LAMBA TA UKU

1K 35 0
                                    

[9/10, 14:14] Lovly tah 1: *KISHIYA*






®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏽*
_{Gaskiya d'aya ce daga k'inta sai b'ata burin mu mu fad'akar da Al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_





*NA*



*UMMU NABIL*




*NO.11*








Da hanzari ta kashe wayar ta nufi d'akin ama yana toilet,don haka ta samu wuri ta zauna tana jiran fitowar shi,ta gumi ta zuba,tunani kala-kala take cikin ranta daurewa kawai zatayi tayi magana ama ji take tamkar ta kashe shi saboda kishi,yana fitowa kuwa ko kallon inda take baiyi ba,ganin haka yasa ta tashi taje gare shi,daka tar da ita yayi tare da cewa

"Karki kuskura ki matso inda nake,inba haka ba,ranki zaiyi mummunar b'aci"jin haka yasa jikin ta yayi sanyi,ama duk da haka bata fasa kusantar shi ba,ya kuma daka mata tsawa tare da cewa

"Ai bansan ke baki da tunani ba wallah Mahfuza kin bani mamaki,ban tab'a tunanin haka daga gare ki,ama karki damu idan kinga hakan ta faru kinga da gaske nake,sai naga haukar taki zata kaiki gidan mahaukata ne ko kuwa"Zaro ido tayi sanan tace



"Banshigo wurin ka domin mu cigaba da cece kuce kamar yara ba,na shigo ne da niyyar silhu,ama tunda naga abin naka yana neman wuce gona da iri mu zuba mu gani,zaka sha mamaki,kai da samun farin ciki kuwa a rayuwar ka har abada,na fad'a maka kuma ka rubuta ka ajiye"Fuuuu ta fice daga d'akin,ta koma nata d'akin,rufe k'ofa tayi ta fad'a kan gado ta shiga rusa kuka,wayan ta ta ciro ta kira Maman ta bugu uku ta d'auka jin kukan d'iyar tata ba k'aramin tada mata hankali yayi ba,tare da hadda sa mata fad'uwar gaba cikin sassarfa tace

"Ke waye mutu,fad'amin naji,Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

"Mama Babu wanda ya mutu,sai dai ni da ake k'ok'arin kashe ni da raina,na shiga uku Mama ki taimaka min,wallah kashe ni zaiyi"ta kuma rushewa da kuka.

Jin haka yasa Mama yin shiru tana nazarin kalaman ta sannan tace"Kiyi shiru kimin bayani,ke dad'ina abu k'alilan ne zai tayar maki hankali baki iya dangana da abun duniya ba,kinga mi yake faruwa bani labari tundaga farko"Haka ta shiga yi mata bayani,tass aikuwa tana gama sauraron ta,tace



"Kan Bala'i!baki bata labarin cewa uwar ki ma haka take zaune ita kad'ai sai abinda takeso shi take yi agidan mijin ta ba,maza-maza ki shaida mishi idan ba haka ni zanzo gidan da k'afafuna"


"Mama,wallah duk abinda zanyi duk inda zan shiga zan fita don naga na dakatar da wannan auren don bazau tab'a yiwu ba Mama kiyi wani abu akai"


"Ke dakata kijini da kunnen basira,ina so daga yanzu,daga rana irin ta yau inaso ki fita harkar shi,babu ke babu shi,karki sake wata hanya ta had'a ku,karki bashi fuska,kinji na gaya miki,ki bari har sai nayi wani abun,share hawayen ki,kina dani kuma baki da matsala,keda matsala har abada kinji ko"


Ta kuwa share hawayen ta,daga nan suka yi sallama.



_Toh fa masu karatu kunji fa wata uwa_🤔




Haka ranar ta kwana cikin bak'in ciki,da rashin walwala,washe gari yayi shiryawar shi ya fita ko sallama bai yi mata,itama ko bi takanshi bata yi ba,bayan fitar shi da 'yan mintuna ita ma ta shirya ta tafi gidan su Mabruka daga nan suka kama hanya.




Commen N Share


*UMMU NABIL*
[9/10, 14:15] Lovly tah 1: *KISHIYA*






®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏽*
_{Gaskiya d'aya ce daga k'inta sai b'ata burin mu mu fad'akar da Al'umma domin ribantar duniya da lahira.}_





KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now