part 39

1K 104 15
                                    

HIKIMA WRITER'S ASSOCIATION


KYAN DAN MACIJI.........

By Zulaihat Aliyu Misau

Wattpad@zulaihatualiyumisau
Part 39

                           🐍. 🐍

No comment, no vote, no update on time, eheee...

Not Edited........

Tun tana sa ran shigowarsa har bacci yayi nasarar yin gaba da ita. Sai wurin 2am ya shigo ya dauki pillow da bedsheet ya koma falo, saman 3 sitter ya jefa pillow dinsa, ya kwanta, bayan ya kashe komai, yayi addua a haka bacci yayi gaba dashi.

*******************
Kusan asubah ya tashi, ya gabatar da nafilfilinsa, sannan ya fara karatun qur'ani, har lokacin sallar Asubah. Sabrina kam bacci yayi dadi, don tana tattare da gajiya, ko juyi bata yiba. Jikin gadon ya fara bubbugawa da gwuiwar yatsunsa, juyi tayi, tana kara shigewa cikin lallausan bargonta. Kara kwankwasawa yayi da karfi fiye da farko, juyi tayi, ta fara bude idonta a hankali, tana yamutsa fuska. " tashi kiyi sallah." Ya fada yana kokarin barin dakin. Tsaki taja " in na tashi zanyi ai!! Haka kurun mutun na cikin baccinsa mai dadi, zaka wani tashe shi." Ta fada cikin murya mai cike da bacci.  Ta kara Jan tsaki, ta juya zata ci gaba da baccinta. Har yasa kafa zai fita, ya jiyo abinda take fada. Kada kai yayi, ya nufi fridge! Robar ruwa ya dauka, ya koma dakin. Har ta koma baccinta, hankali kwance. Bargon ya yaye, hakan yasa ta motsa tana tura baki, saukar ruwan sanyi taji a jikinta, a zabure ta mike tana jan numfashi, saboda sanyin ya hadu biyu, dama dakin ya dau sanyi sosai, saboda AC, gashi ruwan yayi sanyi sosai, ita kuma ba suturar arziki ba, balle ya tare mata wani abun. " karki fara wannan gan- gancin! Matukar kina gidan nan, sallah kan lokaci ya zama miki dole, in ba haka ba zaki sha mamakina wallahi, akan matakin da zan dinga dauka a kanki." Ya fada cikin bacin rai

" shine zaka watsa min ruwan sanyi? Sallar kai zan mawa ko kaina?" Ta fada cikin tsiwa.

" zaki tashi kosai na dau mataki na gaba." Kallonsa tayi, ganin yadda ya hade rai ba wasa, yasa tsoro a zuciyarta, don haka cikin karfin hali taja dogon tsaki ta mike zuwa toilet din dake cikin dakin.

Da harara ya rakata, ace yarinya kamar wannan bata san ta kula da ibada yadda ya dace ba, sai shirmen banza! Ga ilmin amma bata aiki dashi ko kadan. Shi yama rasa gane sakacin natane kona iyayenta? Koda yake sune manyan masu laifin, don yaro da abinda ka saba masa yake tashi. ( a wurin Sabrina is a different case )

Dauke kansa yayi, ganin yadda ta fito tana wani karai -raya, ita ba kayan arziki ba ajinta. " ki sameni a falo." Ya juya ya fita

" mugu!!." Ta fada tana zunbula hijab dinta, tabi bayansa.

Shiya jasu sallah, bayan ya sata tayi raka'atul fajr. Rabonta da samun sallah kan lokaci harta manta. Suna idarwa ta mike tana zabga hamma zata koma daki. " dawo ki zauna!!" Kallonsa tayi tana yamutsa fuska, " bacci na keji malan, tunda nayi sallar a barni na kwanta ai ko?" " in kin gama azkar dinki kyaje ki kwanta din, kasa uwar bacci." Ya fada yana jifanta da wani matsiyacin kallo. Saman kujera ta zauna, tana zabga hamma, tare da ja masa Allah ya isa, don idonta har wani zafi- zafi suke kamar an zuba barkono a ciki, don baccin da take ji. Sama - sama tayi azkhar din, kafin ta mike ta koma daki ta kwanta.

Shikam yana kammalawa ya fara shirin tafiya office, don motocin company ke kai ma'aikatan compound din, sabanin compound dinsu Yaya, da kowa keda motar kansa. 7am dai - dai motarsu ta daga, anan ya samu damar gaisawa da nevours dinsu, wasun kam ya sansu a wurin aiki Suka masa congratulations

KYAN DAN MACIJI ( Completed )Where stories live. Discover now