LAMBA TA TAKWAS

750 39 5
                                    

[10/8, 20:29] Lovly tah 1: *KISHIYA*














®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼





*NA*






*UMMU NABIL*










*NO.31*




Zama Aunty Momy tayi tace"Wallah zan saɓa maka idan kana saka min ɗiya kuka,haka kawai tunda tace bata so ai sai ka ƙyale ta,imm inyaso ni idan nazo zata bayar,maza yi shiru abin ki maza goge hawayen ki bata ta tasha kinga ai tana jin yunwa".






Goge hawayen ta tayi da ƙyar tana cije baki wai ita zafi ta bata.Mahfuz yace



"Shagwaɓar kawai,Allah Aunty ke kike zugata ma".ya faɗa tare da marairaice face nashi.




"Zaka gamu dani idan baka yi ma mutane shiru ana ba".



Ta juya ta kalli Du'a tace"Wai ina son tambayar ki,meye ya same ki a goshi ne ya fashe?".




Gaban Du'a ya yanke ya faɗi,take ta fara hawaye nan da nan-nan taji abin ya dawo mata sabo kwata-kwata bata ko son ganin Mahfuz kallon Aunty tayi ta nuna Mahfuz da yayi tsaye yana son jin mi zata ce,sai kawai yaga ta nuna shi tana hawaye.


Zaro ido yayi waje tare da tuna kansa yace"Ni kuma yaushe,Allah Aunty Momy lokacin ina shigo wa na dawo daga wurin aiki Na ganta a ƙasa bata motsi shine na kawo ta asibiti".



Cike da mamakin kalaman shi take kallon shi ta fara girgiza kai.shiru Aunty Momy tayi tana nazarin kalaman Mahfuz tace"Kira min Doctor".



"Doctor kuma Momy mi zai yi dama?".



"Nace ka kira min shi ko".

Babu musu ya fita,Mahfuza data bushe da zaman jiran shi,tana ganin ya fito ta miƙe,tunanin ta ya fito ne,don su Tafi sai taga ba wurin ta yayo ba,koma wa tayi ta zauna a zuciyar ta tunani iri-iri fal ya hana ta sukuni.





Tare suka dawo da Doctor lokacin Du'a ta shirya,tana zaune bakin gado suka shigo ɗauke da sallama a bakin su.Aunty Momy tace



"Ahmm Doctor dama ina son ce ne,yarinyar nan tunda ta farka bata yi magana ba Kuwa da wani abu ne?".



Shi kanshi Mahfuz bai taɓa kawo haka a ranshi ba,tunanin guda ko duk cikin shagwaɓa ne yasa yin hakan wato duk inda babba yake yafi yaro zurfin tunani.



"Gaskiya Hajiya ba ƙaramin zurfin tunani kika yi ba,wallah ko arai banyi tunanin haka ba,ganin zata ci zata sha yasa ban kawo akwai wani abu dake damun ta ama yanzu za'a je ayi hoton kai nata idan akwai wata matsala zamu gani".



Haka suka rankaya suka je inda ake hoton kai aka yi cikin lokaci ƙanƙani aka basu suka dawo ma da Doctor,bayan su Du'a sun koma ɗaki.


Bin ciken farko ya nuna ta samu matsala a kanta samakon Buguwar da tayi,jijiyar dake fitar da sautin magana ta samu matsala a halin da ake cike ta daina magana.



Lokacin Da Doctor yake baya nin Mahfuz ji yake tamkar labarin wani ake bashi ba Matar shi ba,kallon Doctor Na'im yayi yace"Wai labarin waye ne kake bani dama?".



Ɗan murmushin ƙarfin hali Doctor Na'im yayi yace"Am sorry to say Matar ka,ta daina magana sai a hankali bazan ce har abada ba,saboda Allah shine mai halitta shine mai rayawa shine kuma mai kashe wa".




KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now