💞komai daren dadewa💞

75 9 0
                                    


💖na Anty pink💖

Bayan kamar minti ashirin likitan ya fito. Da fitowar shi Abba ya shiga tambayar shi mey ke damunta. Likitan yae murmushi yace ai there's notin  t wrry about insha Allah matar ka tanada juna biyu wata daya bakaramin dadi suka ji ba barin  ma Anty da ba abunda take fata  yanxu kamar itama tasamu NATA da.namijin.
A kwana a tashi ba wiya a wurin Allah shekara ya zama kamar wata, wata ya zama kamar sati, sati ya zama kamar kwana, kwana ya zama kamar awa yau cikin Anty ya shiga  watan haihuwa ita kuwa haj Fatima ciwo sai cinta yakeyi yau lafiya gobe babu sai mafarkai take masu ban tsoro ankira likita ya duba ta amma yace bai ga komai a tattareda ita ba ciwo sai gaba yakeyi. Wata rana da safe Anty ta tashi da ciwon Mara mai tsanani Wanda har yasata ta kasa fitowa Karin safe. Haj Fatima CE ta ce ma Anty baby taje  ta dubo Anty ko lafia ta amsa da toh ta fice. Cikin tashin hankali ta sami su Abba a dinning table tace  umma wlhy Anty bata da lfy sosai ki xo Kigani da hanxari tabi bayan Anty baby. Da sauri ta tallabi Anty suka fito falo duk da itama bata da wani kuxari Abba har ya rigada ya dauko mukullin mota suka wai  yake  jira.cikin Mintuna kalilan suka isa asibitin akai dakin haihuwa da ita. Da fitowar likitocin suka shaida ma abba cewa an samu karuwa ya mace. Farinciki kam ba'a magana. Abba ne  yace da Umma  bari yaje yaji sai yaushe za'a sallame ta. Tace  mishi toh itama tace bari taje  taga masu haihuwa.yana isa office din likitan yashiga knocking da come in ya amsa mai kasancewar likitan ba musulmi bane. Hannu likitan ya mika mai alamar gaisuwa bai yi tantama ba ya mikamai suka gaisa yaja kujera ya zauna. Abba ne ya shiga tambayar likitan cikin harshen turanci kamar haka 'doctor I came t ask u when is she going t b  discharged likitan yayi sauri yace no no ai that's not a problem ai ko nan xuwa yamma zaku iya tafiya. Abba yai mishi godiya ya fice. Yana isa dakin da aka kai Anty domin hutawa ya yatararda haj Fatima rike da jaririyar a hannunta Anty na daga gefe kan gado tana bacci. Tana ganin Abba ta shiga  tambayar shi tana cewa mey  likitan yace ma, akwai matsalane, yaushe za'a sallameta. Abba yaja kujera ya xauna yace mikomun jaririyar ingani kafin in ansamiki tambayoyinki. Umma ta mishi murmushin nn nata  mai kyau tace  toh gata ta mikama Abba jaririyar tace toh baka amsamin tambayoyina ba. Abba yace likitan yace nan da yamma xamu iya tafiya gida sannan babu wata matsala in Allah ya yarda. Abba ne yashiga yi ma jaririyar huduba a kunne tareda rad'a mata suna 'KHADIJA'. Juyowar da Abba zai yi sai dai me zai gani? Umma yagani kwance a kasa sumammiya. Cikin rudu ya ajiye jaririyar kusa da Anty cikin keken da ake  ajiye yara yayo kanta ya shiga  tambayarta meya sameta. Dai dai lokacin Anty ta bude idanunta taga haj Fatima kwance a kasa wani malalacin murmushi tasaki tace  cikin ranta ai ko ba komai haj Fatima takusa xuwa karshe. Likita ne yashigo dakin ya shiga  tambayar su meya ke faruwa domin ya Dan ji hayaniya daga waje. Likitan bai kuma tambayar Abba meya ke faruwa ba suka dauketa sukayi ICU(intensive care unit) da ita. Alokacin sukuma su Anty bab suka iso so koda suka xo basu Tarar da umma a wajenba. Suna isa dakin da aka aje Anty suka shiga  tambayar ina umma. Anty tai caraf tace  ai ummar ku bata da lafia daxu naga ta suma  a nan bansan ko mey ke damuntaba. Anty baby ta kwalalo ido tace bata da lafia kuma Anty. Maryam tace  toh Anty bakisan dakin da takeba Anty ta tabe baki tace nima bansani ba sai abbbanku yaxo Ku tambayeshi. Safiya kuwa tuni hawaye suka fara mata xarya a idananu sukuwa su khalifa basu Masan halin da ake cikiba domin suna can suna wasa da jaririya Khadija. dai dai lokacin suka ji anbude kofar kowa ya maida hankalinshi kan kofar suna jira suga waxai shigo sai da aka kusan dau  minti daya kafin Abba ya sa kai ya shiga  safiya na ganin Abba t Mike da sauri ta isa inda yake  ta kama hannun shi ta shiga  tambayar shi INA umma. Abba ya ce safiya ummarku......sai kuma ya kasa Karasawa safiya ta shiga girgixa kanta ta CE Abba kayi magana mana meya sameta. Abba yai karfin hali yace safiya ummarku bata da lafiya kuma an kasa gane  mey ke damunta

#vote
#share
#comment
     Kubiyoni domin jin Karin bayani.
        
      09050233294
Ayi karatu lafiya
Nagode

💞komai daren dadewa💞Where stories live. Discover now