LAMBA TA TARA

797 41 0
                                    

[10/24, 12:23 PM] Summy: *KISHIYA*





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*_ƘARYA DUKA ƊAYA TA RUGU JE👊🏽,A DAƊE ANA SAI GASKIYA_*




*NA*






*UMMU NABIL*

*INA GODIYA SOSAI MASU BIN NOVEL NAWA,KUMA KUNA HAƘURI IDAN BAKU JINI BA,WALLAH YANZU BANA SAMUN LOKACI,KUMA TUN FARKON FARA LITTAFIN NA SHAIDA MAKU BANDA WEEKENDS A POSTING SBD ƘAIDAR ƘUMGIYAR MU NE HAKAN NAGODE SOSAI*


*NO.35*




A kiɗe me tare da rashin makoma Aunty Momy ta kira sunan shi,ama kafin kace meye wannan ko motsi baya yi,ganin haka yasa Doctor Na'im saurin ƙarasowa inda yake tare da tambayar meke faruwa.


Banda kuka babu abinda Du'a keye cike da tashin hankali ta buɗe baki tace,


"Doctor ka taimaka mana kamar yadda Allah ya taimaka,kaga akan Matsalar yarinyar da aka kira ka,kuma sai gashi shima wata matsalar ta same shi don Allah ka taimaka mana".ta ƙarashe tare da rushewa da matsanan cin kuka,Aunty Momy kam banda safa da marwa babu abinda take yi a cikin ɗakin,Mahfuza kam ƙemagadau idanun ta babu alamun danasani acikin sa.sai wani harare-hararen banza da wofi take.



Sai da ya fara duba Hunaida ya ɗago ya kalle su cikin kwantar da murya yace"Alhamdulillah da ranta ba kamar yadda kuke tunani ba,sai mu godewa Allah".

Hamdala suka yi ma Allah,banda Mahfuza data doka uban tsaki ta fice daga ɗakin, kan Mahfuz ya koma ya shiga duba shi cikin nutsuwa shima dai cikin ikon Allah ya farfaɗo idanun shi rufe sai jujjuya kai yake faɗin,

"Momy Karki raba ni da matata wallah indai na rasata mutuwa zanyi please Aunty nasan kina min komi ina so a wannan karon ma ki taimaka min".gaba ɗaya hawaye sun wanke mashi fuska sharkaf kai kace tap aka kunna yake shatata.


Ta rasa inda zata saka kanta,Doctor Na'im ne yace,



"Aunty Da alamu yana cikin matsanan ciyar damuwa,idan har bazata gagara ba,Momy ina son ki taimaka ma Aboki na,kiyi mashi abinda yake da buƙata"yayi shiru yana jiran furucin da zai fito daga bakin ta.


"Babu komi,Doctor Karka damu ubangiji zaiyi mana jagora,yanzu ka rubuta mana medecines in yaso sai na bayar a siyo, in kuma ba yanzu Zai samu ba zan turo Yaro sai ya amsa".



"A'a zai samu yanzu ama sai dai Na Baby shi ina tunanin gaskiya sai mun dangana da asibiti,bari na rubuta maki na Hunaida".nan take ya rubuta ya miƙa mata ya kalli Du'a yace,


"Masha Allah,ashe madam baki ya samu".sai lokacin Aunty Momy ta tuna da hakan ta kalli Doctor tace,

"Ban fahimci zancen ka,wai Maimunatu kake nufi ba?"Ikon Allah kasan Allah da ike na shigo ba hayyacina ba kwata-kwata ban lura ba".


Haka suka yi ta hira akan maganar daga bisani Aunty Momy tace Maimunatu ta shirya saboda asibiti zasu wuce.

Kallon Momy tayi da alamun tambaya tunda ita yanzu ba matar shi bace tace,

"Ama Momy.."bata ƙarasa ba ta dakatar da ita tare da cewa,

"Nasani,nasani kiyi yadda nace bamu da lokacin ɓatawa tunda kinga dai halin da muke ciki ba?".

KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now