Page 2

9K 344 49
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

               *KWARATA RETURN...*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

Rubutawa...
            *JAMILA MUSA...*

       *SAI NA AURI D ' K*

*ASMA'U ZAYYAN* {{ Asmeenat Xeyyan }}

🅿 ------ 2

        Palon ƙasa cike yake da duk wani ma'aikaci dake gidan mace ko namiji gaba ɗayansu hallare suke zaune a ƙasa amma shi mai gidan baya wurin. Duk yadda akayi zaibar ƙasar ne , duk lokacin da akayi irin wannan zaman zaiyi tafiya ne , idan zaije Abuja ko ina ne ba'a haɗuwa sai zai tafi yabar nigeria. Ina ganin haka banma yadda na sauko ba na nufi ɗakinshi.

Da sallama na shiga ya amsa yana gyara ma Papi riga , kusa dashi naje na tsaya ba tare da na sake magana ba , shima baimin magana ba yaci gaba da abinda yakeyi , bayan ya gama yace ma Papi yaje ya jirashi wurin Ashiru yana zuwa , saida ya taɓoni yana murmushi yace kayyalni nayi cau....? Murmushi nayi nima tare da cewa kayi kyau , na ƙarasa maganar ina kallon Dikko dake ta wani haɗe rai , Papi yana fita na ƙara matsawa kusa dashi nace ina kuma zakaje ne ? Rai a riƙe kuma bai kalleni ba yace inda kika aikeni.....

     A ɗan tsorace na taɓashi da hannuna na dama ina kallon fuskarshi , da yanayin tsoro nace yanzu kuma meya faru kake fushi ? Ba komai ya faɗa a taƙaice yana matsawa daga kusa dani , ƙara matsawa nayi inda ya matsa jikin madubi yana tattara wasu takaddu , baimin magana ba saida ya ajiye makullin ɗaki a gabana , girgiza kai nayi alamar a , a , to minene ? Cikin rawar murya nace zanji babu daɗi ne idan ka tafi , da gaske ? Ey , kin tabbata ? Na tabbatar da haka , ai bazan daɗe ba ya ƙarasa maganar yana ɗaukar takkadun ya matsa gaban gado ya ajiye sannan ya nufi wurin weldrop , ƙara binshi nayi na fara kuka , har yanzu yaƙi ya kalleni , amma a tausashe yace kinsan ni bana san wannan kuka²n ko ? Yayi maganar yana miƙomin hannunshi. Riƙe hannun nashi nayi shi kuma ya riƙe tare da shigar dani jikinshi. A kasalance yace yi shiru An matana.

      Cikin kuka nace to me yasa zaka tafi ne ? Yi haƙuri ai zan dawo in Allah ya yadda , kwantar da kaina nayi saman ƙirjinshi naci gaba da kuka , bai sake magana ba kuma bai ɗagani daga jikinshi ba , yadai cire hannunshi daga kaina ne tun lokacin daya shigo dani jikinshi. Kenan bai rumgumeta ba , saidai a ranshi yaji babu daɗi tanayin kuka , a zahirance kuwa ya nuna ko oho da yanayin ma idan tai mishi ɗanyen kai zai zaneta ba abinda ya dameshi , Allah ya sani yana san An mata kuma yana tausayinta amma ta rainashi iya raini dan ko gaban waye idan ta tashi mishi rashin kunya sai taje inda take so hankalinta zai kwanta , kuma ita rayuwa ba'ayinta haka wannan dalilin yasa shi yaja mata layi ya kuma tsare gida yanzu yasan tsoronshi ya fara hawa zuciyarta. Gashi yanzun ma taji tsoronshi shi yasa ta firgita dashi take mishi magana a tsorace , naso na tambayeshi abinda yasa zaiyi tafi bai faɗamin ba , kuma ince mishi kenan da banga ma'aikata a palo ba saidai inji labari baya nan , tou ya wani haɗe rai cikin rashin mutunci , sauka nayi daga jikinshi bayan nasha kukana harna gode Allah duk na ɓata mishi rigar jikinshi da hawaye , ina sauka ya cire kayan ya canja wasu.

       Bayan ya gama ya ɗauki abinda zai ɗauka da wayoyinshi danshi bayayin tafiya da kayan sakawa shi kaɗai ɗinshi yake tafiya saidai ɗan abinda ba'a rasa ba , da ya tashi fita yayi bankwana dani kamar yadda ya saba , ya sumbaceni tare da shafa gefen fuskanta , ya riƙe haɓata yana ɗagota dan mu kalli juna , na kalli cikin idonshi yayi murmushi mai tattare da tsantsar so sannan ya ƙara shafa fuskata ya kama kumatuna da yatsu biyu kamar anayi ma yaro wasa yanamin wani irin kallo , ajiyar zuciya nayi tare da sauke idona wani wuri daban na daina kallonshi , wasa yayi da tafin hannunshi a gefen fuskata { kumatuna }sannan ya fita daga ɗakin ba tare da yayi magana ba. Yana fita na fashe da wani irin kuka mai kama zuciya , yana jin kukan Sultana har a ranshi amma ya daskare yai tafiyarshi.......

KWARATA...Where stories live. Discover now