LAMBA TA ƊAYA

4.8K 118 4
                                    

[9/2, 18:29] Lovly tah 1: *KISHIYA*





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍.*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai ɓata,burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da lahira._}



*NA*







*UMMU NABIL*




*NO.3*








Washe gari kuwa bayan na kammala komi nawa,na fita parlour,zaune na iske Maman Yara tana kallon TV gefen ta na samu nima na zauna earpiece ne kunne na kamar kullum ina sauraron sautin dake tashi,ina kuma bi,kallo na Mama tayi ta girgiza kai,ta kuma kallo na a karo biyu,gaza yin shiru tayi tace

"Ina fatan karatun Allah kike sauraro bana shaid'an ba?"
Bata Masan mi take fad'a mata ba,sai kad'a k'afa data ke,a k'ufule kuma cewa"Wallah Du'a karki kuskura nazo inda kike don zuwana bazai maki dad'i ba,ina ai tayi nisa bata jin kira can kuma daga gefe guda ta jiyo kamar ana magana,d'agowa tayi sukayi ido hud'u da Mama,wadda ta cika ta batse don haushi da sauri ta cire tace


"Mama sai naji kamar kina magana,don Allah kiyi hak'uri,banji mi kike ceba wallah,yanzu inajinki" banza tayi da ita,ta maida kallon ta kan TV magana Du'a ta kuma yi,cikin fushi Maman Yara tace

"Wallah ki kiyayeni inabaki son ranki yayi mummunan b'aci wallah,sabida iskan ci ke bazaa fad'a maki magana guda kiji ba,wato kin fiso ayi ta maimaita magana guda akan ki,ko toh wallah ki kiyaye ni,kina son na k'wace wayan naki shisa,kuma nima zan fita harkar ki,tunda naga kamar d'aurin gindin da kike samu daga gareni yana neman ya saki fito da wani wulak'anci na daban ama tunda haka kika zab'a shikinan." Cire earpiece d'in tayi ta shiga bata hak'uri saboda taji tana fad'in k'wace waya ita kuma bata shiryawa hakan ba,hannu biyu ta had'a tana bata hak'uri,ana haka Ya Aliyu ya shigo,jin sai bada hak'uri take ya sashi takowa har inda suke bayan sun gaisa da Mama yace

"Wai mi yake faruwa ne nikam,naji sai bada hak'uri take halan tayi wani laifin ko" ya fad'a yana kallon Mama.





"Hmm barni da ita wallah tana son mu b'ata.." Nan ta labarta mashi abinda take,ai kuwa shima nan take ya ara ya yafa, yace"


"Lallai kam ai babu musu ma,bani wayanki," ya fad'a babu ko alamun wasa atare dashi,hawaye ni ya fara zubo wa sharsharshar ya kuma maimaitawa,cikin sauri ta mik'a mashi jikin ta har rawa yake,

Kallon shi tayi tayi rau rau ido,tare da tab'e baki dama tuni hawaye ya gama wanke mata fuska,bud'e baki tayi zatayi magana,ya d'ora hannun sa bisa kan lips nata yace

"Kul kikamin kuka,inba haka ba yau sai jikin ki ya fad'a maki,kuma daga yau babu ke babu rik'e babbar waya, assignment kuma idan an baki kina zuwa wurina sai kiyi da system nawa"daga nan yayi ma Mama sallama ya saka kai ya fita.




Mama dama tana daga can stairs tana hango su duk abinda sukeyi dad'i taji cikin ranta,bata k'araso ba ta fasa yin abinda zatayi kawai ta koma ciki.



Kuka ta zauna tayi ta Rusa ma Maman Yara,ita fa a Bata wayan ta,inba haka ba ta daina Kula kowa ma agidan.Maman Yara tayi dariya sannan tace

"Yaro kinan man kaza,yoh Du'a don kin daina kulamu sai me,ke kad'ai zakiyi rayuwarki muma muyi tamu,kuma ke Zaki sha wahala saboda mu muna da yawa ke kuwa ke d'aya ce,Kinga ni na tafi ma karki ishen da shirme"daga haka ta tashi ta barta zaune nan tana kuka,ganin babu sarki sai Allah yasa ta tashi ta koma d'akin ta.



Ranar kuwa haka ta yini zaman d'aki ko abinci Bata fito ta ci saboda bak'in ciki,jira take kawai Ya Usman ya dawo ta shaida mashi laifin da kayi mata tasan shi zai siya mata wayan,Tana wannan tunanin Mama ta shigo tace


KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now