Page 40

5.6K 265 14
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

                       *KWARATA*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

                         &

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 40

             Miƙewa yayi bayan ya gama surutanshi ya fita babban palo maƙulin motarshi ya ɗauka ya fita , ina tsaye a jikin window ina kallonshi har ya shiga mota ya bar gidan da gudu bansan inda zaije ba , kuma ga dukkan alamu bazai kwana gidan ba , murmushi nayi tare dayin magana ƙasa² nace sauka lafiya.

     Yana fita na dawo na kwanta saman katifa naja bargo na lulluɓe na rufe idanuwana ina jinjina irin wulaƙancin da Dikko yayi mana shi mai kuɗi , "yar madara dabbace amma duk lokacin da naji an kira sunan mage ko na ganta sai magena ta faɗon min a rai da Dikko yabi ta kanta da mota bataji bata gani ba ,

      Wulaƙancin da yayi ma Babana a ranar daya wankemin ubanda yafi ko wane uba a wurina da ruwan taɓo , lokacin daya bugamin kanshi har na suma , uwa uba ƙarshen wulaƙanci daya keta min mutuntaka ta , idan ma har zuciyata ta bari ƙiyayyar Dikko ta goge a cikinta ban yafewa kaina , ɗaukar fansa ƙudirina ne kuma muradi nane ko ba daɗe ko ba jima saina kafawa Dikko tarihin da bazai taɓa gogowa a rayuwarshi ba ,

     Maganar cewa idan na kawo mishi na 20 zai rufe ƙofa dani nayi masa rata har abada nayi masa nisan da bazai iya kamoni ba , yanda Annabi ya gagari arna haka na gagareka Dikko sa'a ɗaya kawai nake nema fita daga hannunka amma da zaran na zare tou kwankin hararka sun soma...

      Dukan sitiyarin mota Dikko yayi a daidai wannan lokacin yace wallahi ƙarya kike , dan tunda ya fito daga gidan zuciyarshi tana faɗa mishi Sultana tana sanshi tabbas kuma akwai wannan soyayya domin yaga soyayyashi kwance a cikin idanuwanta !

       Da safe tunda nayi sallah asuba nayi wanka na shirya cikin kayan makaranta , jakata na ɗauka da sauran kuɗina da ban kashe ba nayo babban palo ,

      Na daɗe dan nafi ƙarfin awa ɗaya amma babu Dikko babu alamarshi kuma babu mota ko ɗaya a gidan , tun ina zama na marmari har na fara gajiya na kwanta saidai na kalli agogo nayi tsoki dan gani ma nake lokutan basa sauri , raina fa ya gama ɓaci sosai dan har nayi tunanin kila bayau zan koma ba ,

     Ƙarfe 9:46am ya shigo gidan , a kasalance ya fito daga cikin motar ya nufo palo , kallo 3 nayi mishi kafin ya iso na kauda kaina , kamar yayi kuka dan yanayin fuskarshi ya nuna rai a haɗe kamar hadarin tsakar dare ,

      Da sallama ya shigo palon bai ko kalli inda nake ba ya wuce ciki , na ansa sallamar na gaishe shi bai ansa ba ya wuce , murmushi nayi a zuciyata nace kila matarshi taci ƙaniyarshi , mugu kenan sai lahira a gane halinshi...

      Yayi fata² da awowi biyu sannan ya fito tunda ya fito ƙaramin palon ƙamshin turarunshi ya fara zagaye cikin gidan nan lungu da saƙo bana tunanin akwai inda ƙamshin bai kai ba , ƙamshin turare mai daɗi mai jefa mutum cikin wani irin baƙon yanayi mai wahalar mantawa ,

      Bayan kamar minti biyu ya iso cikin babban palo , wallahi dole tasa na juya dan yanda naji ƙamshi inga wace shiga yayi haka ? Dan nasan bazaiyi wannan ƙamshin a banza ba , yanayin ƙamshin nasan yanayin haɗuwar da zaiyi kuma ba'a magana , dan duk yanda zan musulta muku kyawun Dikko zakuga kamar shiri ne abun , gaskiya Dikko yana da kyau fiye da duk yanda mutum yake zato , tunda nake a rayuwa ban taɓa ganin wayayyen namiji ɗan gayu mai saurin shiga rai kamar Dikko ba , ko ta ina babu inda mutum ya isa ya kushe shi saidai wani halin daban dan ɗan adam 9 yake bai cika 10 ba , Dikko yana da aji yana da natsuwar da ko mace tayi natsuwarshi taci Allah buɗa ,

KWARATA...Where stories live. Discover now