HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION
KYAN DAN MACIJI.........
By Zulaihat Aliyu Misau
Part 37
Wattpad@zulaihatualiyumisau
🐍. 🐍
No comment, no vote, no update on time, eheee...
Wannan page sadaukar wane gareku masoyana, ba sai na fadeku daya bayan daya ba, kunsan kanku, ina alfahari daku..........
Not Edited........
Cike da ladabi take gaishe shi, zuciyarta na dakan uku- uku, na rashin sanin dalilin kiran! Don tabbas mahaifinnata baya kiranta sai da kwakwaran dalili, sai dai ita ke kiransa kusan kullun ta gaishe shi, ko bayan kwana biyu in abubuwa sun mata yawa.
" yayanki ya gaya miki sakona?" Tambayarsa ya dawo da ita daga sake- saken da ta keyi. " a'a " ta fada a sanyaye. Numfashi yaja " yana gida ko bai dawo ba tukun?" " bai dawo ba, amma ban sani ba ko yanzu ya shigo?" " shikenan!! Munyi magana dashi ki taho tunda kun kammala jarabawa. Sannan banji dadin abinda kikayi ba! Ban san rashin mutuncin naki har ya kai ki iya daga hannu ki mari babba ba. Anyah!!! Kina ma kanki fada kuwa? Irin tarbiyyar dana baki kenan?." Baki ta zumbura cikin shagwaba " nafa bashi hakuri!!" Ta fada. " gidanku!!! Gidanku nace!! Kuma kisa a ranki kin aureshi kin gama, da na baki zabi a karo na biyu, amma tunda baki da hankali da sanin ya kamata na janye, duk da yanzu kina da damar zabawa kanki abokin zama! Na zaba miki, in kuma kinki to sai dai ki nemi wani uban da zai daura miki aure amma bani ba." Ya fada cikin fushi. Kuka ta fara " Bai yi karatu bafa Abba! Gashi dan kauye dashi!" Ta fada cikin kuka da shagwaba " yo!! Keda kikai karatun mai ya kara miki? Yaron da keda ilmin addini har a kirashi baije makaranta ba? Shine kuwa yaje makaranta, dama ni tun farko yadda naga yana kula dake lokacin rashin lafiyarki hankalina ya kwanta dashi, don dai lokacin kin riga kin fitar da mijine kar inyi karanta, kuma shi bai nuna yana sonki ba, amma yanzu tunda harya furta to zan kuwa bashi aurenki. Yaro mai hankali da natsuwa irin wannan, shine mijin da nake miki fatan samu. Yaro dan mutunci tun da nake tare da iyayensa ban taba ganin abin aibu ko ashsha a tare dasu ba, mutane masu mutunci da sanin ya kamata." " don't Allah Abba kayi hakuri." Ta fada still tana kuka.
" mun riga mun gama magana da mahaifinsa dazu, mun yanke komai sauran bayani kyaji a wurin yayanki. Ni kuma ina jira inga in zakimin biyyaya ko zaki bijirewa bukata ta." Yana kaiwa nan ya katse kiran.
Share hawayenta tayi, ta saki dariya, sosai take dariya tana rike ciki. Sai da tayi mai isarta sannan ta gyara kwanciyarta tana kallon ceiling, murmushi ta sake tana kada ido. " good job Sabrina!!! Aikinki yayi kyau." Ta fada tana lumshe ido. Tasan yadda Yaya yaso ta auri Muhd a can baya haka mahaifinnata, don har ya furta hakan a gabanta, ranar da ciwonta ya tashi, gaba daya gidan sun gigice duk wani taimako da aka amso mata sunyi anfani dashi amma ba sauki, dole ya kira Yaya, ya gaya masa, suna wurin aiki, haka suka taho Bauchi. Shigowar dare sosai sukayi, sun samu har lokacin ana fama da ita. Addu'oin daya saba mata ya mata, cikin ikon Allah ba'ayi 30min ba bacci ya dauke ta. A nan ne abban yake jinjina yiyuwar aurenta, gashi a lokacin saura baifi 1month ba. " ba wani abun damuwa bane, in har zata kula da ibada yadda ya kamata, sannan ta daina wasa da azkhar na safe dana yamma, zata samu sauki. Yanzu din ma sakaci da takeyi dasu ne yasa abun baya sauki duk da taimakon da ake mata." Muhd ya fada, sannan ya musu sallama ya nufi part dinsu.

YOU ARE READING
KYAN DAN MACIJI ( Completed )
Romanceyana dauke da fada karwa, nishadan tarwa, ilmantarwa, soyayya. akwai sakonni da yawa a cikinsa. in bakya comments ko vote! please don't read my story.