KYAN DAN MACIJI.........
By Zulaihat Aliyu Misau
Part 14
Wattpad@zulaihatualiyumisau
No comment, no vote, no update on time, eheee...
🐍. 🐍
Not edited......
Hannunsa yasa ya kara rufe kunnensa dasu da kyau, saboda wani ihun da Sabrina ta kara sakewa, Cikin bacin rai yayi kanta zai mangareta, ko me ya tuna kuma ya dungule hannun ya koma ya zauna. Anty fari ta karaso tana tambayarsa lafiya? Hararar Sabrina yayi ba tare da ya furta komai ba.
Bimbo da Iman tuni suka koma kitchen don ci gaba da gyare- gyare.
" wallahi dama na fada ka daina sona kwata-kwata! Ka rasa wanda za kayi sha'awar hadani dashi sai wannan banzan dan kauyen, dako aji bai je ba, saboda ka tsaneni!"
" gara shi, Ajin ne bai jeba ke da kika je ajin mai ya tsinana miki zuwa ajin?" Yaya ta fada cikin bacin rai.
Kuka Sabrina ta fara da gaske, saboda tsabar takaicin maganar yayan. " Allah ya tsareni da mummunnar kaddara." Ta fada cikin kuka
" ko da hakan ta kasance shi aka cuta ai!! Don na tabbata duk wanda kika aura ya hadu da aiki da irin wannan halayyar taki." Shiru tayi tana kallon yayan nata, da kallo daya zaka masa kasan yana cikin bacin rai.
" Haba!!! Kai kuwa? Duk meya kawo wa'annan magan- ganun? Ba girmanka bane." Anty fari ta fada
Makullin motarsa ya dauka ya fita, rai bace.
Anty fari ta kai kallonta kan Sabrina databi yayanta da ido. " kema kina abu kamar wata karamar yarinya! Wannan irin ihu kamar ana kwakule maki idanuwa?"
Harara Sabrina ta zuba mata " sai ki zuba ruwa a kasa kisha, kinyi nasarar sa Yaya ya tsaneni kuma wallahi kisa a ranki kafin in bar gidan nan, sai wa'annan banzayen yan ci ranin sun bar gidan nan, don ba gidan ubansu bane, yadda suka mallake min Yaya, ni nafi karfinsu..." Taja tsaki ta wuce dakinta tana kara wa da " yan bakin ciki kawai!!! Wallahi sai dai mutun ya mutu, nan gani nan bari, na gaba yayi gaba."
Baki sake Anty fari take binta da kallo ita kuma meye nata a ciki? Tabe baki tayi " Allah ya shirya, ni kam na gode Allah, gara ki tattara ki kara gaba, ko na samu sakewa da wata yawa a gidana, haba wannan fitina har ina? Daga wannan sai wancan, kanki ke kadai kwallin- kwal, shima da rashin gane halinki ne, yanzu kuwa yasan komai." Ta mike ta koma don ci gaba da hidimominta cike da farin ciki da nishadi.
Ita ko Iman ba zata zauna da ita ba, hakan ya mata, data ci gaba da zama da Sabrina da kullun wulakancinta sabon darasi take budewa a gidan. Ga wani tsana da tsangwama da ta dauka ta daurawa iman, kamar bata San daga inda ta fito ba.
Tana shiga dakinta wayarta ta dauka ta kira ummanta, cikin kuka ta zayyana mata duk abinda ya faru, har da kari. Ran Hajiya kubra ya baci sosai, ba bata lokaci ta kira jibrin ta wanke shi tsaf.
Sai washe garin ranar suka bude tsarabar MK, saboda rashin walwala da aka samu a gidan. Kyauta ce ta bajinta da asalin tsada, Kowanne da zunansa a kan nasa.
Godiya Anty fari tayi, tace ta masa godiya. Don Yaya kam ko ta Kansu bai bi ba, har lokacin yana jin haushin hadashi da Hajiya da tayi duk da kunnenta daya ja sau ba adadi.
******************
Yau kwana 5 kenan da zuwan MK. Sabrina na dakinta, Iman ta shigo da sallama. Wani kallon banza Sabrina ta watsa mata " tafiya. " ta fada cikin daga murya

YOU ARE READING
KYAN DAN MACIJI ( Completed )
Romanceyana dauke da fada karwa, nishadan tarwa, ilmantarwa, soyayya. akwai sakonni da yawa a cikinsa. in bakya comments ko vote! please don't read my story.