KYAN DAN MACIJI.........
Part 2
By Zulaihat Aliyu MisauWattpad@zulaihatualiyumisau
🐍. 🐍
No comment, no vote, no update on time, eheee...
Not Edited.
Anty fari ce ta fito daga kitchen rike da wani trey mai kyau, da aka shakeshi da yankakkun fruit. Tasha kwalliyarta cikin atamfa super wax Riga da skirt. Sun mata kyau sosai, baka ce ita ta haifo su Arafat ba.
Dariya sabrin tayi, tana binta da kallo. Ran Anty fari ya matukar baci, amma ta shareta.
" oh!!!! Allah! Naga randa kan mage zai waye? Miji zai dawo, a rasa kwalliyar da za'a masa, sai this thing." Tana sama da kasa, da hannu. Da anyi magana my husband, my husband house!! Amma ba'a san yadda xa'a burge shiba." Sabrin ta fada tana zama kan daya daga cikin kujerun falon, kafa daya kan daya, tana kadawa a hankali, Idonta a kan Anty fari tana mata dariyar rainin hankali
Shiru Anty fari ta mata, ta ci gaba da kananun ayyukanta. Zuciyarta cike da kunci, da takaici, yadda kanwar bayanta ta samu bakin gaya mata magana son ranta, bata son biye mata, Don every moment mai gidan zai iya shigowa. Wanda ta lura abinda Sabrina din ke so kenan, ya dawo ya samu suna hayaniya, taji dadin gaya masa karya da gaskiyar da aka mata baya nan.
Tsayuwar mota, tare da hone shiya katse zaman shirun. Yara sukayi waje da gudu, don tarbar Abban nasu. Cike da murna.
Sanye yake cikin manyan kaya, light blue gezner, Jamfa da wando, sai babbar riga da tasha Aiki, ya murza hular damanga black, kafarsa na sanye da black cover shoe, kyakyakwan mutun a kalla zai kai 45years, Wanda hutu da jin dadi, ya kara boye shekarun nasa. Dagasu ya fara daya bayan daya, yana juyi dasu, kafin ya sumbaci kumatunsu ya ajiye, ya dauki daya. Dadda ne karshe, inda ya makale Abban yaki sauka. Murmushi yayi kafin ya kara gyara rukon da ya masa dakyau.
Arfat tuni ya bude bayan, don daukar laptop bag din Abban kanar yadda ya saba. Sai lokacin suka lura da mutumin dake tare da Abban nasu. Dake kallonsu fuskarsa dauke da murmushi.
Gaishe shi su Arfat sukayi, ya amsa still fuskarsa dauke da murmushi
Dai - dai fitowar Sabrina don ta kasa hakurin jiran yayan nata ya shigo.
Cike da shagwaba ta iso, inda suke tsaye, rungumeta yayi, ta gefe daya, dadda na makale a gefe dayan. " sweet sis how are u?" Ya fada fuskarsa cike da fara'a narkewa ta karayi a jikinsa, " fine, sai missing dinka da mukayi sosai. Thank God u are back know! "
Har zasu shige ciki, ya juyo " Bismillah muh'd" juyowa tayi don taga da wanda yake, don kwata kwata bata lura da wani a tare dashi ba. Ido hudu sukayi haka kurun taji gabanta ya mugun faduwa, kallo daya ta masa, taja tsaki ta juya ta shige ciki.
***********************
Bakajin komai sai karar plates da spoons,. Sabrina ta fito daga kitchen dauke da holandia yeghout taja kujerar dake pacing Abba ta zauna. " Yaya ya ka barosu ammi?" Ta fada tana serving din kanta. " lafiya kalau, sunyi missing naki sosai, sun dauka tare dake zamuzo." Ya fada yana kallonta cike da kulawa." ayya nima nayi missing dinsu, especially ammina! da nayi hutu zan je."
" Allah ya kaimu." Ya fada a takaice
Kallon wanda dazu ya kira da muh'd tayi, tana tabe baki. " Yaya shi kuma wannan ina ka samoshi?"
Murmushi yayan nata yayi " he's your brother, yaron malan dhalha ne." Ya fada yana murmushi
Tabe baki tayi, tana kare masa kallo cike da kaskanci, " he's not my brother. Yaron da akace ya shiga duniya tun yana 15years, ba a san inda yake ba?"
Harararta yayan yayi, ganin tana neman badashi gaban muh'd gashi ko gaisheshi batayiba" point of correction an nemeshi an rasa." Ya fada a takaice
Kauda kanta tayi, don ta lura yayan nata baya son maganar, ita kuma yanzu ta shirya yinta. " to meya biyoka yi a'nan?"
" its not your business. " ya fada," da ido take bin yayannata ganin yadda ya hade fuska, Murmushi tayi " Allah yasa ba kwaso mana shi kayi ba? Ammi da wannan Matar taka sun fara bataka da kwashe - kwashe, Sai ranar da kuka kwaso abinda yafi karfinku kwa gane." Ta fada tare da mikewa ta koma kusa da Anty fari dake zaune a falo, ta zauna, ta dauki remote ba tare data ji ko dar ba, ta canza, zuwa channel din da takeso.
Da ido yayan ya bita, cike da takaici, kallon muh'd yayi " kayi hakuri don Allah, yarinta na damunta.
Murmushi muh'd yayi, " ba komai, ya fada cikin sanyin jiki.
Tsaki Sabrina taja tana karewa muh'd kallo daga inda take. Dogone, don zasuxo tsowo daya da yayan nata, yana sanye da Riga da wando, da babbar Riga irin dinkin yan nijer, na wani yadi mai layi layi da gani yadin bazai yi tsada ba. Ga wani rawani daya kima a kansa. In baka lura da kyau ba, zaka dauka tsohone. Saboda gewayen fuskarsa kadan kake iya gani. Farine, yana da manyan ido, da dogon hanci, bakinsa dan dai -dai red. Yatsunsa dogaye, wanda gashi baki yayi luf- luf a kan farar fatarsa. Yana da kirar karfi, duk da babbar rigar dake jikinsa zaka iya hango hakan. Tsaki ta kara ja " in banda abun yayah ta yaya, zaka kwaso this thing zuwa lagos? In ba xubarwa kai mutunci da class ba." Ta fada a ranta.
Anty fari da haushi ya gama cikata, saboda canza channel din da Sabrina tayi, tana tsakiyar kallon competition na cake, a tashar food. Ta kalli Sabrina " ubangiji Allah ya shiryeki! Na rasa randa zaki girma kisan ya kamata a gidan nan." Ta mike ta shige dakinta, don muddin ta zauna, to abin ba zai musu dadi ba.
"Nan gani, nan bari." Ta fada tana tabe baki, da fari da ido.
Sun kammala cin abinci, yaya da kansa ya raka muh'd boys quarters, da yake kowanne house yana da daki daya da toilet, a Boy's Questar's. Dakin bashi da wani girma, karamin bed ne, sai dan kanter na kaya daga gefe, sai dan filin da bai wuce wurin sallah ba, amma yasha tiles da penti yayi kyau. Sai toilet shima karami ne sosai, shower sai toilet sit ne kawai, shima yasha tiles blue. Godiya sosai muh'd ya masa. " don't mention! Karka manta were brother's. " murmushi muh'd yayi " still na gode."
" in kana bukatar wani abu, just call me, ko kuma ka je ciki wurin Anty dinku." Ya fada yana barin dakin.Dakin ya kara bi da kallo, bayan fitar yaya. Kafin ya nufi kakkabe gadon ya kwanta, yana mai kallon fankar sama, dake juyawa, tare da runtse idonsa.
*******************
"Congratulation sis. " ya fada cike da farin ciki, bayan sabrina ta gama bashi labarin yadda competition dinsu ya kare, tare da nuna masa award da gifts din data samu, da pictures.Gefe daya Anty fari da yaranta, sun kurawa TV ido, don gaba daya hankalin yayan yana wurin sabrin, data kasa ta tsare. Ta gefen ido Anty fari ke kallonsu cike da takaici. Nemakon a matsayinsa na babba ya tsawata ma sabrin, amma sauda yawa shi ke kara mata karfin gwuiwa. In ba haka ba ina yar musulmai ina wani beauty contest?
" brother shi wannan da ka taho dashi, a nan zai zauna?" Sabrin ta fada tana kallon yayan nata.
" eh!! Anan akwai opportunity da yawa da zan iya taimaka masa, wurin samun abunyi, akan can." Ya fada yana gyara zamansa.
Kada kai tayi, " lallai wannan dan kauyen zaka dauko, ka kawoshi nan? Wannan wallahi kunya zai baka! T .p kal lokal man, ga wani uban rawani kamar limamin kauye." Ta fada tana yatsina fuska in diecasting way
" stop! Kar in sake jin irin wa'annan kalaman, haka dazu kika bani kunya a gabansa, Meye hadinki da how he look? After all he's like brother to you, so stop insulting him."
Tura baki tayi, " sorry brother! Bazan iya gani inyi shiru bane, shi yasa. I hope ba'a gidan nan zai ci gaba da zama ba? Don ko ganinsa banson yi. Shekara da shekaru daya shiga duniya, amma ka dauko shi ba tare da wani dogon bincike ba ka kawoshi nan? waya Sani ko dan fashi ne ko kidnapper?." Anty fari ta mike ta dauki Armelle da tayi bacci a cinyarta, bayan taja dogon tsaki ta nufi dakinta. Da kallo suka bita, Jin tsakin nata. Sabrina ta bita da harara don tasan ita takewa tsakin, don tun dazu ta Lura tana harararta da zarar sun hada Ido, Tasan hakan baya rasa nasaba da hanata sakewa da mijin nata da tayi, Dama kuma intentionally tayi don ta bata haushi.
" kinga tashi kije ki kwanta, dare yayi." Ya fada yana mikewa don bin bayan matarsa. Shagwabe fuska tayi, " ni bana jin bacci, haba yaya muna cikin hirarmu mai dadi, zaka tafi?"
" sorry sis, ma karasa hirar gobe in sha Allah."
Anty fari ce ta fito da manyan duvet da zata shimfidawa su Arfat. Ko kallon inda suke bata yiba, ta fara kokarin janye center table din dake falon, don samun wadataccen wuri.
" me ya faru da dakin nasu? Kike musu shimfida anan?" Yaya ya tambaya bayan ta gama gyarawa yaran, tare da kwantar dasu. A kai kaice ta kalleshi Iman da Armelle ne zasu kwana a dakin, kafin gobe in gyara mata wancan dakin."
Kallonta yayi, sannan ya juya ya kalli sabrin da har zuwa lokacin tana nan a zaune. " me yasa bazata kwana a dakin sabrin ba, zuwa goben? Da wannan uban sauron zaki bazamin yara a falo!" Ya fada cikin bacin rai.
" sai ka tambayi kanwarka." Ta fada cikin jin haushi, ta fara ma yaranta adduar data saba musu duk dare.
Kallon sabrin dake faman hada rai, tana tuttura baki yayi. " what is the meaning of all this? "
Kallonsa sabrin tayi cikin shagwaba " haba Yaya! Ya za'ayi ace in kwanta daki daya da wannan village girl din?"
Kada kai yayi cike da takaici, ba tare daya tanka mata ba, ya dauki Arfat ya nufi dakinsa dashi, da kallo suka bishi, minti kadan ya dawo ya dauki dadda. Harara sabrin ta zabgawa Anty fari, kafin taja dogon tsaki ta wuce dakinta, Cikin halin ko in kula.
Anty fari ci gaba da zaune a wurin kamar wadda aka dasa, tana tariyo rayuwarta, da irin so da kaunar data nunawa Sabrina a can baya, yaya ne ya dawo dauke da filo a hannunsa. Kallonsa tayi har yayi wanka, ya canza zuwa pajamas ta kai kallonta kan filon hannunsa.
Murmushi ya sake mata " kije ki kwanta, ni nayi manage a nan." Jiki a sanyaye tamike ba tare da tace masa uffan ba, ta nufi dakin dake mazaunin mallakinta da shi. Da kallo ya bita, tare dajin rashin kyauta mata a zuciyarsa. A jiyar zuciya yaja tare da kyara kwanciyarsa da kyau, kewar matarsa ne fal gangar jikinsa da ruhinsa. Tabbas yaso Kwarai su raya wannan daren, kodon kewarta da yayi for good 1week, da baya tare dasu.
**********************
Jingina tayi da kofar, hawaye wani nabin wani. " sai yaushe zan huta? Sai yaushe zan samu farin ciki da walwala a gidan aurena? Har yaushe zan ci gaba da jure cin mutunci da cin kashin suruka da kanwar miji.? Sai yaushe zan samu cikakkiyar soyayyar mijina?" Ta dade tana zubar da hawaye tare da tausayawa kanta da rayuwarda ta tsinci kanta a ciki. Kafin ta nufi toilet tayi wanka, ta shirya cikin wasu hadaddun kayan bacci masu kyau da nauyi, saboda an fara sanyi sosai.Kwanciya tayi tsakiyar yayanta, Wanda zuwa yanzu su take gani taji sanyi, da farin ciki a zuciyarta. Su suka zamo mata sanyin ido, da zata jure komai ko don inganta rayuwarsu. Ajiyar zuciya ta sake tare da ammaton Allah. Tana mai jin zafin mijinta na rashin daukan mataki akan sabrin, yaci ace ya mata fada, saboda shi Dan Adam darajane dashi, bai kamata kana tozartashi ko kaskantar dashi ba, Don kana takamar yazo cin arziki gidanku. Ko ba komai sa mata kara, Iman kanwarta ce, babansu daya, amma akan idonta sabrin ke kiranta village girl, shi kuma ya kasa cewa komai? Duk da ba wannan bane karo na farko da take mata hakan. Sai dai na yau yafi mata zafi. Tana bukatar mijinta, tayi babban tanadi a wannan daren, amma ya zama in vain, Mara anfani! A haka har bacci yayi gaba da ita.
**************************
Sabrin kam tana shiga, alwala ta dauro, tare da jera sallolin da batayi ba. Tun daga kan sallar Azhuhur har zuwa isha Wanda basu da maraba da yar faki, ba yawa sai lada. Tun kafin ta sallame isha wayarta ta fara ringing kafin kaftawar ido har ta sallame tahiya ta rarumi wayar. Ganin sunan dake jiki, yasa ta fara saita natsuwarta, tare da furta sauke numfashi, mai hade da ajiyar zuciya "salamu alaukum" ........Follow 🏇🚵🚴.........
Vote... 💕💛💜💙
Comment 💌