai ma mugun kallon da take binsu safiya dashi batareda mahaifinsu yasaniba. Anty baby na dago kai idanunta suka hade da na Anty wani mugun harara data dalla mata sai da hanjin cikinta suka kada tsabar tsoron abunda zatayi musu idan mahaifinsu baya nan. Ana gama cin abinci kowa yakama gabansa yai dakinsa sukuma su khalifa da Abdulgaffar da abdulsalam dakinsu daya sai humaira da Khadija dakinsu daya. Anty baby kuwa da Anty Maryam da safiya kowa da NASA dakin. Sai dakowa ya shige dakinsa kafin Anty baby ta fito ta kakkashe wutan gidan ta rife kofa ta tofesu da addua sannan itama ta je ta kwanta cikeda tunanin mahaifiyarsu da kuma irin abunda Anty zata musu gobe.

🌃🌃kiran farko akunnen Anty baby dayake yau asabar zasu tafi islamiya daga tashinta  ta shiga  tashin kowa . Anty da Abba ne kawai bata tadaba Dan sunriga sun tashi sannan itama ta gabatar da nata sallahn. Tana idarwa ta fada kitchen ta Shiga hada musu breakfast.chips ne da soyayyan kwai sai ketchup da kuma tea mai kauri tana gamawa tashiga wanka. Koda tafito ta tarar da kowa zazzaune a dinning table tana isa  ta gaishe da Abba da Anty. Abba ya amsa mata dauke da murmushi a fuskarsa Anty kuma ta amsa mata murya can ciki ta kare  mata kallon 'kaskanci batareda ta bari mahaifinsu ya gane halin da suke ciki ba. Abba ne yace da khalifa yace maryam ta fito suci abinci . khalifa ya amsa da toh yana isa  bakin kofar yaganta akulle cikin sa'a kuwa yana murdawa yaji ta bude. Da sallama ya shiga  dakin yashiga bubbuga kafarta a hankali amma taki tashi haka yai ta dukanta amma taki tashi haka yafita yaje yasami Abba ya CE mishi taki tashi ran Abba ya soma baci yace da safiya taje ta tasheta. Tana shiga  ta ganta a kwance a kan gado tayi rub da ciki kamar mai bacci ta na zuwa ta zauna kusa da ita  tace  Anty Maryam kitashi Abba fa ke kiranki. Haka tai ta magana amma ko motsi batayi ba. Aguje ta is a inda  su Abba suke zaune tasanar dashi halin da akeciki. Cikin tashin hankali ya nufi dakin da take ciki ya nazuwa ya nufi inda  take ya shiga  jijjigata amma  taki tashi . Hankalinshi ba karamin tashi ya yiba duk ya rikice ya dauketa ya nufi mota Anty na ganin Abba ya fito da Maryam rike a hannunsa ta saka wani ihu kamar da gaske tanakuka ta na fadin ta Shiga uku nan kuwa cikin ranta kukan dadi takeyi kamar an zuba mata ruwan sanyi a zuciyarta take ji. Sai da ya isa bakin mota kafin yatuna baima dauko mukullin motar ba yace ma anty baby taje ta dauko cikin yan mintina kalilan ta dawo da mukullin mota ahannunta ta mikwa Abba ya sata  a back seat akan cinyar Anty baby Anty na zaune a gaba sai abba da ke tuki
Agigice suka is a asibitin suna shiga likitoci suka karbe ta sukayi emergency da ita . sai bayan Minti talatin sannan likitocin suka fito sukace suna bukatar ganin Abba jiki a samyaye ya tashi ya bi bayan likitan har cikin office dinshi. Likitan ya danyi gyaran murya yace ar u hr father? Yace yes I'm hr father likitan yace ur child is in serious problem saboda tana dab da kamuwa da hawanjini Abba ya mike tsaye yace what hawan jini kuma. Likitan yace yes of course jawan jini  kuma sai kunyi takatsantsan da lafiyarta in bahaka ba duk abunda ya farubKu kuka janyo. Haka dai likitan yai ta bashi shawarwari tareda kara jaddada mishi da ya tuntubeta yaji meke damunta sannan yai mishi godiya ya  fice daga office din

Yana fitowa yaga su anti da Anty baby sunata rusar kuka suna ganinshi suka taso da sauri suna tambayarshi meya ya sameta  Abba dai bai ce musu komaiba yashiga ward din da Maryam take. Kwance ya ganta hankalinta kwance tanata bacci. Kujera yaja ya zauna Yakama hannunta ya shiga murzawa a hankali hawaye yashiga zubo mishi.. Ahankali ta Shiga bude idonta tana kokarin tashi zaune Abba yayi maza yamaidata ya mata alama data kwanta, ba musu ta koma ta kwanta cikin karfin hali Abba yace Maryam me ke damunki har kike kokarin jawowa kanki hawan jini eye Maryam. Maryam tayi shiru batace komai ba saima sadda kanta kasa dataayi Abba yace maryam magana make miki fa tace Abba ba  komai fa kawai........bata karashe  maganar ba ya katseta da cewa Maryam nifa mahaifinki ne idan baki  gayamun damuwar ki ba toh wa za ki gayawaa a halin yanzu eh Maryam kina kokrin ki jefa kanki cikin wani hali da wane ido  kike son in kalli ubangiji ranar gobe kiyama eh Maryam ki dubi  girman Allah ki gayamun damuwarki

💞komai daren dadewa💞Where stories live. Discover now