Page 49

6.3K 303 21
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

                       *KWARATA*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

                         &

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 49

       Gaba ɗaya na firgice na fita hayyacina kururuwar da nakeyi ta karaɗe kaf girman hotel in , hayagagata ya jawo hankalin mutane akayo wurina ana lafiya ? Duk wanda na gani sai inga fuskar mutumin nan gareshi wayyo Allahna na shiga 3 🙆🏻 na lalace shikenan mutuwa zanyi na bani ׳ na ƙarasa maganar tare da faɗuwa ƙasa ina burgima.

      Baiwar Allah lafiya ? Meke damunki ? Shine tambayar da mutanen da suka zagaye ni sukemin amma maimakon naji maganarsu sai naji muryar mutumin cikin muryar tsoratarwa da firgitarwa yana cemin da hantarki da ƙodarki ko zuciyarki wanne kika bamu....

      Da sauri na dafe cikina na tallabo saitin zuciyata amma har yanzu wayata na riƙe ram a hannuna , cikin kuka nace wallahi bazan bayar ba , nawa ne ni ɗaya , cikina ne da zuciyata hantana da ƙoda Allahna ya bani ba wani ba , kuma ubangiji bazai baku damar rabani da ko ɗaya ba , wata irin gigitacciyar dariya akayi tare da cewa kina nufin kinci kuɗinmu a banza ? Tou wannan kuɗin ki sani jinin wasu ne da wasu sassa na jikin ɗan adam dole ki bayar da naki kema domin a bawa dodo ya bamu kuɗi zuciyarki zata shiga kwarya , bankwana da duniya sai wata rana....

       Gaggaɓewa akaci gaba dayi da dariya data gigitani a karo na biyu , addu'o'e naci gaba dayi da ƙarfi idan ina addu'a bana gama wata saina saketa na kamo wata , dai najin sautin muryar dariyar nayi sai sautin kuka har zuwa wannan lokacin ban daina addu'a ba , bayan wani lokaci kuma na dainajin sautin kukan gaba ɗaya...

      Da sauri na miƙe ko jikina ban tsaya kakkaɓewa ba nayi gaba , mutane suka bini da kallo yayin da wasu ke tunanin ko ina da taɓin kwalwa ne , da gudu na fita daga hotel in , ina na fita na samu napep sai gidan Mamy amma har yanzu hankali na baya jikina gaba ɗaya a ruɗe nake , napep na tsayawa na fita da gudu nayi cikin gidan Mamy , bata nan sai yara na samu nace musu ina Mamarsu ? Sukacemin yanzun nan ta fita tace idan kinzo ki kirata ,

      Jikina yana ƙyarma na fara laluben wayar Mamy babu ɓata lokaci ta ɗauka , gaisawa mukayi nace mata kina ta ina haka ne ? Sunan hotel in dana baro ta faɗamin tare da cewa wani sabon sauna ne na samu ki jirani na wankoshi cikin mintuna kaɗan zan dawo , kaina ya juya a gigice nace karki je , ki dawo hotel in nan akwai wani gahurtaccen matsafi daya bayyana karki shiga ɗaki ki dawo , Mamy tace wane ɗaki ? Nace ɗakin dana shiga wallahi matsafi ne karki shiga ki dawo akwai zama na musamman , Mamy tace tou lamba nawa ne ɗakin ,

       Da sauri na dafe kaina duniyar ta riƙa juyamin kamar nahau shillo mai wanawa , gafa lambar ɗakin ina gani a idona bana iya faɗa dan na iya lissafin lambobi tunda dasu nake sarving numbobin mutane a cikin wayata , ganin na kasa faɗa kawai nace ....

      Ki dawo........... Na faɗi ki dawo cikin wata irin murya hawaye suka gangaro daga cikin idona ina cewa nidai kawai ki dawo matan aure yake nema ko wane ɗaki bana so ki shiga ki dawo Auntyna bana san na rasa ki adaidai wannan lokacin ki dawo dan Allah na ƙarasa maganar ina durƙushewa ƙasa naci gaba da kuka , amma duk wannan maganar da nayi sam Mamy bata jini ta riƙa hello , hello idan kina jina kawai ki jirani , tana faɗin haka ta kashe wayarta ,

      Da gudu na fita daga cikin gidan , mai napep in daya kawoni shi nace ya maidani inda ya ɗaukoni dan dama ban sallameshi ba , nace kayi gudun bala'e ka kaimin motar nan maleji karka tsaya kuma karka kauce ina so kawai na buɗe idona na ganni a hotel in nan kamar kyaftawar ido ,

KWARATA...Where stories live. Discover now