LAMBA TA BIYU

1.6K 54 2
                                    

[9/10, 14:14] Lovly tah 1: *KISHIYA*






®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍🏽*
{Gaskiya d'aya ce,daga k'inta sai b'ata,burinmu mu fad'akar da Al'umma domin ribantar duniya da lahira.}






*NA*





*UMMU NABIL*




*NO.4*





Haka muka Sha Hira da Muhseen sai gaf da magriba yace min zai tafi,muna tsaye na rakoshi bakin gate Baba dasu Ya Aliyu motar su ta sako Kai,bai jira sun iso ba mukayi sallama ya tafi.






Da dare Ana zaune a parlour kasancewar al'adar gidan muce duk kowa zai zauna bayan magriba sai dai idan kana da uzuri Mai k'arfi,Ina gefe nayi tagumi saboda jina nake tamkar bana duniyar saboda Waya ta da Ya Aliyu ya k'wace min,kuma shi na kalla harkar shi yake to babu alamun zai bani,duk juyin Dana yi kuwa sai na saci kallon gefen da yake,wai kozai tuna Dani ama shiru kake tamkar an aiki bawa garin su,Yaya Usman ne ya lura da halin Dana ke ciki,ya juyo da kallon shi gareni tare da cewa



"Yar Maman ta,mi ya faru ne nikam,Naga tun safe ban ganki cikin walwala ba,halan wayan ki ya samu matsala tunda Naga ba'a aikin da aka Saba"ya fad'a cike da zolaya.kamar jira take ta taso kusa dashi ta samu ta zauna tace



"Ai ni da matsalar ma ta samu to da sauk'i"ta maida kallon ta inda Aliyu yake,shikam ko kallon su baiyi ba,suna magana da Baba,shiru Usman yayi,daga bisani yace


"Bangane mi kike nufi ba k'anwata,bani nasha"harda gyara zaman sa,ai kuwa Nan take ta bashi labarin abinda ya faru.



Duk Baba Yana ji kasamcewar ya raba hankalin shi gida biyu,b'angaren Aliyu ma haka take a tunanin shi zata k'ara wani abun.sai yaji babu k'ari a zancen nata.




Baba ne ya dakatar da zancen da sukeyi,yace

"Yawwa ai nikam yayi min dai-dai wallah,dama nima inada niyyar yin hakan,ka kyauta kuma Abu na biyu shine waye Wanda yazo wurin ki d'azun,na uku kuma gobe Salman zaizo munyi magana da Kawun ki,yace bayana Nan ama idan ya dawo zaizo".



Ai gaban tane ya buga rasss ta dafe k'irji,cikin zuciyarta tace,yau ni Naga ikon Allah,Ina ma ban dawo daga makarantar bama nayi Zama na,kodan sunga na k'ara cika da girma shisa suke son yimin aure ban shirya ba nikam,ohhh Ni Maimunatu.ganin ta zuba mashi ido yasashi cewa


"Yau Naga ikon Allah,Ina tambayarki maimakon amsa sai zuba Mani ido da kikayi halan bakiji abinda nace ba ko?"

Ido ta shiga k'iftawa,tare da inina tace"Baba aboki na ne fa,kawai ya kawo min ziyara ne mun gaisa ama babu komi tsakanin mu Allah kuwa Baba wallah Allah"mamaki ne ya cikasu su duka Usman ya Kalli Abbakar tun zaman su yake Danna waya sai yanzu daya bud'a baki yace


"Kinga Du'a wallah yau idan bakiyi wasa ba sai na Zane maki jiki,dama tunda Kika dawo ban tab'a lafiyar ki ba shisa,mi yeni abin rantsu haka,duk Wanda yafiya rantsu to zancen shi akwai k'arya a ciki saboda haka shiga hankalin ki bana ciki da iskanci"Rau rau tayi da ido ta fara matso hawaye zata bud'e baki tayi magana Baba yace

"Tashi ki bamu wuri,shagwab'b'iyar banza da wofi"Mai makon ta tafi d'akin ta sai ta fad'a kan Maman Yara ta shiga rera kuka,ita kuma ta shiga rarrashinta tana bubbuga mata baya.

Mama kan don haushi tashi tayi,tayi masu sallama ta shige d'akinta,Kai tsaye bayi ta shiga Tayo alwala ta shiga yima Allah bauta,tare da nemarwa d'iyar Tata mafita.



Yau bama a d'akinta ta kwana ba,ita da Maman Yara suka kwana.da safe kuwa bayan sunyi wanka sun karya,tun wurin k'arfe Sha biyun Rana tace zata je gidan su Halimatu Wanda ake ma lak'abi da(Miss Xerks)haka ta yini gidan saboda k'awarta ce sosai kuma ta fad'a mata duk abinda ke damun ta,ta Bata shawara sosai,daga nan tayi ma Hajiyar su Halimatu Sallama suka fito domin ta taka mata,suna tafiya Kafin sukai titi Halimatu tace

KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now