LAMBA TA SHIDA

942 36 2
                                    

*KISHIYA*














®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼





*NA*





*UMMU NABIL*




*NO.20*





"Hello Mabruka kina jina?ke dole mu koma wurin boka yau ko gobe,bazai yiwu ba,idan banyi da gaske ba,wallah yarinyar nan nema take tak'wace min miji,wanda ko a mafarki bana ganin hakan zata yiwu bare kuma a gaske,kinga yanzu meye abinyi?"



"Hmm K'awata kinan karki damu kanki,bare ki nemi ki d'orawa kanki ciwo,yanzu abinda na saka ki daren jiya kin aiwatar kuwa?"



"Eh nayi mana yazo har sai da muka d'an gaisa ma kad'an tukun nace ya shaida mashi yadda zaiyi,kuma ke abinda nake tunani ya afku tsakanin su,shisa gaba d'aya hankali na ya tashi,kinga fad'a min yaushe ne kike da lokaci?"






"Ai kin gama magana,kuma yanzu gaskiya bazai yiwu ki fita a wanann rana kun ba,saboda duk wanda yazo zai tambaya kina ina,kuma bamu son aikin mu ya samu matsala,kedai ki cigaba da yin abinda nace maki"Mahfuza ta amsa da toh.Daga nan suka yanke kiran.



Bayan sun koma d'aki kuwa Mahfuz tunani ne yazo mai cikin ranshi yace"Ai bai kama ta ace,daga gidan su za'a kawo mata abinci ba,sai aga gazawa ta akan hakan yace da ita"Bari na kira Aunty Momy ta baiwa Mubin ya kawo mana abinci kinji,bani waya ta"mik'o mashi wayar tayi ya kira Aunty Momy buku uku ta d'aga bayan sun gaisa,ta tambayeshi amarya yace

"Aunty Momy Muna son abinci ki bawa Mubin ya kawo mana,idan yana nan,idan kuma baya kusa ki bawa driver ya kawo mana"



"Mahfuza bata nan ne?"Aunty Momy ta tambaya.


"No Momy tana nan,tace kanta yana ciwo ne"Okay inji Aunty Momy,nan kuwa tasan k'alau take sai dai tsiyar banza kawai.




Bayan minti Talatin kuwa mai gadi yayi mashi waya yace yana waje,fita yayi ya amsa ya dawo ciki,a palour ya tarar Mahfuza da rigar dai ta d'azun bata canja ba,da alamu kuma bata yi sallahr ba,kamar yadda tace,kallon banza ya aika mata,da sauri ta mik'e ta biyo tace


"Yawwa bari nazo muci"ko kulata baiyi ba,har d'akin Du'a ta biyo shi,dire abincin yayi ya shige kitchen ya d'auko cokali da flat ya dawo,ci kanki bai ce da ita,ya zuba abincin yace da Du'a



"Bismillah"sakkowa tayi ta zauna,suna fuskantar juna murmushi yayi yace"Ko baki iya ci da kanki na baki?"satar kallon Mahfuza tayi taga tayi daga lo tana kallon ikon Allah,ganin haka yasa ta wani marairaice fuska tace



"Ka fara ci tukun,ko kuma kana bani ina baka"wani malolo ne yazo ma Mahfuza wuyan ta ya toka re ta,ta rasa yadda zata yi kawai sai ta mik'a hannun ta zata ci da sauri ya daka tar da ita ta hanyar cewa



"Karki kuskura kisa min wannan hannun naki anan,wanda ko wanka bai samu ba bare ya samu ayi ibadar Allah dashi"matuk'a taji haushin kalaman shi ta maze tace


"Yoh kai waye fad'a maka banyi sallahr ba,naga wankan dai yanzu zanje nayi,kasan dai idan mutum yana jin yunwa baya iya aika ta komi, kaga nifa ba zuwa nayi ku cimun mutun ci ba,idan zaka bani ka bani idan kuma baza ka bani ba,naje nayi da kaina"



"Ai da kinsan zaki iya kiyi girkin kika zauna b'ata yawun bakin ba,tashi ki fitar min anan"yana yin maganar da yayi sai da jikin ta yayi b'ari,da sauri ta tashi tana gungini,ta fice.




KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now