LAMBA TA GOMA{ƘARSHE}

1.3K 47 3
                                    

[10/24, 12:23 PM] Summy: *KISHIYA*








®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼






*NA*




*UMMU NABIL*





*NO.37*



A zabure Mama ta tashi zaune tana karanto sunayen Allah,saboda irin halin da taga Du'an ta a ciki,cikin hanzari ta miƙe ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta shimfiɗa sajjada ta shiga nafila tare da nemarwa Maimunatu kariya daga mugun abunda taga ya tun karo ta.


Ɓangaren Du'a kuwa rarumar Hunaida tayi ta rumgume ta a ƙirjin ta,ta shiga addu'a hawaye nabin kuncin ta,gashi babu haske ɗakin takai hannu inda wayan ta take zata ɗauka,wani mugun sara taji an kaima hannun ta,tsoron ta ya ƙara hauhawa bata dai daina addu'a ba,ta kuma ƙamƙame Hunaida a ƙirjin ta.



Duk iya ƙarfin ta ta buɗe muryar ta kwarara ihu tare da kiran Sunan Aunty Momy,a fusace Aunty Momy ta juyo ta kalli inda ɗakin yake a miliyan suka kwaso suka yo ɗakin,suna isowa suka same ta a tsaye ta ƙamƙame Hunaida idanun ta a rufe,banda ƙyarma babu abinda take.


Har ta kai hannu zata taɓa ta sai ta fasa ta kira sunan ta,a kiɗime ta buɗe idanun ta ta sauke su kan Aunty Momy da Baban Mahfuz.ga kuma hawaye shaɓe-shaɓe dake kwance kan fuskar ta.

Aunty Momy ta taka har inda take ta zaunar da ita a bakin gado,kallon hannun ta tayi wanda sai jini yake zubarwa,ba ƙaramin tashin hankali ya ziyarci ranta ba tace,

"Subhanallah!me ya faru mai ya same ki,bugewa kika yi baki gani ne har kika fasa hannun ki haka Maimunatu???".

Sosai Baban Mahfuz yake nazarin Du'a yace,



"Hajiya".

Aunty Momy ta amsa da na'am.ya cigaba da cewa,

"Zo ina son magana dake".

Miƙewa tayi tabi bayan shi,suka fita harabar ɗakin cikin nutsuwa yace,


"Gaba ɗaya yadda nayi nazarin ciwon Mahfuz da duk wasu abubuwa dasuke faruwa ciwon su kaf bana asibiti ne ciwo ne wanda ya danganci mugun sihiri,ke baki duba da haka ba?".

Ɗan jimm Aunty Momy tayi ta nisa cikin tunanin ta ɗago ta kalli Baban Mahfuz tace,

"Tabbas na lura da haka,kuma ina iyaka iyawa ta wurin yi masu addu'a dai-dai gwargwadon iko na,saboda da ace na asibiti gwaje-gwaje da ake gabatar wa akan Mahfuz yaci ace an gano abinda yake damun shi,kaji dai yadda na shaida tun daga farkon abinda ya same shi".

"Hakane shisa nace maki bana asibiti bane,banƙi bama ace ko Hunaida ama daga shi har Maimunatu ciwon su yana buƙatar addu'a bata wasa ba kuwa,saboda haka yanzu kije ki tambaye ta abinda ya faru ni kuma zanje na sanar da Malam Ahmad Sulaiman abinda yake faruwa duk yadda yace zan kira ki kinji".

"Toh ubangiji ya bada sa'a,Allah yasa mudace sai na jika".

Daga haka suka yi sallama yabar asibitin ya kama hanyar gidan Ahmad Sulaiman dake anguwar Karkasara babban layi.ita kuma Aunty Momy ta koma ciki.




"Maimunatu me ya faruwa dake faɗi min naji?".


Goge hawayen ta tayi ta shiga rattabawa Aunty Momy abinda ya faru,sauke numfashi Aunty Momy tayi ta kalli Du'a tace,


You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 06, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now