💞komai daren dadewa💞

82 5 0
                                    


💖 na Anty pink💖

Kullum su Anty baby sai su zauna kmr kurmaye ba um ba um um ko abinci sai anyi da kyar suke ci su kuwa su Abdulgaffar kullum cikin rusa kuka suke wai sudai akawo musu ummar su inbahaka ba subita. Haka suka zauna har a akayi saadakan bakwai babu yanda yan uwan Umma basuyiba akan Abba ya bari kanwar Umma goggo Rayyana ta xauna dasu Anty baby har na dan wani lokaci amma Abba fafur yaki amincewa wai ai ga Anty ma xata iya kula dasu haka suka hakura suka koma garinsu. Sai bayan sati biyu da rasuwar Umma kafin akayi sunan Khadija su Anty baby yanxu kam sai ma wani canji da suka fara gani daga anty . masu aikin gidan duk ta korasu idan Abba yai magana sai tace ai aiki take koya musu idan suka je gidan miji ai ba wani ne zai musu aikinba. Haka yake hakura ya kyaleta dan shi gani yake duk abunda takeyi baxata taba cutar dasu ba hasalima shi duk abunda tace agidan toh ya xauna . sai dai abudaya ne bata yi bata taba kuntata ma khalifa da abdulgaffar ba domin tasan xasu iya gayama Abba kuma idan Abba ya sani toh zamanta a gidan yakare. Haka har akayi shekara uku ta sake haihuwa wannan karan kam da namiji ta Haifa aka sama yaron suna abdulsalam. farinciki gun Anty ba a magana domin abun so yasamu. Haka suka cigaba da rayuwa cikin kunci har kawo yanxu.

         *CIGABAN LABARI*

Sai da sukai kwana daya a asibitin kafin aka sallamesu suna dawowa Anty baby ta hau share share ta dafa abinci domin safiya akwai son jiki ko ta iya ma ba dafawa zatayi ba. Da daddare bayan sallahn isha angama cin abinci kowa yayi shigewarsa Anty baby ta sami Anty Maryam a daki tashiga mata nasiha tana cemata ta dena sa damuwa a ranta hakan zai iya jawo mata matsala. Anty Maryam tace amma Anty baby akwai cutarwa yanxu da ummarmu na nan ai da duk haka bata faru ba. Anty baby tace toh ya muka iya Maryam dole muyi hakuri duniya ta ishe kowa Riga da zani. Anty Maryam tace toh amma ni anty baby abunda ban gane ba shine ranar da Umma zata rasu kintuna abunda ta fada? Anty baby ta girgixa kanta cikeda son jin Karin bayani. Anty Maryam tace "caa fa tayi *KOMAI DAREN DADEWA* gsky zata bayyana. Toh gskyr mey Umma ke nufi cewar  Anty baby. Basu yi aune ba sukaji an wanke Maryam da wasu lafiyayyun mari har guda biyu ta kowane kunci sai data fadi kasa dafe da kuncin ta. Anty baby ta mike tsaye cikin tsoro tashiga ba Anty hakuri. Anty Dan Allah kiyi hakuri ni  nai  miki laifi basu ba dan haka ni zaki hukunta. Anty ta matso dap da Anty baby ta tallabo habarta ta matse tace 'na baku last warning daga ke har kannenki wlhy wlhy bazan yi rantsuwar kaffara ba toh ko na lahira sai ya fiku jin dadi ke ko subutan baki kukayi kuka fada ko toh abunda zan muku sai ya wuce tunaninku kinji ni ko bakijini ba Anty baby ta girgixa kanta cikin fargaba Anty ta sake matse habarta ta tace kinjini ko kuwa Anty baby tace eh naji. Anty tace if she doesn't understand make her understand cox I won't hesitate to deal wit anibodi dat  messes wit me got dat anty baby ta girgixa kanta da Sauri Anty tace da yafi da yafiyemuku gabadayanku Anty ta buga tsaki tai ficewarta tana fadin aikin banxa. Tana fita Anty baby ta tashi takaraso inda Maryam ke kwance har yanxu ta tallabo ta ta shiga lallashinta har ta samuta sassauta kukan da takeyi tai mata sai da safe ta fice xuwa nata dakin. Tunda asuba Anty baby ta tashi ta tashe kowa sallah kamar yanda tasaba tanagamawa ta fara share share tana cikin sharannan ne  Anty Maryam taxo. Anty baby kawo tsantsiyar in tayaki ta fada tareda rike bakin tsintsiyar. Anty baby tai saurin rike tsintsiyar tareda annuri a fuskarta tace" a'a Maryam barshi kawai  xanyi keda ma bakida lafia. Anty Maryam tai murmushi tace toh ai Anty baby na warke bagashi ma har zani makaranta ba. Anty baby tace toh yanzu da wannan kafewar da kikeyi ba gwara ki je ki shirya ba. Anty Maryam ta karyar da kai tace toh Anty baby if u insist. Tana gama fadin haka tai ficewarta. Bayan ta gama hada ma yan makaranta breakfast ne kowa ya hallara a dinning banda Abba da anty wanda dama  can ba tashi sukeyi Idan xasu makaranta .Anty Maryam ce tashiga tambayar anty baby tacemata anty baby yau bazaki school bane. Anty baby ta ce zanje amma sai karfe goma. Anty maryam ta sauke ajiyar xuciya tace anty baby wlhy mun kusa fara waec din mu kuma ni wlhy maths dinnan ba wani gane mishi nake sosai ba. Anty baby tace toh meyasa bakizo nakoyamiki ba. Bata kaiga bata amsa ba taji muryar khalifa yana cewa anty maryam wai inji baba direba yace kixo mutafi mun yi latti. Anty maryam tace toh yi sauri ka dauko mun jakata. Ya amsa da toh yana gunguni ya fice. Koda anty baby ta fito xata tafi makaranta anty kawai ta tarar a palo da dukkan alamu Abba yatafi office. Har kasa ta duka ta gaisheta. Wani wulakantaccen kallo anty ta aikamata tace ina zaki anty baby tace makaranta zani ina da lectures. Anty ta harareta kamar idanunta zasu zazzago ta ce makira karya kikeyi makaranta zaki ko gun shashancinki da kika saba zuwa. Da sauri anty baby ta dago kai idanunta sun cika da hawaye kiris kawai ya yarage ta fashe da kuka tace subahanallah anty gun shashanci fa kika ce. Anty ta dungure ta tace toh karya akamiki ko kuwa waye shedan din daxa ki wani ce subahanallah. Anty baby tai kasa da murya tace anty ni ba nufi ba ba kenan amma kiyi hakuri. Anty taja wani kafirin tsaki irin na tsofaffin mugayennan waenda suka kware a iya makirci tace ni dallah tashi ki ban wuri yara zabga zabga daku amma ace bakusan abunda ya kamace kuba. Har anty baby ta kai bakin kofa anty tace keey.
   
     Anty baby ta tsaya cak ba tareda ta juyo ba anty tace wai tukun ma ke da kikacewa xaki tafi school kin gama aikinki ne? Anty baby tace eh nagama bata jira amsartaba tai gaba abunta tafada cikin motar tareda goge dan guntun  hawayen da ya gangaro mata kada direban yagane halin da takeci. Da suka isa makarantar direban ya tambayeta karfe nawa zaizo daukarta tace mishi karfe uku yaja motar yai gaba abunshi.

#vote
# share
#comment

💞komai daren dadewa💞जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें