💞komai daren dadewa💞

90 12 0
                                    


💖na Anty pink💖

ASALIN LABARI

Alhaji Abubakar Mas'ud haifaffen Dan garin jahar Adamawa ne . yayi makarantarsa ne a farfaru da ke jahar sakkwato bayan ya gamane yasamu aiki bayan ya fara aikine iyayensa suka matsamishi da ya fidda matar aure shi kuma alokacin an tura shi aiki jahar kaduna anan ne ya hadu da wata budurwa mai Suna Fatima. Alokacin ita kuma Fatima tana ss2 dama tadawo gida hutune saboda a boarding skull take. Haka yai ta dawainiyarta harta gama ss3 ya dauke wa mahaifinta duk wata dawainiya tata hatta visiting dinta shi yake zuwa bayan ta gamane da wata biyar akayi bikinsu. Iyayensa bakaramin dadi sukaji ba ganin ya samu yarinya natsatstsiya, kamila, mai hankali, mai rikon addini da kuma sanin ya kamata. Bayan shekara biyar da auransune ta haifi santaleliyar yarta mai suna Zainab wacce ake kira da baby sosai ta biyo ta saidai bata dauko hasken ta ba kasancewar mahaifinta ba mai haske bane. Bayan shekara biyu ta sake haifo wata yar mai suna Maryam bayan kuma wasu shekaru biyu ta kuma haifo wata yar mai suna safiya daga nn kuma bata sake haihuwa ba sai bayan shekara uku wnn karan km na miji ne. Ya ci sunan mahaifinshi ne wato Abubakar sadiq amma khalifa ake cemasa. Bayan ta haifi khalifa ne aka tabbatar mata da cewa bazata sake haihuwa ba domin ta samu matsala wajen haihuwarsa. Sosai suka shagwaba khalifa kasancewar shi kadai ne namiji a gidan. Da yake Allah karimun rahimun ne bayan wasu shekarun biyar ne ta sake haihuwa wannan karan ma na mijine suka samishi suna Abdulgaffar. Alokacin shi kuma alhj Abubakar mas'ud ya sake aure ya auri wata mata mai suna haj hassana bayan wata Biyar da haihuwar abdulgaffar ne itama ta haifo tata yar mai suna Aishatul humaira amma humaira ake cemata. Zaman su ya soma kyau sai dai ita haj hasaana tana da wani Abu a kunshe a ranta gameda haj fatima da yaranta domin yanda taga alhj Abubakar na nuna musu so. Babu yanda bata yiba akan ta ga ta rabashi da su amma allah bai bata nasara ba.wata rana haj hassana (Anty) ta yanke shawarar takira kawarta haj kaka ta gayamata halin da take ciki domin tana da yakinin cewa ita kadai CE zata iya Samar mata mafita. Haj kaka ta shaida wa Anty da ta same ta a gidan ta yanzu yanxu tasan mata kin da xa ta dauka. Bayan ta is a gidan ne haj kaka ke shaidamata da cewa gidan boka zasu da farko Anty ba ta yarda ba it a ko haj kaka a harzuke ta shiga zazzaga ma Anty kwandon masifa tana fadin ai dama duk abunda takeyi domin ita takeyinshi amma tunda da haka zata sakamata ba matsala ai gobe ma rana CE.

Da jin haka Anty ta rude ta Shiga bata hakuri tana fadin ai itama tasan duk abundata keyi tasan Dan jin dadin ta takeyinshi Dan haka ta kwantar da hankalinta baxata taba watsa mata kasa a idon taba. Suna isa wajen bokan mai suna ilu zamau yace yasan abunda ke tafe dasu amma Abu mawuyaci ne akashe haj Fatima da yaranta Lokaci daya sai dai su xabi daya ko ita ko su. Atake suka yanke shawarar akashe haj Fatima inyaso daga baya tasan yanda xatayi da yaran ita dai damuwarta 'HAJ FATIMA'. Boka ilu zamau ne y katse musu xance da cwa baxai fara aiki ba sai Yaga jaka a bude a hka ska zube mishi makudan kudi. Yabasu wani Abu a kulle a Leda yakuma shaida musu da cewa ta tabbatar ta sama ta shi a abinci amma fa maganin sai ya dau kusan shekara daya. Da haka sukai mishi Godia suka fice . Anty na isa gida ta tarar da kowa a falo banda abbba Wanda dama ba dawowa aiki ykeyi ba sai byn sllhn isha. Bata reda kawo komai cikin ransu ba suka tashi suka rungumeta sukai mta sannu d zuwa sukuwa su safiya saidai gaisuwa suka bita da shi ba yabo ba fallasa ta amsasu ta kuma gaida haj Fatima kafin ta wuce dakinta tareda mugun Abu kulle a ranta. Wata rana da safe kowa ya hallara a dining table kmr yanda aka saba Anty kawai suke  jira ganin shirun yayi yawa ne  yasa haj Fatima cewa bari taje  ta duba taga ko lafia. Daga  Isar ta dakin ta tsinkayi Anty tana ta mutsul mutsul ta na kiran wayyo Allah kaina zai fashe da jin haka haj Fatima tayo kanta da sauri ta shiga  ciccibarta ta na kiran meya faru karki damu yanxu zamu je  asibiti karki damu kinji. Suna fitowa falo suka yi tozali da alhj Abubakar a rude yayo Kansu ya shiga  tambayar su meya ke faruwa. Cikin rudu haj Fatima tashiga bashi amsa  tace  abban baby nima bansani ba kawai dai ta CE kanta zai balle  inaga kanta ke ciwo Dan Allah ka hanzarta mu kaita asibiti.

💞komai daren dadewa💞Where stories live. Discover now