LAMBA TA HUƊU

712 37 1
                                    

[9/11, 14:29] Lovly tah 1: *KISHIYA*






®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

         🎐 '''G•W•A'''🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼




*NA*






*UMMU NABIL*




*_Jinjinar ban girma gare ku,Aunty mariya,Ammin Muntasir,Ummy ontop,Mmn Mu'azzam,Mmn Ibtisam,Jiddah(Grp Mene Matsayina),Ummu Abdallah(Ummu Babana)Zee Smart(Zumunta Novella) ina godia da comment naku ku cigaba dagashi yanzu aka fara wasan_*




*NO.16*




Maganar biki ta kankama,ko wanne b'angare nasu shirin suke gyara kuwa ta b'angare amarya ba'a magana,saboda yanzu Du'a tayi hankali ba yadda kuka santa ba..



Mahfuza ce zaune gaban Boka Dak'ayanus wanda ya bata k'ulle-k'ulle iri daban-daban wanda zata k'ara kama su su duka a hannu Boka yace


"Abinda nakeso ki gane kuma ki fahimta shine,kinga mudai muna iya namu yin ama bamu isa mu datakar da Abinda Allah ya k'addara ba,saboda haka na hango abubuwa da yawa tare da ita wannan yarinyar sai dai,bazan iya fad'i miki koda guda kuwa daga ciki ba,ama inason ki kwantar da hankalin ki,kuma ban gaya miki,sati biyu da suka wuce na aika aljani Lamarutu ya kai mata ziyara kuma ya bani tabbacin zamu yi nasara akanta"dariya Mahfuza tayi saboda jin dad'in kalaman Boka Dak'ayanus tace



"Aikuwa indai haka ne,baka da matsala kuma duk abinda kake so zaka samu ko ya kasance mai tsada ne daga gare ni"dariya yayi irin tasu ta bokaye yace



"Toh toh baki da damuwa nima kuwa zanyi miki abinda kike so,kuma zaki kasance mai samun nasara ako yaushe,zaki zamo ta gaban goshin mai gidan ku,sai abinda kika ce,ama ina k'ara fad'a maki,sai kinyi hak'uri saboda aikina yana tafiya dai-dai da yadda nake tafiyar dashi saboda haka sai ranar da tashigo gidan ki,da d'an wani lokaci kad'an kinji ko"murmushin jin dad'i tayi tace


"Nagode Boka Dak'ayanus"Boka yace

"Karki damu,shi wannan idan kin koma gida zaki fara amfani dashi kinji ko?" ta amsa mishi da toh.

Daga nan ta tashi tafi,gida ta har had'a abinda boka ya bata harda wanda zata saka ma Mahfuz a abinci.




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°Yau ta kasance ranar da za'a fara bikin Mahfuz Da Maimunah wato Du'a ba'ayi wata bidi'a ba duk da Mahfuz yana da kud'in dazaiyi iya ka Dinner da akayi bayan an d'aura aure a daren ranar kuma za'akai ta,fad'a da nasiha babu irin wadda ba'ayi mata ba,jikin ta tayi mugun sanyi iya kuka kam tasha kuka cikin yayinta kuwa babu wanda baiyi mata fad'a ba,haka ma B'angaren su Mama,Maman Yara harda kuka saboda wata irin shak'uwa ce tsakanin su da Du'a ita ma Du'an haka ta k'ank'ame Maman Yara tak'i sakin ta,babu irin bakin da ba'a bata ba ama sam tak'i sakinta,ganin haka yasa Ya Aliyu yaje ya kira Baba dakan shi yazo ya kama hannun ta k'awayen ta 'yan uwanta tana ji tana gani haka ta barsu,su Halimatu ma sai kuka suke.

Har cikin Mota Baba ya saka ta,bisa sunnah shine zai kaita gidan ta dakanshi,sai Ya Aliyu dake driving motar sai kuma ita Amarya.Dake ta faman kuka.




Suna isa mai gadi ya bud'e masu suka samu wuri suka yi parking Baba ya fito da ita dai-dai bakin k'ofar parlourn Har ta taka k'afar ta Baba ya dawo da ita yace


"Ki fara saka k'afar dama sannan ki karanta ayatul kursiy da amanarrasul da falak'i da nas d k'ul huwallahu ahad k'afa uku -uku"hakan tayi duk da muryar ta ta dashe wurin yin kuka,sannan tayi bismillah suka shiga har parlourn ana suka iske k'awayen Mahfuza sai shewa suke duk da suna ganin su a bakin parlourn ko gaisuwa Baba bai samu daga gare su ba,sai da Ya Aliyu yace

KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now