💞komai daren dadewa💞

42 9 0
                                    


💖Na Anty pink💖

Acan gida kuwa Anty baby nafita Anty ta d'aga waya ta kira aminiyarta haj kaka tana cemata ita wlhy yarannan sun isheta ta rasa yanda zatayi dasu. Haj kaka tace "kwantar da hankalinki tawan ita baby aji nawa take a secondary? Anty tace secondary kuma? Yarinyar da ke level 200 a university. Yauwa kinga faduwa taxo daidai da zama kinga sai a ahadata da d'an kishiyata. Wa kenan cewar Anty. Haj kaka tace Aliyu haidar amma mamarshi batanan ta fita tunda dadewa kema kinsan bana wasa kuma duk abunda nace yayi yanxu xaki ga yayishi Dan ya dauke in tamkar uwa a gareshi. Anty tace toh a ina yake aiki? Haj kaka tace ai banker ne a CBN yake aiki amma fa a abuja yake zaune. Ai haj kaka aikinki na kyau bari abbansu ya dawo in mishi magana nasan bazai ki ta tawaba Cewar Anty. Toh shikenan tawan duk yanda ake ciki ki sanar dani nima zanyi ma mahaifinshi magana indai ya amince toh banida Matsala. Daga haka sukai sallama.

Sai karfe biyu da rabi su Maryam suka dawo daga schl. Ranar sunci sa'a Anty ta dafa abincin rana da saidai insun dawo su dafa da Kansu. Haka zalika sun ga sauyi daga gareta Dan yau daga gani tana cikin farinciki. Ita kuwa cikin ranta tasan mugun tarkon da ta kulla ma Anty baby, Abba kawai take jira ya dawo indai ya yarda toh aure kam ba fashi. Sai da la'asar Anty baby ta dawo daga mkrnta su kuma Anty Maryam a lkcn suke shrn zuwa islamiya. A'ah Anty baby sai ynxu cewar maryam. Anty baby tace " ke dai bari wlhy yau lectures din namu ban zata haka zai kasance ba". Maryam tace "kenan yau bazaki islamiya ba". Wlhy nagaji baxan iya xuwa ba kuma kinga ga abincin dare dole ni xan daura. Anty Maryam tace wane abincin dare ai Anty tariga da ta daura. Cikeda mmki Anty baby tace " Anty fa kikace " eh Anty ta daura abinci hatta abincin rana ma ita ta daura. "Eh ni na dafa abinci ko akwai mtsla". Kamar daga sama suka jiyo muryar Anty. Anty baby tai saurin sunnadda kanta tace " a'a ko daya kawai dai nayi mmki ne". Ai ba abun mmki aciki sbd nan ba da ddewa ba zaki bar mana girki. Anty baby ta dago ta kalleta cikeda alamar tmbya a fuskarta. Anty bata jira cewarsu ba tai gaba abunta. Maryam tace Anty wai me matarnan ke nufi, kar dai ace wani abun take kullawa. Anty baby tace ynxu ki dai bar wnn mgnr har Ku dawo tukunna kada kuyi latti. Maryam tace toh badan ta gamsu ba ta fice waje.

Wanka Anty baby tafara yi kafin tayi alwala tayi sllh tana gamawa ta shiga kitchen dan duba abnda Anty ta daura. Ta na isa ta ga Anty tana kwashe farar shinkafa ixuwa warmer. Anty na juyowa ta ganta. Aaaah baby je ki huta ai na rigada na kammala sai dai in xaki yanka fruit ita dai Anty baby bata ce komai ba ta tsaya tana kallonta sai dai girgixa kai kawai ta iya yi. Anty tayi wani shu'umin dariya barin ma yanda taga Anty baby na kallonta tace kina mmki ne? Wai naga kin kusa barin gidan ne shiyasa nace bari tun kafi ki tafi na fara rage miki aiki. Wani mugun faduwar gaba Anty baby taji tadago ta kalle Anty tace bangane mey kike nufi ba. Eh nasan bazaki ganeba amma nan ba da ddewa ba zaki gane inda na dosa cewar Anty tana gama fadin haka ta fice xuwa dakinta. Anty baby tace cikin xuciyarta "wai me ta ke nufi da haka ne, kaddai ace wata kulalliya ta kulla mun dan ta fitar dani daga gidannan. Toh in ma hakane Allah bazai taba bari a cutar da bawansaba.

#vote
#share
#comment

Gsky I'm really disappointed in u guyx it won't take u a minute to click on dat small yellow angelic star by ur left. Pls improve else I won't post any update again.😢😢

Har ynxu taku ceh

Anty pink💋

💞komai daren dadewa💞Where stories live. Discover now